A+ R A-
05 December 2021

Tuna Bayan Jagora Dangane Da Ranar 12 Ga Watan Farvardin 1358

Shinfida: Abin da ke biye wata hira ce da aka yi da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, a shekarar 1985 dangane da Ranar Jamhuriyar Musulunci ta Iran:

 

Tambaya: Bayan godiya saboda lokacin ka da ka ba mu. Kamar yadda ka sani ne cewa a halin yanzu muna cikin ranakun cika shekaru bakwai da kafa tsarin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ne. Shekaru shida da suka gabata a irin wannan rana ce al'ummarmu ta hanyar fitowa kwansu da kwarkwatansu a yayin zaben jin ra'ayin (wani irin tsari ne al'ummar Iran suke so ya jagorance su) al'ummar Iran suka zabi Jamhuriyar Musulunci (a matsayin tsarin da suke so ya jagorance su). Idan har akwai wani abin da kake son fadi dangane da wannan lamari ko kuma wani abin tunawa mai faranta rai dangane da wadannan ranaku, ko za ka yi mana bayaninsa:

 

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Abubuwan fadi dangane da ranar Jamhuriyar Musulunci da kuma ranar da aka gudanar da wannan kuri'ar jin ra'ayin al'umma suna da yawan gaske, sannan kuma ko shakka babu akwai abubuwan da zan iya tunawa wanda lalle ba za a iya fadinsu gaba daya ba a dan wannan karamin lokaci. To amma a takaice ranar Jamhuriyar Musulunci wani lokaci na tarihi da ba shi da tamka cikin tarihin kasar mu, saboda kuwa wannan shi ne karon farko bayan bayyanar Musulunci sannan kuma bayan dan wani karamin lokaci bayan nasarar da musulmi suka samu a kan Iran (a lokacin halifofi), wato cikin wadannan ‘yan shekaru na mulkin Musulunci, tsawon wadannan shekaru da kasar take da su, (wannan ne) a karon farko aka sanar da wata hukuma, aka sanar da wani tsari wanda yake da wasu siffofi guda biyu na al'umma da kuma na Ubangiji; wato Jamhuriyar Musulunci.

A hakikanin gaskiya wannan lamari ba zai taba yiyuwa a kwatanta shi da wani yanayi cikin tarihin kasar mu ba. Ya kasance wani lamari ne mai cikawa da kuma kammala juyin juya halin ranar ashirin da biyu ga watan Bahman (ranar da aka samu nasarar kafa tsarin Musulunci da kuma Jamhuriyar Musulunci a Iran), wato takaitaccen abin da aka samu a ranar ashirin da biyu ga watan Bahman shi ne ranar Jamhuriyar Musulunci wato ranar sha biyu ga watan Farbardin (watan farko na hijira shamsiyya).

A wata mahangar kuma ta daban, ranar Jamhuriyar Musulunci rana ce mai matukar muhimmancin gaske, hakan kuwa shi ne cewa wannan shi ne misali na farko a duniyarmu ta yau da aka gabatar wa al'ummar duniya da irin wadannan koyarwa, tsari, siyasa da mahanga da hanyoyi daban-daban. Wannan shi ne misali na farko da al'ummar duniya suka gani. Babu guda daga cikin jamhuriyoyi na ‘yan gurguzu da na ‘yan demokradiyyar yammacin duniya da sauran su da ya kasance wani sabon abu. Don kuwa asalin jamhuriya ba wani abu ne sabo ba, to amma jamhuriyar da ta ginu bisa koyarwa ta addinin Musulunci, to wannan wani abu ne da ba shi da na biyu.

Akwai wata siffar kuma ta daban da take cikin ranar Jamhuriyar Musuluncinmu hakan kuwa shi ne cewa wannan lamari ba wai kawai abin farin cikinmu mu al'ummar Iran kawai ba ne, face dai ranar murna da idi ne na dukkanin musulmi wato kimanin mutane biliyan guda. Wadannan mutane dai, wato al'ummar musulmin, sun saba da cewa Musulunci yana cikin yanayi ne na kare kansa da kuma yanayi da mai da shi saniyar ware. A lokacin da aka sami wata al'umma da take cikin yanayin fuskantar ma'abota girman kan duniya da kuma gwamnatoci irin na mutum da suke da nakasa sannan kuma ta sanar da wata jamhuriya wacce ta ginu bisa asasin koyarwar Musulunci, to hakan babban abin alhafari da dauakka ne ga al'ummar musulmi. A takaice dai akwai siffofi daban-daban da wannan rana ta Jamhuriyar Musulunci ta kebanta da su.

Dangane da abin da zan iya tunawa kan wannan rana, duk kuwa da cewa a ranar kada kuri'ar na kasance a garin Kerman ne, Imam ne ya ba ni wani aiki a can wato in tafi Baluchestan da garuruwan Baluchestan din don ganawa da mutane sannan kuma in isar musu da sakon Imam. Ku duba ku ga irin wannan sako na so da kauna wanda tun a ranar farko Imam ya kasance cikin tunanin wadannan wadanda aka raunana da yankunan da suke can nesa wadanda aka manta da su a lokacin tsohuwar gwamnatin (Shah), don haka ne Imam ya tura ni can din saboda ina da ‘yar masaniya kan yankin don gudanar da wannan aikin.

Lokacin da na isa Kerman, a kan hanyar Baluchestan wanda a ranar ce ake gudanar da wannan zabe. A loakcin matasa masu son addini na Kerman sun zo da wasu akwatunan zabe. Kowa daga cikinsu yana so ya kawo nasa akwatin don in kada kuri'a ta. Wadannan matasa sun san ni. Saboda a baya na kasance na kan je Kerman kuma mutanen Kerman sun san ni. Ni ma dai tun da jimawa na kasance ina da wata alaka ta so da kauna ga mutanen Kerman, mutane ne da suke cike da nuna kauna, a ko da yaushe suna kan idanuwana. Lalle lokaci ne da ke cike da ababen farin ciki a gare ni, a lokacin da na ke kada kuri'a ta cikin akwatin zaben, na kasance ina ganin irin kumajin da mutanen Kerman suke nunawa. Daga baya kuma sai aka sanar da cewa kashi casa'in da tara cikin dari na mutane sun kada kuri'ar amincewa ne da Jamhuriyar Musulunci.

Abin da nake son fadi a matsayin abin tunawa a nan zan yi ishara ne kawai da irin nuna rashin amincewa da kada kuri'ar da irin yanayin da aka gudanar da shi, wato akwai bangarori daban-daban da suka nuna adawarsu da gudanar da wannan zaben jin ra'ayin al'umma. Wato bangaren da yake da iko kan kafafen watsa labarai na kasa, masana masu ra'ayin gurguzu da masu sassaucin ra'ayi, wadanda su ne suke rike da jaridun wancan lokaci irin su Ittila'at da Keyhan na wancan lokacin. Alhamdu lillahi daga baya duk an yi waje da su, duk da cewa babu wata jarida ta azo a gani, wato babu ko da wannan jarida ta Jamhuriyar Musulunci, haka nan sauran jaridun da aka tafi a kansu. Dukkanin abin da zuciyarsu take so ne suke rubutawa. Sun tafi nan da can suka tattauna da bukatar ra'ayoyin wannan masanin na wancan kungiya ta mulhidai da wadanda suka yi kusa da mulhidan suna tambayarsu kan mene ne ra'ayinsu kan na'am da kuma a'a? (wato dangane ko sun amince da jamhuriyar Musuluncin ko kuma a'a) ko kuma (suna cewa) ku zo mu gabatar da wani yanayi na hukuma sannan mu samu ra'ayin mutane. Manufarsu ita ce su fitar da mutane daga cikin wannan magana guda da aka samu, ko da yake dai babu wani bambanci da hakan ya haifar, wato bai yi wani tasiri ba. Na'am a dabi'ance dai mutane ba za su kada wa wancan hanyar ta daban ra'ayinsu ba musamman ma bayan irin wannan fitowa fili da Imam ya yi inda ya ce Jamhuriyar Musulunci kawai babu ragi babu kari, amma dai wadannan mutane sun ci gaba da gudanar da ayyukansu ko watakila za su sami damar haifar da wani gibi, wato su rage irin wannan yawan kuri'ar mutane, su raba kuri'un mutane. Haka suka kasance suna yi ga shi kuma muna da wani irin yanayi mara kyau a cikin majalisar juyin juya halin inda sakamakon irin ayyukan ‘yan kungiyar da suke da ra'ayin sassauci wato na ‘yan kasanci, amma dai haka aka iya tabbatar da cewa wannan hanya (da muke kai) ita ce hanyar gaskiya.

(Hira dangane da ranar 12 ga watan Farbardin ranar 10/1/1364 (30/3/1985).)

(Mun Samo Wannan Labarin Ne Daga Shafin Jagora Imam Khamenei)