A+ R A-
08 December 2023

Imam Ali (a.s), Shahidin Tabbatar Da Adalci A Tsakanin Bil’adama

Ranakun goma na karshen watan Ramalana mai alfarma, ranaku ne masu muhimmancin gaske ga al’ummar musulmi don kuwa ranaku ne da suke dauke da dararen “Lailatul Kadari” wadanda Alkur’ani mai girma ya bayyana su da cewa “sun fi watanni dubu” don kuwa “aminci ne a cikinsu har zuwa fitar alfijir”. Har ila yau kuma a cikin wadannan ranakun ne dai bil’adama a yanayi na gaba daya sannan kuma musulmi a yanayi na kebance suka yi babban rashin da Mala’ika ya bayyana shi da cewa “Lalle, wallahi an ruguza ginshikin (rukunin) shiriya” wannan rashi kuwa shi ne na Amirul Muminin Ali (a.s), wanda ya faru a ranar 21 ga watan Ramalanan.

Rayuwar Imam Amirul Muminin (a.s) cike take da abubuwa masu yawan gaske da suka hada da tsoron Allah, gudun duniya, jaruntaka, tausayi, kauna da dai sauransu, wadanda kowane guda daga cikin su mutum ya kalla zai ga wani gagarumin teku ne da sai dai iyakacin abin da mutum zai iya diba kawai na ruwan da ke ciki amma ba dai ya kure shi ba kamar yadda shi kansa ya ke fadi cikin sananniyar hudubar nan tasa ta Al-Shakshakiyya yayin da yake magana kan cancantarsa ga halifancin Annabi yake cewa: “….kwararar ambaliyar ruwa daga gare ni take gangarowa, sannan kuma tsuntsu ba ya iya kai wa wajena….”

To amma da ya ke muna ranakun shahadarsa ne, za mu dan yi dubi ne cikin wani bangare na rayuwarsa ne da ke da alaka da yanayi na zamantakewa, wanda kuma shi ne nake ganin dalilin shahadar tasa ko kuma alal akalla daga cikin manyan dalilan kashe shi d aaka yi. Wannan batu kuwa shi ne adalcinsa.

Idan har muka duba rayuwar Amirul Muminin (a.s) da kuma abubuwan da suka faru lokacin halifancinsa na shekaru biyar za mu ga cewa mafi girman matsalar da ya fuskanta ta samo asali ne daga kokarinsa na tabbatar da adalci cikin dukkanin lamurra na rayuwa. Don kuwa a wajensa tabbatar da adalci a tsakanin al’umma shi ne a kan gaba don haka ne ma a cikin huduba ta 224 na littafin Nahjul Balaga yake cewa: "Wallahi na fi fifita in kwana a kan tsinin icen sa’adan (wata irin bishiya ce mai kaya a jikinta) ko kuma a dinga ja na (a kan titi) daure cikin sarka, a kan in sadu da Allah da ManzonSa ranar Kiyama alhali ina mai zaluntar wasu daga cikin bayin (Allah) da kuma kwace wani abu na abin duniya".

Duk da karancin lokacin halifancin Imam Ali (a.s), to amma a aikace ya tabbatar da adalci; wanda hakan shi ne tushen matsalolin da masu adawa da adalcinsa suka haifar masa.

Kungiyoyi uku ne suka yi fada da Amirul Muminin (a.s), saboda wannan akida tasa ta tabbatar da adalci su ne:

1. Kungiyar Kasitin (azzalumai); wato Bani Umayya karkashi jagorancin Mu’awiyya. Mutane ne da suka kasance azzalumai; ba su taba yin imani da ginshikin Musulunci ba, shin cikin mulkinsu ne ko kuma cikin rayuwarsu. Don haka ba su yarda da tushen tabbatar da adalci da raba abubuwa cikin adalci ko aiki da adalci ba; don kuwa idan har suka ba wa adalci fage, to su ne gawar fari. Don haka suka kirkiro hanyoyi daban-daban don fada da adalcin Imam Ali, ciki kuwa har da batun fakewa da girmama sahabbai. Manufar su dai ba ita ce goyon bayan ra'ayin sahabbai ko kuma su kansu sahabban ba; manufar dai wani abu ne na daban kamar yadda Amirul Muminin (a.s) yayi ishara da hakan cikin wata wasika da ya rubuta wa Mu’awiyya (Ana iya duba littafin Nahjul Balagah huduba ta 28).

2. Kungiyar Nakisin (masu karya mubaya'ar da suka yi); wato tsoffin sahabban Amirul Muminin (a.s) wadanda suka gagara jure wa adalcinsa don haka suka kaurace masa. Mutane ne wadanda sun san Imam Ali, wasu daga cikin su ma sun taimaka wajen halifancinsa; amma sun gagara jurewa adalcinsa; don kuwa sun ga cewa sanayya da kuma zaman tare ba su da wani matsayi a wajensa, gaskiya da adalci su ne ma’auni a wajensa. Wadannan mutanen sun hada har da wasu manyan sahabbai irin su Talha da Zubair wadanda da farko sun yi masa mubaya’a da tunanin kare manufofin kashin kansu ne, to amma daga baya da suka fahimci cewa Imam Ali ba irin mutumin da zai bar su su cimma hakan ba ne, don tun ranar farko ya sanar da su da sauran mutanen da suka yi masa mubaya’a cewa: “duk wata dukiyar da aka ba wa wani da bai cancance ta ba, idan ya samu dama zai dawo da ita baitul mali” sai suka juya masa baya da haifar masa da matsaloli ciki kuwa har da yakin Jamal.

3. Kungiyar Marikin (Khawarijawa), su ne mutane masu tsaurin ra'ayi da wuce gona da iri cikin ra'ayi; ba tare da dogara da wani tushe da masaniya ta addini ba. Irin wannan yanayi na su ne ya sanya suka zamanto marasa matsaya guda, duk inda iska ta kada su sai su yi wajen. Babban misalin hakan shi ne a yakin Siffin, lokacin da mutanen Mu’awiyya suka tabbatar za su sha kashi, cikin yaudara sai suka daga Alkur'anai a kan tsirin masu, nan take suka fada tarkon yaudararsu suna masu matsa wa Amirul Muminin (a.s) kan dakatar da yakin, don a cewarsu ba za su yaki wadanda suka daga Alkur’ani ba. Cikin sauki aka yi wasa da hankalinsu, suka yi watsi da Imaminsu, wanda shi ne ma “Alkur'ani mai magana”. Daga baya kuma da suka fahimci cewa an yaudare su, sai ma suka ce kowa ma ya kafirta, Ali ma ya kafirta. Daga karshe dai su ne suka kashe Imam Alin (a.s).

Wadannan su ne kungiyoyi uku da suka yaki Amirul Muminin (a.s) a Siffin, Jamal da Nahrawan, duk kuwa saboda kokarinsa na tabbatar da adalci da ajiye abubuwa inda ya kamata.

Malaman tarihi sun yi bayani dangane da yanayin da Amirul Muminin (a.s) ya kasance bayan sararsa da Ibn Muljam yayi har zuwa lokacin shahadarsa. Daga cikin su akwai Lut bn Yahya Abu Mikhnaf wanda ya ce: “A lokacin da aka sari Imam (Ali), bai yi ihu ba”, wato bai yi wata alama ta jan hankulan mutane ba, abin kawai ya fara fadi shi ne: “Bismillah wa billah wa ala millati Rasulillah. Fuztu wa rabbil Ka’aba” (Wato: “Da sunan Allah, saboda Allah sannan kuma a bisa tafarkin Manzon Allah. Lalle hakika da Ubangijin Ka’aba, na samu babban rabo”. Daga nan sai ya daga murya don sanar da mutane halin da ake ciki, inda nan take suka nufo inda ya ke don ganin me ke faruwa. Koda suka zo sun same shi yana daure kansa, wato inda aka sara da kyalle sannan jini yana gudana a fuskarsa da kuma gemunsa, yana mai cewa: “Wannan shi ne abin da Allah da Manzonsa suka yi (min) alkawari, sannan kuma Allah da Manzonsa sun yi gaskiya”.

Mutanen garin Kufa da sauran garuruwan da suke gefe wadanda wannan labari ya zo musu sun shiga cikin halin damuwa. Don haka ne suka taru a kofar gidansa. Kamar yadda wata ruwaya ta nuna Imam Hasan al-Mujtaba (a.s) ya fito ya ga jama'a cikin kauna suna son ganawa da Amirul Muminina (a.s), sai yace musu: Ya ‘yan'uwana, ku yi hakuri ba zai yiyu ku ga Amirul Muminina ba saboda halin da yake ciki. Don haka ku yi hakuri ku tafi. Sai jama'a suka watse, sai kawai Asbagh Ibn Nubata (daya daga cikin manyan sahabban Imam Ali) ne ya saura ya ki tafiya, yana mai cewa duk kokarin da na yi kokari tafiya sai in ji na gagara. Bayan wani lokaci sai Imam Hasan (a.s) ya fito ya ganni ina tsaye sai ya ce min Asbagh ashe ba ka ji na ce jama'a su watse, ba za a iya ganin Amirul Muminina (a.s) ba. Sai na ce masa: Ya dan Manzon Allah, wallahi ba zan iya tafiya ba ne, ba zan iya daurewa in bar wajen nan ba, idan har zai yiyu a bar ni ko da na dan wani lokaci ne in gana da shi.

Daga karshe dai Imam Hasan (a.s) ya bar shi ya shiga. Ya ci gaba da cewa: Lokacin da na shiga na ga Amirul Muminina (a.s) a kwance a kan gado cikin rashin lafiya an daure kansa mai albarka, wato inda raunin yake. An daure kansa da wani kyalle mai launin rawaya, amma na gagara ganewa kyallen ne ya fi zama rawaya ko kuma fuskar Amirul Muminina (a.s) saboda tsananin halin da yake ciki sakamakon gubar da ke jikin takobin da aka sare shi da shi. Sai Asbagh ya matsa kusa da gadon da Amirul Muminina (a.s) ya ke kwance. Sai Amirul Muminina (a.s) ya kama hannun Asbagh ya gaya masa wani hadisi. Hadisi ne mai tsawo, amma daga cikin abubuwan da ya gaya masa har da wannan batu na tabbatar da adalci a tsakanin al’umma da muke yi, inda ya ce: “…Allah Ya la’anci wanda ya zalunci wani lebura (ko ma’aikacin da ya dauka aiki) cikin ladar aikinsa”. Wanda hakan na nuni da muhimmancin da Imam Ali (a.s) yake ba wa batun tabbatar da adalci a tsakanin al’umma hatta a gadon shahadarsa.

Abu Hamza Al-Thumali ya nakalto daga wajen Habib bn Amru cewa: a daren 21 (ga Ramalana), na tafi don ganin Amirul Muminin (a.s). Sai na sami daya daga cikin ‘ya’yansa mata a wajen tana ta kuka, sai na fashe da kuka. Lokacin da mutanen da suke wajen dakin suka ji kukanta sai su ma suka fara kuka. Amirul Muminin (a.s) ya bude idanuwansa ya ce: idan da a ce kuna ganin abin da na ke gani, to da ba ku yi kuka ba. Sai na ce: Ya Amiral Muminin me kake gani ne? sai ya ce: Ina ganin Mala’ikun Allah, ina ganin Mala’ikun sama, ina ganin dukkanin Annabawa da Manzannin Allah duk sun yi sahu, suna yi min sallama da maraba. Ina ganin Manzon Allah (s.a.w.a) a zaune a gaba na, yana kira na cewa Ya Ali ka zo mana, ka gaggauta zuwa. Ya ce: sai na zubar da hayawe sannan kuma na tashi, ban riga da na fita daga gidan ba, sai na ji kukan iyalan gidan. Sai na fahimci cewa lalle Ali ya bar duniya.

Amincin Allah ya tabbata a gare ka Ya Amiral Muminin . Allah Ka sanya mu daga cikin 'yan Shi'an Amirul Muminin (a.s) na hakika.