
Annabi Muhammad (s.a.w.a)…Manzon Rahama Da Kyawawan Halaye
- Details
- Published Date
- Written by Muhd Awwal Bauchi
- Category: Rayuwar Magabata
- Hits: 15862

Kamar yadda a makon da ya gabata muka yi alkawarin fara bude wannan fili na “Rayuwar Magabata” da dubi cikin tarihi da rayuwar Manzon Allah, Muhammad (s.a.w.a) don daukar darussan da suke ciki.
Girman matsayin da Annabinmu Muhammadu (s.a.w.a) yake da shi ya kasance wani yanayi maras tamka cikin tarihin bil’adama. Wannan girman matsayi kuwa ya samo asali ne sakamakon wasu dalilai masu yawa sai dai ana iya takaita su cikin wasu tushe ko mabubbuga guda hudu:
Mabubbuga Ta Farko: Zabi Na Ubangiji:
Siffa ta farko da Annabi (s.a.w.a) ya kebanta da ita wacce kuma ta ba shi irin wannan girman matsayi da yake da shi, ita ce cewa Allah Madaukakin Sarki shi ne Ya zabe shi da kuma kusato da shi kusa da Shi sama da dukkanin bil’adama, kai sama da dukkanin halittu ma; don kuwa Shi Ubangiji shi ne yake da wannan siffa kamar yake fadi cikin Suratul Kasas 28: 68: “Kuma Ubangijinka Yana halitta abin da Yake so kuma Yake zabi”. Allah Madaukakin Sarki, bisa mashi’arsa, Ya so ya samar da wasu ababen koyi, masu wasu siffofi na kyawu da kamala, a cikin bil’adama, don su zamanto musu abin koyi a rayuwarsu. Wadannan kuwa su ne Annabawa da Manzanni, wadanda su ne kolin kamala cikin bil’adama. Suna da duk wata siffa ta alheri da kamala, duk da cewa daukaka da falalar da suke da ita ta bambanta a tsakaninsu, kamar yadda Allah Yake fadin cewa: “Wadancan Manzannin mun fifita sashensu a kan sashe”. Cikin ikonsa kuwa sai ya sanya Annabinmu Muhammadu (s.a.w.a) shi ne mafifici da daukaka cikin dukkanin wadannan Annabawa da Manzannin.
Haka Allah Madaukakin Sarki Ya so Manzon Allah (s.a.w.a) ya kasance mafificin daraja da matsayi hatta a tsakanin Annabawa da Manzannin ballantana sauran bil’adama kuma. Shi ya sa ma kamar yadda ya zo cikin littafin Bihar al-Anwar, Manzon Allah (s.a.w.a) yana cewa: “Ni ne shugaban dukkanin ‘ya’yan Adamu. Ba bisa alfahari ba, ni ne kuma Cikamakin Annabawa kuma shugaban masu tsoron Allah, kana kuma Manzon Ubangijin talikai”. Daga wannan bayanin za mu iya fahimtar wannan hakika ta cewa shi ne mafificin daraja kana kuma mafi soyuwan halitta a wajen Allah Madaukakin Sarki, don kuwa kamar yadda ya zo cikin Suratul Hujurat 49:13: Lalle mafificinku daraja a wurin Allah, shi ne mafificinku a takawa (tsoron Allah)”, shin akwai wani mutum a fadin duniyar nan da za a iya kwatanta tsoron Allahnsa da na Annabi (s.a.w.a)? Babu. Ko shakka babu, shi ne mafi girman tsoron Allah cikin mutane, don haka shi ne mafi daukaka a wajen Allah.
Wannan zabi da Allah Yayi masa da kuma fifita shi bisa sauran bil’adama yana tattare da wasu abubuwa a wannan duniya da kuma lahira. Daga cikinsu kuwa har da abubuwan da riwayoyi suka zo da su da suke nuni da girman matsayin da yake da shi da suka hada da batun cewa shi ne mutumin farko da kasa za ta fara tsagewa don ya fito a ranar Kiyama lokacin da ake tayar da mutane. Da kuma cewa shi ne Annabin farko da zai fara neman ceto ga al’ummarsa a wajen Allah. Don kuwa al’ummomin sauran Annabawa za su tafi wajensu da bukatar su nema musu ceto a wajen Allah, to amma babu guda daga cikinsu da zai iya neman wannan ceton gabannin Annabi (s.a.w.a); haka nan kuma shi ne mutumin farko da za a bude masa Aljanna, sannan kuma shi ne mutumin farko da zai shiga Aljanna, kamar yadda aka ruwaito shi yana cewa: “Ni ne mutumin farko da zan kwankwasa kofar Aljanna, sai Mai gadinta ya ce: Kai ne wa? Sai in ce: Ni ne Muhammadu. Sai ya ce: Bari in tashi in bude maka, ban taba tashi don bude wa wani kafinka ba, sannan kuma ba zan tashi don bude wa wani a bayanka ba”. Shin akwai wani girman matsayin da ya wuce wannan?
Mabubbuga Ta Biyu: Girman Sakon Da Aka Aiko Shi Da Shi
Haka nan Allah Madaukakin Sarki Ya sanya sakon da Ya aiko Annabinmu (s.a.w.a) da shi, ya zamanto mafi cika da kamalar sakonsa zuwa ga bil’adama. A fili yake cewa Annabawan da suka gabata sun zo wa al’ummominsu da sakonni daga wajen Allah, to amma Allah Madaukakin Sarki Ya sanya sakon Musulunci ya zamanto shi ne mafi daukaka da kuma cikan dukkanin sakonnin da Ya aiko zuwa ga bil’adama. Saboda kuwa wani sako ne da ya tabo dukkanin bangarori na rayuwar dan’adam. Sako ne da ya damu da bangaren ruhi, kamar yadda ya damu da bangaren jikin dan’adam. Ya damu da duniya, a daidai lokacin da kuma bai yi watsi da lahira ba. Ya ba wa hankali muhimmanci, ba tare da kuma ya rufe ido ga bangaren tausayi ba. Don haka sako ne da ke da kamala da daidaito. Sako ne mai gyarawa da kuma shiryar da dan’adam a dukkan zamunna da kuma dukkanin bigirori, matukar dai aka fahimce shi hakikanin fahimta.
Mabubbuga Ta Uku: Kyawawan Halaye Da Dabi’u
Manzon Allah (s.a.w.a) ya kebanta da mafi kyawu da daukakar halaye, duk kuwa da irin wannan al’umma ta jahiliyya da ya tashi a cikinta. Mai yiyuwa ne za a iya fahimtar girman matsayin da wadannan halaye na Manzon Allah (s.a.w.a) ne idan aka yi la’akari da cewa sun bayyana ne a cikin wata al’umma wacce ta ke rayuwa cikin mafi kolin koma baya. Amma haka Annabi (s.a.w.a) ya rayu cikinsu da irin wadannan kyawawan halaye da dabi’u nasa ta yadda hatta makiyansa sun shaide shi da irin wadannan kyawawan halaye, don haka ne Allah Madaukakin Sarki Ya siffanta shi da cewa: “Lalle hakika kana a kan halayen kirki masu girma”.
Ko shakka babu Annabi (s.a.w.a) ya nuna wani irin hali da dabi’a maras tamka cikin wannan al’umma ta jahiliyya wacce ta ci baya. Saboda kuwa a fili yake cewa a lokacin da mutum yake rayuwa cikin wata al’umma ma’abociya ci gaba da kuma kyawawan halaye na gaba daya, ko shakka babu irin wadannan halaye da dabi’u za su yi tasiri cikin rayuwarsa, komai kashin tasirin kuwa. Haka nan idan aka sami akasin hakan. Tarihi ya shaida cewa al’ummar da Annabi ya taso a cikinta wata al’umma ce ta jahiliyya da dukkanin ma’anar kalmar. Al’umma ce wacce ta yi kaurin suna wajen rashin tausayi hatta a tsakaninsu, ina ga kuma wani na waje. Don haka ne ma ake ganin yadda rayuwarsu ta ke cike da yakukuwa da zubar da jini. A takaice dai ba a wuce gona da iri ba idan aka ce suna rayuwa ce irin ta dabbobi, mai karfi ya murkushe mara shi. To amma sai ga shi Manzon Allah (s.a.w.a) ya tashi a cikinsu amma da irin wadannan kyawawan halaye maras tamka duk kuwa da kiyayya da cutarwar da suke masa. An ruwaito cewa a lokacin da Annabi (s.a.w.a) zai tafi Da’ifa don isar da sakon Musulunci, mutanen Da’ifan sun cutar da shi cutarwa, da suka hada da zagi, cin mutumci, da kiransa da dukkanin sunaye na batanci irin su makaryaci, mai sihiri, mahaukaci, suna jifarsa da duwatsu har sai da suka farfasa masa jiki. Amma a irin wannan yanayi da yake ciki, a lokacin da Mala’ikun Allah suka zo suka ce masa: “Ya Muhammad, kai ne mafi daukakar halittun Allah, umurninka abin aikatawa. Gaya mana abin da kake so mu aikata da wadanda suka cutar da kai”. Riwayoyi sun ce ba Mala’ika guda ba ne ya zo, Mala’iku daban-daban ne suka zo da suka hada da masu kula da iska da ruwa da sauran abubuwa masu karfin gaske da suke tafiyar da duniya. Suna jiran umurninsa ne kawai. Amma duk da irin wannan yanayi da yake ciki, da irin wannan cutarwar da mushirikai suka yi masa, amma maimakon yayi musu addu’ar a halakar da su, sai ya daga kansa sama ya ce: “Ya Allah, Ka shiryi wannan al’umma tawa, saboda su din ba su sani ba ne”.
Assalamu alaika Ya Rasulallah! Wannan wani irin halitta ce? Shin akwai wani kyakkyawan halin da ya wuce wannan?
Irin wadannan kyawawan halaye na Ma’aiki (s.a.w.a) sun kara fitowa fili ne yayin mu’amalarsa da mafiya girman makiyansa wadanda suka shafe rayuwarsu wajen yakansa da kuma kashe masa wasu daga cikin mafiya soyuwa cikin sahabbansa. Duk da irin wannan kiyayya da cutar da shi da suka yi, amma a lokacin da ya samu nasara a kansu, wato ranar Fathu Makka, sai ya ce musu: “Ku tafi ku din nan ‘yantattu ne”. Kai abin ma bai tsaya nan ba, lokacin da Abu Sufyan ya zo wajensa ya ce masa: Ya Manzon Allah, ka yi afuwa wa dukkanin mutane kuma ni ma ina daga cikinsu, to amma da yake ni ina da matsayi a cikin al’umma ta, ina bukatar wata alfarma ta daban daga wajenka. Sai ga Manzo (s.a.w.a) ya rufe ido kan dukkanin kiyayya da Abu Sufyan ya nuna masa, inda ya ce: “Ku sani duk wanda ya shiga gidan Abu Sufyan ma ya tsira”. Haka ya aikata da Abdullah bn Ubaiy, shugaban munafukan Madina, wanda ya aikata abin da ya aikata wa Annabi (s.a.w.a), to amma a lokacin da ya zo mutuwa ya bukaci Annabi (s.a.w.a) da ya ba shi rigarsa don a yi masa likkafani da ita, haka Annabi ya amsa masa wannan bukata tasa.
Wannan wani bangare ne na irin wadannan kyawawan halaye na Ma’aiki (s.a.w.a) wadanda ya sami nasarar sauya tarihi da su.
Mabubbuga Ta Hudu: Nasarar Da Ya Samu
Hakika Manzon Allah (s.a.w.a), cikin dan karamin lokaci na rayuwarsa ya samu nasarar aiwatar da wasu manyan ayyukan da ake ganinsu a matsayin mafi girman nasara cikin tarihi. Irin wadannan ayyuka nasa kuwa sun ba wa mafiya yawa daga cikin masana da malaman tarihi hatta wadanda ba musulmi ba mamaki. A saboda haka ne ma babban masanin tarihin nan Ba’amurke Micheal H. Hart, cikin littafinsa: ‘The 100: A Ranking of the Most Influential Person in History wanda ya kumshi jerin sunayen mutane 100 da suka yi tasiri cikin tarihin bil’adama ya sanya Annabi (s.a.w.a) a matsayin mutumin farko cikin jerin wadannan sunayen. Mene ne dalilinsa na hakan, ga abin da ya ke cewa: “Zaben da na yi wa Muhammadu a matsayin mutum na farko a jerin sunayen manyan mutanen duniya zai ba wa wasu masu karatu mamaki, wasu kuma za su yi inkari; amma shi ne wani mutum makadaici a tarihi, wanda ya sami madaukakiyar nasara a dukkan bangarorin da suka shafi addini da ma wadanda ba su shafe shi (duniya) ba”. Marubucin ya ci gaba da cewa: Hakika Muhammadu ya samu nasarar kafawa da kuma yada daya daga cikin mafiya girman addinai a duniya, sannan ya zamanto daga cikin mafiya ficen manyan ‘yan siyasa. A irin wadannan ranaku sannan kuma bayan gushewar kimanin karnoni 13 da rasuwarsa, amma har ya zuwa yanzu yana da gagarumin tasiri”.
Wadannan su ne mabubbugar daukaka cikin tarihin Manzon Allah (s.a.w.a).
A hakikanin gaskiya a wannan zamanin da muke ciki da ake da hanyoyin sadarwa kala-kala sannan kuma ga irin gurguwar fahimta da wasu, shin makiya ne ko kuma wasu masoyan ma, suka yi wa tarihin rayuwar Ma’aiki (s.a.w.a), akwai bukatar sake dubi cikin tarihin rayuwar Ma’aiki (s.a.w.a) da mahanga ta zamani wacce hakan za ta kara fito mana da girman matsayin da yake da shi, da kuma magance mana wasu shubuhohi da wasu suke shigowa da su cikin wannan addini ta yadda ake ganinsa da wani irin kallo na daban.
Abu na biyu mai muhimmanci shi ne cewa sake dubi cikin rayuwar Ma’aiki (s.a.w.a) zai taimaka mana wajen tarbiyyartar da ‘ya’ya da kuma zuriyarmu. Don kuwa tarihin rayuwar Ma’aiki (s.a.w.a) cike yake da irin wadannan kissoshi da za su iya zama darasi ga rayuwar. A bangare guda kuma da isar da wannan sako zuwa ga sauran al’ummomin duniya, wadanda makiya suka cika kunnuwansu da wasu labarai marasa tushe dangane da shi kansa Manzo din da kuma sakon da ya zo da shi.
Da yardar Allah a fitowa ta gaba za mu yi kokarin bayani dangane da yadda rayuwar Ma’aiki (s.a.w.a) ta kiyaye da kuma tabbatar da karama da kuma mutumcin dan’adam wanda shi ne mafi girma da daukakar komai a gare shi sabanin ikirari na karya da wasu suke yi kan batun kiyaye hakkoki da kuma karamar dan’adam.
Wassalamu alaikum wa rahamatullah.