A+ R A-
05 December 2021

Imamul Umma Imam Khumaini {r.a.}

An haifi Imam Ruhullah al-Musawi al-Khumaini ne a shekarar 1901 a garin Khumain, kuma haihuwarsa yayi da ranar da aka haifi Sayyidatuna Fatima al-Zahra (a.s), 'yar Manzon Allah, matar Imam Ali, uwar Hasan da Husain (a.s), mafifiyar mace kana kuma Shugaban matayen duniya gaba daya. Shi dai Imam Khumaini ya fito ne daga cikin zuriya ma'abuta addini, don mahaifinsa Ayatullah Sayyid Mustafa Musawi ya kasance sanannen malami ne wanda yayi karatu a garuruwan Najaf da kuma Samarra da suke kasar Iraki, kana daga baya ya komo garin haihuwarsa wato Khumain inda yaci gaba da karantarwa da kuma shiryar da jama'a har lokacin da Allah Ya karbi ransa yana dan shekara 42. Mahaifiyar Imam ma ta kasance ta fito ne daga gidan ilimi da addini, don kuwa ta kasance 'ya ce ga shahararren malamin nan wato Ayatullahi Mirza Ahmad.

To a sabili da rasuwar mahaifinsa tun yana karami, Imam (r.a) ya girma ne a karkashin kulawan mahaifiyarsa da kuma gwaggonsa mai suna Sahiba, to amma ita ma wannan gwaggo nasa ta rasu lokacin Imam yana dan shekara goma sha biyar, bayan dan wani lokaci kadan mahaifiyarsa ma ta rasu. Hakika wadannan rashi sun kasance abubuwan tashin hankali ga Imam, to amma hakan ma ya dada kara wa Imam karfin gwuiwa da kuma dogaro ga Allah da kuma kara imani da Shi Madaukakin Sarki.

Imam Khumaini (Allah Ya kara masa yarda) ya fara karatu ne tun yana dan karami, kana kuma yaro mai tsananin hazaka da fahimtar karatu. Tun yana dan karami ya fara koyon rubutu da karatu a wajen babban wansa Ayatullah Pasandideh (Allah Ya lullube shi da rahamarSa), kana kuma ya koya yaren larabci, nahwunsa da kuma Mandiki, bugu da kari kan wasu darussan kuma.

To bayan karatu na wadansu shekaru a wannan gari na Khumain, Imam yayi hijira zuwa garin Arak don kara fadada karatun nasa, kana daga baya kuma ya koma garin Kum don ci gaba da karatu, inda anan ya zama babban masanin fikhu da sauran ilmummuka. Imam dai ya kasance mutum ne mai tsananin kyawawan dabi'u, mai kula da ayyukan addini da kuma kiyaye hakkin mutane da kuma na Ubangiji Tabaraka wa Ta'ala. Sannan kuma mutum mai tsananin hangen nesa da kuma sanin ya kamata, ga kuma dimbin karatu, don tun yana shekara 27 ya fara koyar da falsafa.

Imam Khumaini yayi aure ne yana dan shekara 30, inda ya auri 'yar wani malamin addini mai tsananin tsoron Allah da gaskiya, kuma Allah Ya albarkaci wannan aure nasu da 'ya'yaye guda biyar, biyu maza uku kuma mata.GWAGWARMAYARSA

 

Imam dai, kamar mahaifinsa, ya kasance mutum ne mai kin zalunci da kuma fallasa asirin azzalumai a duk inda suke ba tare da jin tsoro ko nuna gazawa ba. Irin tona asirin zaluncin da tsohuwar gwamnatin gidan sarautar Pahlawi ta Iran take yi zai dada tabbatar mana da hakan kuma hakan ma shi yasa suka dinga tsangwamansa, daure shi kai da ma korar sa daga kasar zuwa gudun hijira.

Misali, a shekarar 1962 lokacin da gwamnatin zalunci na kasar Iran na wancan lokacin ta sanya hannu kan wata doka da ta cire kasantuwan addinin Musulunci a matsayin addinin kasar kamar yadda tsarin mulkin kasar ya tanadar da kuma cewa ba lalle ne sai wadanda aka zaba zuwa majalisa sun yi rantsuwa da Alkur'ani mai girma kamar dai yadda dokar kasar ta tanadar ba, nan take Imam Khumaini da wasu malamai daga birnin Kum suka nuna rashin amincewarsu da wannan doka, kuma Imam ya aika wa Prime Ministan kasar na wancan lokacin sako inda yake Allah wadai da wannan hukumci da ya yanke bugu da kari kan tofin Allah tsine da irin mika wuya da suke yi wa haramtacciyar kasar Yahudawan Bani Isra'ila, da kuma yi musu barazanar cewa matukar basu janye wannan hukumci ba to zai kirayi al'umma su fito don yin gwagwarmaya da wannan gwamnati ta zalunci.

Hakan kuwa aka yi don al'umma sun fito a birnin Kum, a bisa umurnin malamai, don nuna rashin amincewarsu da irin wadannan matakai da gwamnatin take dauka da kuma irin goyon bayan da take nuna wa haramtacciyar kasar Isra'ila. Al'marin da ya tilasta wa gwamnatin janye wannan hukumci.

Irin wannan jaruntaka, karfin gwuiwa, sadaukarwa da kuma tsage gaskiya ya sanya kaunarsa da kuma jin maganansa a zukatan al'uma, al'amarin da ya kasance babbar kafar ungulu wa gwamnatin zalunci na wannan lokacin. Misali a shekarar 1963, lokacin malamai a birnin Kum suka sanar da cewa kada mutane su gudanar da bukin sabuwar shekara a wannan shekarar, hakan kuwa saboda yayi daidai ne da ranakun shahadar Imam Sadiq (a.s) (Limamin Shi'a na shida). Wannan lamari ya sosa wa gwamnatin hambararren sarki Shah rai, ba don komai ba sai don saboda ganin yadda al'umma suke bin maganganun malamai musamman ma shi Marigayi Imam (r.a), to sai gwamnatin ta kirkiro wata hanya ta yin kafar ungulu wa wannan lamari. Don haka sai gwamnatin ta tura wasu daga cikin 'yan koranta da kuma 'yan kungiyar leken asirin nan na SAVAK zuwa garin Kum dauke da makamai. A daidai wannan lokaci kuwa gidan Imam yana cike da mutane, kwatsam kawai sai aka ji wasu mutane suka take kin addini da kuma cin mutumcinsa, kana kuma wadansu daga cikin wadannan 'yan iska suka wuce zuwa makarantar Faiziyya don tada hankalin jama'a da kuma kai hari wa dalibai da sauran jama'a. Kana a wasu bangarorin kuma suka bude wuta da kuma dukan wasu malamai da sauran jama'a, hakan dai duk da nufin tsorata malaman da sauran jama'a don su yi shiru.

Koda da wannan labari yazo kunnen Imam, nan take ya fito yayi wani jawabi don tabbatar da mutane kan wannan tafarki da suka kama, inda yake cewa:"Ku daure! Don kuwa ku mabiya Wasu Shuwagabanni ne wadanda suka fuskanci zalunci sama da irin wanda kuke fuskanta. Irin wannan lamari abu ne mai dada karfafawa. Da yawa daga cikin manyan mutanen Musulunci sun fuskanci irin wannan zalunci, kai har ma da mutuwa don su isar da wannan addini gare ku. Don haka ya hau kanku ku kiyaye wannan madaukakiyar gado". Nan take wannan jawabi na Imam ya samu karbuwa a wajen al'umma, ba don komai ba sai don saboda irin matsayin da Imam yake da shi a zukatansu da kuma cewa shi ma kansa an yi masa wannan barazana ta mutu.

Bugu da kari kuma Imam ya umurci malaman da suke birnin Tehran da su suma su yi Allah wadai da irin wannan danyen aiki na gwamnatin, kana kuma ya bukaci limamai da masu wa'azi da suma su dinga tona asirin wannan gwamnati da irin alakar da take da shi da haramtacciyar gwamnatin Isra'ila a duk lokacin da suke gabatar da hudubobinsu.

Nan take kuwa suka rungumi wannan kira na Imam. To irin wannan karbuwa da Imam yake samu a wajen al'umma ya kasance babban abin damuwa ga gwamnati, wacce ta dauki hakan a matsayin babban barazana gare ta. Don haka sai suka fara tunanin kirkiro hanyoyin da zasu yi kafar angulu wa irin wannan karbuwa da yake samu a wajen al'umma. Daga cikin irin wadannan matakai shi ne hana shi gabatar da wa'azi da lakcoci da makarantar nan ta Faiziyya. To amma Imam ko ya kula da wannan hani da suka masa, inda ya tafi wannan makaranta a yammacin ranar 10 ga watan Muharram (wato ranar Ashura don tunawa da Shahadar Imam Husain), inda ya bayyana cewa:

"Mu mun fahimci cewa su (gwamnati) suna gaba da Musulunci ne da kuma jagorancin addini. Haramtacciyar kasar Isra'ila so take ta ci mutumcin Alkur'ani mai girma, wannan madaukakin Littafi namu da kuma gusar da jagorancin addini. Isra'ila so take ta tatse mana harkokin tattalin arziki, kasuwa da kuma aikin gonanmu".

Wannan jawabi na Imam ya girgiza sarki Shah da gwamnatin nasa, don haka a daren ranar 15 ga watan Khordad (5th Yuni 1963) sai gwamnati ta tura jami'an tsaronta zuwa birnin Kum, inda suka kama Imam kana suka tafi da shi birnin Tehran kana suka tsare shi a gidan yari, daga baya kuma suka tafi da shi zuwa wani bariki na soji. Koda gari ya waye sai al'umma garin Kum bisa jagorancin dan Imam, (Haj Mustapha Khumaini) suka fito kan tituna don yin Allah wadai da gwamnatin, suna masu rera taken"Ko Mutuwa Ko Kuma Khumaini". A birnin Tehran ma mutane sun fito don bukatar a sako Imam. Su kuma jami'an tsaro sai suka bude wuta inda suka kashe da kuma raunana darurrukan mutane. Washe gari ma haka mutanen suka sake fitowa, a wannan karonka har da wasu garuruwan, don nuna goyon bayansu ga Imam da kuma neman a sako shi ba tare da bata lokaci ba.

Bayan 'yan watanni sai aka sako Imam daga wannan dauri da aka masa, inda ya dawo garin Kum. To amma maimaikon Imam ya ja da baya, sai ma ya dada kaimi inda yaci gaba da jawabai da kuma dada tona asirin wannan azzaluman gwamnati da kuma ci gaba da kiran al'umma da su fito don kafa hukuma ta Allah.GUDUN HIJIRA NA TILAS

 

Irin wannan karbuwa da Imam ya samu a wajen al'umma da kuma irin tona asirin gwamnati da kuma kin yarda da duk wani abin da tayi wanda ya saba wa Musulunci da kuma maslahar al'umma, ya sanya gwamnatin cikin halin kaka ni kayi da kuma damuwa, don haka sai gwamnatin ta fara shirye-shirye korar Imam daga kasar Iran da kuma tura shi gudun hijira ta dole.

A sabili da haka sai gwamnati ta sake tura sojoji zuwa birnin Kum a daren ranar 13 ga watan Aban 1343 (Nuwamban 1964), inda suka kama Imam da kuma tafiya da shi filin jirgin saman Mehrabad dake birnin Tehran don tura shi gudun hijira kasar Turkiyya. Kana kuma da gari ya waye wadannan sojoji suka mamaye gidajen malamai da sauran mutane inda aka hana su fita. Kana kuma suka kama Haj Mustafa Khumaini suka tafi da shi Tehran (bayan watanni biyu shi ma suka tura shi gudun hijira kasar ta Turkiyya).

To amma duk da haka dai al'umma ba su yi shiru ba, inda suka aika da wani sako zuwa ofishin jakadancin kasar Turkiya da ke birnin Tehran don nuna goyon bayansu ga Imam da kuma jagorancin addini. Shi kuwa wanda ya bada sanarwa da kuma daukar nauyin tura Imam gudun hijira Hasan Ali Mansur aka halaka shi.

Imam dai bai jima a wannan kasa ta Turkiyya ba, don kuwa ita ma gwamnatin ta Turkiyya, saboda irin matsin da take dinga fuskanta, ya tilasta mata korar Imam zuwa kasar Iraki, inda gwamnatin Iraki ta karbe shi amma da sharadin cewa gwamnatin Iran ba ta da ta cewa dangane da lamarin Imam, ayyukansa da kuma shekarun da zai yi a kasar.

HIJIRA ZUWA KASAR IRAKI:

A nan kasar Iraki ma, Imam yaci gaba da wannan aiki da ya fara na kiran al'umma zuwa ga jihadi da kuma tabbatar da hukumar Allah ta hanya jawaban da yake yi wadanda ake aikawa da su kasar Iran ta hanyar wasu amintattun mabiyansa, bugu da kari kuma kan rubuce-rubucen da ya dinga yi. A takaice dai Imam ya zauna a kasar Iraki har na tsawon shekaru goma sha biyar, kafin a yi kulleleniyar korarsa daga wannan kasa.

HIJIRA ZUWA KASAR FARANSA:

Duk kuwa da cewa Imam baya nan cikin Iran, to amma gwamnatin kasar ba ta sami kwanciyar hankali ba saboda irin ayyukan da Imam yake gudanarwa da kuma irin ci gaba da goyon bayan da al'umma suke nuna masa. Don haka, a wata ganawa da ta gudana tsakanin ministan harkokin kasashen wajen kasar ta Iran da takwarar aikinsa na kasar Iraki a birnin Newyork, sun zartar da cewa lalle ne a kori Imam daga kasar ta Iraki. Don haka a ranar 2 ga watan Mehr, 1357 (24th Satumba 1978), sai jami'an tsaro suka kewaye gidan Imam a garin Najaf (a kasar Iraki), wannan lamari ya bata wa dubban al'umman Musulmi na kasar Iran, Iraki da sauran kasashen Musulmi. A wata ziyara da da shugaban jami'an tsaron kasar ta Iraki ya kai wa Imam a irin wannan hali, ya bayyana wa Imam cewa matukar dai yana son ci gaba da zama a wannan kasa dole ne ya bar wadannan ayyuka na siyasa da yake yi. Wannan jawabi ya fuskanci kakkausar suka daga wajen Imam, inda yaki yarda da yin shiru ya gwammace ya bar kasar akan ya bar wannan tafarki na Muhammadiyya.

Don haka a ranar 12 ga watan Mehr, sai Imam ya bar birnin Najaf zuwa iyakar kasar Kuwait. To amma kasar ta Kuwaiti ba ta yarda Imam ya shiga ba, don haka bayan yayi shawara da dansa Hujjatul Islam Haj Ahmad Khumaini, sai Imam ya yanke shawarar zuwa kasar Faransa. Inda a ranar 14 ga watan Mehr ya shiga kasar Faransa (birnin Paris)inda ya zauna a gidan wani Bairaniye a unguwar Noefel Le Chateau.

Imam ya zauna a wannan guri ne kawai na tsawon watanni hudu kawai, inda ya shirya don dawowa gida, al'amarin da ya kawo karshen shekarun gudun hijirarsa da kuma kawo karshen mulkin dagutu a wannan kasa ta Iran.DAWOWARSA GIDA


 

 

A farko-farkon watan Bahman ( watan Janairun 1978), labarin dawowar Imam gida ya yadu, al'marin da ya sanya al'umma cikin farin ciki da jin dadi, don kuwa shekaru goma sha hudu kenan da aka raba su da wannan abin kauna nasu. Koda yake da dama daga cikin mutane suna cikin fargabar cewa wani abu yana iya samun Imam, saboda a daidai lokacin gwamnatin Shah ce take mulki (ba ta riga ta fadi ba) kuma a na nan cikin dokar ta baci ne a kasar. Don haka sai wasu na kusa da Imam suka bukaci da ya jinkirta wannan dawowa har sai al'amurra sun yi kyau. To amma duk da hakan kuma duk da ma barazanar da gwamnatin tayi na fasa jirgin da zai dauko Imam matukar dai yace zai dawo, to amma haka Imam yace zai dawo gida don zama cikin al'ummansa da jin irin wahalhalun da suma suke ji.

To koda gwamnatin Prime Minister Bakhtiar (don a lokacin sarki Shah ya riga ya gudu ya bar ladansa) ta ji wannan sanarwa ta Imam ya bayar na dawowa gida, sai ta bada umurnin a rufe bangaren zirga-zirgan jiragen saman waje na filin jirgin saman birnin Tehran don hana Imam sauka. To amma wannan mataki ya fuskanci mummunan adawa da mayar da martani daga wajen al'umma, inda wasu dubban al'umma suka fito kan tituna don bukatar a bude filin jirgin. Kana wasu malamai da kuma wasu fitattun 'yan siyasar kasar suka shiga masallacin Jami'ar Tehran suna masu cewa ba zasu fito ba har sai an bude wannan filin jirgi. Daga karshe wannan lamari dai ya tilasta wa gwamnatin bude wannan filin jirgi.

Don haka, a safiyar ranar 12 ga watan Bahman (1 ga watan Fabrairu 1978), Imam ya iso birnin Tehran daga birnin Paris bayan shekaru goma sha hudu a gudun hijira. Su kuwa al'umma daman suna nan sun yi dafifi a wannan filin jirgin sama suna jiran abin kaunarsu ya iso. Hakika irin bukukuwa da kuma tarban da al'umma suka yi wa Imam, al'amari ne da ba zai iya siffantuwa a dan wannan shafi namu ba, don haka masu son su gani wa idonsu sai su nemi kasetin bidiyon tarbar don gane wa idonsu, don kuwa an ce sama da mutane miliyan shida ne suka yi dafifi tun daga filin jirgin saman zuwa Makabartar Beheshti Zahra don tarbar Imam.

Isowar Imam ke da wuya sai ya wuce wannan Makabarta ta Beheshti Zahra don girmama wadanda suka yi shahada a yayin wannan gwagwarmaya, inda kuma ya gabatar da wani jawabi mai sosa rai.

Ga kadan daga cikin abin da Imam ya fadi a yayin wannan jawabi nasa.

"Hakika mun fuskanci wahalhalu daban-daban...koda yake an samu manyan nasarori a yayin wadannan wahalhalu....ba zan iya biyan al'umma irin wahalhalu da kuma rashin da ta yi ba...ina rokon Allah Madaukakin Sarki da ya saka da kuma bada ladan hakan. Muhammad Ridha Pahlawi ya gudu bayan da ya lalata komai a wannan kasa, ya rusa wannan kasa kuma ya cika mana makabartanmu da (mutane). Ya lalata mana harkokin nomanmu, ya kuma mayar mana da al'adunmu baya. Muna da jami'oi tun sama da shekaru hamsin, to amma saboda ayyukan cin amanarmu da ya gabatar, babu wata ci gaba da aka samu..."

Bayan dawowar Imam ne da kwanaki goma aka kafa hukuma cikakkiya, kuma aka kori sauran mabarnatan da suka saura. A takaice dai aka sami cikakkiyar nasara da kuma kafa gwamnatin Allah. Don haka ne a kowace shekara akan gudanar da bukukuwan samun nasarar Juyin Juya Halin Musulunci a kasar Iran, daga ranar da Imam ya dawo har zuwa wadannan kwanaki goman da aka sami cikakkiyar nasara.


Nan al'umman Iran ne suke gudanar da bukin zagayowar ranar
samun nasarar Juyin Juya Halin Musulunci a dandali Azadi cikin birnin Tehran


JAGORANCINSA

Bayan dawowar Imam gida da kuma kafa daular Musulunci, Imam ya ci gaba da rayuwa da al'umma yana mai shiryar da su, kulawa da su da kuma bada shawarwari ga gwamnatin da al'umma ta zaba. Bugu da kari kuma, Imam ya cika dukkan alkawarin da yayi wa mutane na kasancewa tare da su da kuma da basu kariya da kuma shiryar da su kan yadda zasu gudanar da rayuwarsu da kuma kare su daga abokan gaba da kuma irin farfagandojinsu, al'amarin da ya sanya kaunarsa cikin zukatan al'umma. Irin goyon bayan da al'umma suka ba wa wannan jaririyar gwamnati ta Musulunci shi ya sanya har yanzu muke ganinta a raye kuma take tsaye da kafafunta duk kuwa da irin makirce-makircen da abokan gaba suke mata, baya ga irin ci gaban da kuma 'yancin da ta kawo wa al'umma ba kamar yadda da suka kasance ba.

Imam dai yaci gaba da rayuwa da mutane ne da kuma yi musu jagoranci har na tsawon shekaru goma, inda ya koma ga mahaliccinsa a ranar 3 ga watan Yuni shekarar 1989, bayan rashin lafiyar da yayi.

Ya Allah mu na rokonKa da ka gafarta masa, Ka albarkaci abin da ya bari, Ka sanya hakuri a zukatan al'umman Musulmi na duniya da kuma wadanda ake zalunta saboda wannan babban rashi da muka yi. Ita kuma wannan hukuma da ya kafa Ka ci gaba da kare ta har lokacin bayyanar Shugabanmu kana kuma Waliyinka (A.F.S), wanda na sanya wa wannan shafi nawa sunansa don neman tabarruki gare shi.