A+ R A-
29 February 2020

Rayuwar Magaba.….Manufa Da Tafarki

Babu shakka nazarin tarihin addinai a yanayi na gaba daya da kuma tarihin saukakkun addinai a kebance za su fitar mana da wata hakika guda, ita ce: cewa addinai – tun bayan bayyanarsu – sun gabatar da wasu tushe, dokoki da ladubba na musamman wadanda da su ne suka sami nasarar janyo mutane gare su, har suka zamanto al’umma guda a rayuwarsu ta zamantakewa. Sai dai daga baya – saboda wasu dalilai – wadannan addinai sun rarrabu zuwa bangarori da darikoki ma’abota akidu da ladubba mabambanta.

Al’ummar musulmi ma ba su tsira daga wannan hakika ta tarihi ba. Don kuwa bayan rasuwar Ma’aikin Allah (s.a.w.a) musulmi sun kasu zuwa tafarkoki da mazhabobi daban-daban. Hakan ya yi daidai da abin da aka ruwaito daga gare shi (s.a.w.a) inda yake cewa al’ummarsa za ta rabu zuwa kungiyoyi saba’in da uku; kamar yadda yazo cikin littafa da dama irin su Al-Firak bainal Firak da Buhuth fi al-Milal wa al-Nihal da dai sauransu inda a cikinsu aka ruwaito cewa Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: Yahudawa sun kasu kashi saba’in da daya (ko da biyu), Nasara (kiristoci) sun kasu kashi saba’in da daya (ko da biyu), al’ummata kuwa za ta kasu kashi saba’in da uku.

Babu shakka cewa wadannan sabani da bambance-bambance a farko-farkon lamari sun fara ne a dan karamin yanayi, daga baya kuma sannu-sannu sai suka fara girmama da yaduwa. Sai dai ba dukkan sabanin da suka faru kan lamurran addinin ne suka haifar da samuwar kungiyoyi da darikoki ba, face dai wadanda suke da alaka da lamurra masu muhimmanci a bangarorin akida ko shari’a kamar sabani kan tauhidi, ko batutuwan da suka shafi annabci da imamanci, ko ta tafarkin tafsirin Alkur'ani da fahimtarsa ko hanyar da ake samo sunnar Annabi da sauransu. Hakan ne ya haifar da samuwa da kuma bayyanar kungiyoyi daban-daban cikin al’ummar musulmi.

Masana suna ganin mas’alar imamanci da halifanci a matsayin mafi muhimmancin lamarin da ya haifar da rarrabuwa tsakanin al’ummar musulmi, tun daga lokacin da Manzon Allah (s.a.w.a) ya rasu har zuwa yau din nan. Shahristani cikin littafinsa na Al-Milal wa al-Nihal yana cewa: “Mafi girman sabanin da aka samu tsakanin al’umma shi ne sabanin imamanci (halifanci), saboda ba a tada jijiyoyin wuya (fada) tsakanin musulmi kan wani abu na addini a dukkan zamunna kamar yadda aka tayar kan imamanci ba”. Sabanin ya ginu ne kan ayyana wanda zai gaji Ma’aiki (s.a.w.a) a bayansa, wato wanda zai dauki nauyin jagorantar al’umma a bangaren addini da siyasa da kuma yadda za a zabe shi.

Wasu jama’a daga cikin musulmi sun tafi kan cewa dole ne halifan Annabi (s.a.w.a) ya zamanto yana da irin siffofin da Annabin (s.a.w.a) yake da su, kamar yadda dole ne, baya ga ismancinsa, ya zamanto mafi daukakan sahabbai a bangaren ilimi da aiki. Bisa la’akari da cewa gano wadannan siffofi sun fi karfin mutumin da ba ma’asumi ba, don haka dole ne shi Annabin ne (s.a.w.a) da kansa zai ayyana halifan da zai gaje shi bayansa. Hakan kuwa ya faru yayin da ya nada Aliyu Ibn Abi Talib (a.s) halifa kuma shugaban musulmi a bayansa. Ana kiran wadanda suka yi imani da hakan da sunan ‘yan Shi'a.

Wasu kuma ba sa ganin wajibcin cewa dole ne halifa ya zamanto yana da siffofi irin na Annabi (s.a.w.a), kamar yadda suka yi inkarin ayyana Imam Ali a matsayin halifa da Manzon Allah (s.a.w.a) ya yi. Wadannan mutane suna cewa ne Manzon Allah (s.a.w.a) ya bar wannan lamari ne a hannun al’ummar musulmi, wato su zabi wanda suke so. Ana kiran wadannan mutane da sunan ‘yan Ahlussunna, duk da cewa suna da wasu sunan na daban da ke nuni da kungiyoyin da suka fito da kuma sabanin da suke da shi kan wasu mas’alolin masu muhimmanci. Akwai sabani tsakaninsu kan kungiyar da ta fi dacewa da a kira ta da wannan suna, kamar yadda aka samu bayyanar sabani tsakanin ‘yan Shi'a kan mas’alar imamanci, lamarin da ya sanya suka kasu kashi-kashi.

Abin da yake da muhimmanci a yi ishara da shi a nan shi ne cewa wanda ya dare karagar halifanci bayan Ma’aiki (s.a.w.a) da rike madafan hukumci musamman jagorancin al’umma ba shi da wadannan siffofin da ‘yan Shi'a suka tafi a kansu na cewa dole ne halifa ya kasance yana da su, wanda hakan – a ra’ayinsu – ya cire masa duk wani halalci na shari’a. Hakan ne ya sanya tsawon tarihi suka fuskanci gallazawa da tursasawa daga wajen masu mulkin lokacin.

Wannan mummunan yanayi ya fi fitowa fili ne a lokacin mulkin Umayyawa da Abbasiyyawa. Littafan tarihi sun tabbatar da hakan yayin da ‘yan Shi'a suka fuskanci matsala da takurawa mai girman gaske a bangaren siyasa, tattalin arziki da ma zamantakewa. An ta kirkiran kararraki da zarge-zarge kan akidunsu har ta yadda aka zarge su da cewa sun fita daga Musulunci da kokarin yin zagon kasa wa Musulunci da kawar da tushensa a bayan kasa da dai sauransu. Duk da cewa nazari da bincike cikin adalci sun tabbatar da cewa akidun Shi'a sun fito daga tushen Alkur'ani da Sunnar Ma’aiki (s.a.w.a), da kuma cewa Manzon Allah (s.a.w.a) shi da hannunsa ne ya dasa tushen Shi’anci, shi ne kuma ya sanya mata wannan suna. Wannan dai ba shi ne bahasin da muke son yi a wannan bangaren don haka ana iya komawa ga bangarorin da suka yi magana da kuma karin bayani kan wannan bangaren.

Wani bangare na ilimin zaluncin da aka yi wa mabiya tafarkin Ahlulbaiti (‘yan Shi’a) a kebance da kuma al’ummar musulmi a yanayi na gaba daya shi ne irin gurbata tarihi da murguda shi da wadannan ‘masu mulki’ suka yi don cimma manufofinsu na siyasa da mulki. Abin nufi a nan shi ne irin yadda suka hana al’ummar musulmi sanin hakikanin wadanda ya dace su yi koyi da su, wato su zamanto musu abin koyi da riko da su cikin rayuwarsu don su zamanto musu hannunka mai sanda cikin rayuwarsu ta duniya wacce kuma za ta kai su zuwa ga sa’ada da kwanciyar hankali a rayuwar ta Lahira.

Wadannan mutane sun sauya tarihin wasu manyan bayin Allah wadanda su ne aka mana umurnin riko da su (kama daga Manzon Allah, har zuwa ga Ahlulbaitinsa da sauran sahabbansu da manyan mabiyansu) , inda suka mayar da su ba a bakin komai ba, wasu ma daga cikinsu suka boye tarihinsu babu wanda ya sansu kamar kai ka ce ma Allah bai halicce su ko kuma babu wata gudummawar da suka bayar. A bangare guda kuma suka fito da wasu mutane wadanda a hakikanin gaskiya tarihinsu cike yake da abubuwan da, kamar yadda malam Bahaushe yake cewa, ko kare ba zai ci ba, suka mai da su su ne ma jagororin addinin kana kuma abin koyi. Wanda hakan yana daga cikin abubuwan da suka sanya musulmi cikin wannan rudani da rashin mahanga da suke ciki a halin yanzu da kuma shekaru aru-aru din da suka gabata.

Don haka, wannan fili na “Rayuwar Magabata”, zai yi wa mai karatu dubi ne, duk da cewa a gurguje ne, cikin tarihin rayuwar wadannan gwaraza na tarihin Musulunci. Duk da cewa manufarmu ba ita ce bin tarihin wadannan taurari tiryan-tiryan ba, face dai manufar ita ce nuni da wasu bangarori na rayuwarsu masu muhimmanci da kuma sarkakiya don fitar da abin koyi wanda shi ne daman abin da aka yi kokarin boyewa din don kar su zamanto mana abin koyi, alhali kuwa Allah Madaukakin Sarki ya umurce mu da cewa: Hakika kuna da kyakkyawan abin koyi daga Manzon Allah, ga wanda ke fatan (saduwa da) Allah da Ranar Lahira….” (Suratul Ahzab 33:21). Shi kuma Manzon Allah din yana cewa: Lallai ni mai barin nauyaya biyu ne a cikin ku: Littafin Allah da Kebabbun mutan-gidana (Ahlulbaiti), wadanda matukar kun yi riko da su ba za ku taba bata a bayana ba..”

Har ila yau kuma a wasu lokuta za mu yi kokarin ishara da wasu bangarori na ‘kashin kajin’ da aka yi kokarin shafa wa wadannan mutane don gano manufar hakan da kuma fahimtar irin ta’annutin da aka yi wa tarihin al’ummar musulmi don cimma wata bakar aniya da kuma manufa ta siyasa.

Don neman tabarruki da yardar Allah a fitowa ta gaba za mu fara yin dubi ne cikin rayuwar Ma’aiki, Annabi Muhammadu (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da Alayensa) da irin yadda rayuwarsa ta kasance musamman a bangaren gina al’umma wanda a halin yanzu suna daga cikin abubuwan da al’ummar musulmi suke da bukatuwa da shi ganin irin yadda makiya suke ci gaba da yada bakar farfagandarsu a kan wannan Manzo da kuma sakon da ya zo da shi su ma dai don cimma wata manufa ta su ta siyasa da mulkin mallaka. A takaice dai za mu yi dubi ne cikin irin matsayi da daukakar da Annabi (s.a.w.a) yake da shi da kuma dalilan da suka samar masa da irin wannan matsayin, daga nan kuma sai mu yi dubi cikin irin hanyoyin da ya bi wajen gina al’ummar musulmi tun daga wannan zamanin har zuwa yau din nan.

Sai a biyo mu a fitowa ta gaba.

Walhamdu lillahi rabbil alamin.