A+ R A-
08 December 2023

Mutumci Da Karamar Dan’Adam Cikin Shiryarwar Ma’aiki (s.a.w.a)

Kamar yadda a farko-farko muka yi alkawarin fara bude wannan fili na “Rayuwar Magabata” da dubi cikin tarihi da rayuwar Manzon Allah, Muhammad (s.a.w.a) don daukar darussan da suke ciki, inda muka fara da irin yadda Annabi (s.a.w.a) ya zamanto Manzon rahama da kyawawan halaye. To a yau za mu dora inda za mu yi dubi cikin wani bangare na  rayuwar Ma'aiki (s.a.w.a) din don daukar darussa daga wannan bangaren.

Hakika daga cikin manyan siffofin da sakon Annabinmu Muhammad (s.a.w.a) ya kebanta da su shi ne dawo wa dan'adam da irin kima da karamar ta yake da ita. Tsawon tarihi dan'adam ya rasa karamarsa da hakkoki da kuma mutumcinsa ta yadda an kai matsayin da mutum ba shi da wani mutumci musamman a karnoni na shida da bakwai miladiyya. A wadannan karnoni an nesanta dan'adam daga sakonnin Annabawan da suka gabata (a.s), ba abin da yake iko in ban da zalunci, babakere, fasadi da sauransu. Mutumci da karamar dan'adam ta fadi, kai dan'adam ma ba shi da wata kima ta azo a gani a wancan al'ummar. Idan har muka dubi tarihi za mu ga irin munin da yanayin rayuwa da dabi'un 'yan adam suka kai a cikin al'ummomi mabambanta.

Don haka Manzonmu (s.a.w.a) ya zo don ya tseratar da dan'adamtakar mutum da kuma daukaka karamarsa.

Hanyar da Ma'aiki (s.a.w.a) ya fara bi don cimma wannan manufa ita ce sanar da mutum kansa da motsar da shi wajen dawo da hakkinsa. Ba wai kiran masu fadi a ji din zuwa ga dawo wa mutum da hakkinsa da suka taushe ba. Face dai abu na farko shi ne shi kansa mutum din ya ji cewa lalle yana da wasu hakkoki, don haka sai ya tashi don nemansu. Don kuwa masu mulkin wancan lokacin ba mutane ne masu jin nasiha ba. Babban burinsu shi ne tabbatar da ikonsu a kan mutane. Don haka ne sakon Ma'aiki (s.a.w.a) ya dau wata hanya ta daban ta dawo wa dan'adam da dan'adamtaka da kuma karamarsa.

Manzon Allah (s.a.w.a) ya fara ne da shi kansa mutum din, ya kira shi da ya san matsayinsa don idan ya san hakan to zai yi kokari wajen kare shi. Wannan kuma wani lamari ne da su kansu masu mulki da iko na lokacin suka fahimta don haka suka fara jifarsa da wasu kalamai da kai kararsa wajen baffansa Abu Talib (a.s), suna masu cewa: Hakika dan dan'uwanka ya lalata mana matasanmu. Ma'anar lalata matasa a wajensu shi ne irin wannan kiran matasa da yake yi na su fahimci matsayinsu, su kuwa babban abin da suke so shi ne mutane su ci gaba da zama karkashin duhun jahilci wanda hakan zai ba su damar juya su yadda suke so. Alhali shi kuwa Musulunci ya zo ne don ya  kira mutum ya fahimci kimar da yake da ita. Don haka ne ma ya zo cikin Alkur'ani mai girma cewa: “Kuma lalle ne Mun girmama 'yan'adam kuma Muka dauke su a cikin kasa da teku, kuma Muka arzuta su daga abubuwa masu dadi, kuma Muka fifita su a kan masu yawa daga wadanda Muka halitta, fifitawa". (Suratul Isra' 17:70). Wannan aya dai tana gaya wa dan’adam ne cewa shi din nan ma’abocin karama ne don haka bai halalta ya yarda da rayuwar kaskanci da wulakanci ba. Don kuwa shi din nan yana a matsayin “halifan Allah” ne a bayan kasa kamar yadda wata ayar take nunawa.

A cikin littafin Wasa’il al-Shi’a an ruwaito Amirul Muminin Ali (a.s) yana cewa: “Allah Ya halicci Mala’iku da hankali amma babu sha’awa, Ya halicci dabbobi da sha’awa amma ba hankali, shi kuwa dan’adam Ya halicce shi da dukkansu biyu. Duk wanda hankalinsa yayi galaba a kan sha’awarsa, to ya fi Mala’ika. Wanda kuma sha’awarsa ta yi galaba kan hankalinsa, to ya fi dabbobi muni (sharri)”.

Don haka wajibi ne mutum ya san matsayinsa a wajen Allah, kamar yadda Manzon Allah (s.a.w.a) yake cewa: “Babu wani abu (wata halitta) da take da matsayi a wajen Allah sama da bil’adama”. A saboda haka ne Ma’aiki (s.a.w.a) ya fara da sanar da dan’adam kansa, matsayi da kuma karamar da yake da ita.

Don haka ne shari’ar da Manzon Allah (s.a.w.a) ya zo da ita ta sanya hakkokin dan’adam da karamarsa sama da dukkan komai. Idan muka duba za mu ga dukkanin shari’ar Musulunci tana magana da kuma lura ne da maslaha da kuma abin da zai amfani dan’adam. Don haka ne ake cewa daga cikin mafiya muni kana kuma abin da Musulunci ya fi kyama shi ne take hakkokin bil’adama. Nassosi da dama sun tabbatar da yiyuwar Allah Ya gafarta wa wanda yayi karen tsaye ga hakkokinsa Madaukakin Sarki na daga wasu abubuwan da ya hana. To amma a bangare guda ba ya gafarta wa wanda ya keta hakkin wani. Annabi (s.a.w.a) yana cewa: “Zalunci guda uku ne. zaluncin da Allah ba ya gafarta shi, zaluncin da yake gafarta shi da kuma zaluncin da ba ya rufe ido kansa. Amma zaluncin da ba ya gafartawa shi ne shirka. Zaluncin da Allah Yake gafarta shi, shi ne zaluncin da bayi suka yi a tsakaninsu da Ubangijinsu. Amma zaluncin da ba ya rufe ido kansa shi ne zaluncin bayi a tsakaninsu”. Daga wannan maganar za mu gane cewa Allah Madaukakin Sarki ba zai taba amincewa da wuce gona da iri ko take hakkin wani wani ba, ko wane ne shi din kuwa.

A daidai lokacin da Annabi (s.a.w.a) yake kokarin fahimtar da dan’adam kansa don ya fahimci irin matsayin da yake da shi, har ila yau kuma yayi kokarin samar masa da hanyoyin da zai kiyaye wannan matsayin; wannan hanyar kuwa ita ce hanyar girmama juna da kiyaye hakkokin juna. Don haka ne ma a cikin littafin Usul al-Kafi aka ruwaito Manzon Allah (s.a.w.a) yana cewa: halittu (mutane) iyalan (bayin) Allah ne, mafi soyuwar halittu a wajen Allah shi ne wanda yake amfanar iyalan Allah”. Haka nan a cikin Mustadrak al-Wasa’il an ruwaito shi (s.a.w.a) yana cewa: “Mafi alherin mutane shi ne mai amfanar mutane”. Haka nan a cikin wata ruwayar kuma an ruwaito shi yana cewa: “Mafi kaskancin mutane shi ne mai wulakanta mutane”. Abin la’akari cikin wadannan kalamai na Ma’aiki (s.a.w.a) shi ne yadda yayi amfani da kalmar “mutane” bai ce musulmi ko muminai ba, wanda hakan yana nuni da dukkanin mutane ne. Wato cin mutumci da wulakanta ko wane irin mutum, abin ki ne a wajen Allah Madaukakin Sarki.  

Shi ya sa ma Musulunci yake ganin wuce gona da iri a kan rayuwar dan’adam tamkar wuce gona da iri a kan dukkanin bil’adama ne. Allah Madaukakin Sarki, cikin Suratul Ma’ida, aya ta 32 Yake cewa: “…lalle ne wanda ya kashe rai ba da wani rai ba, ko barna a cikin kasa, to kamar ya kashe mutane duka ne…”, wanda hakan yana nuni da matsayin mutum ne a mahangar Musulnci.

To sai dai abin bakin ciki ne irin yanayin da musulmi suke ciki a halin yanzu sakamakon nisa da suka yi da koyarwar Ma’aiki ko kuma irin yadda wasu mutane suke fassara nassosi na addini don cimma wasu muggan manufofinsu.

Ko shakka babu idan muka yi dubi da kuma kwatanta yanayin musulmi da sauran al’ummomi, za mu yadda wadancan al’ummomin suke kula da hakkokin bil’adama ya bambanta nesa ba kusa da yadda yake a kasashen musulmi da suke ikirarin bin tafarkin Ma’aiki (s.a.w.a); wannan kuwa wata hakika ce mai dacin gaske, amma wajibi ne mu yarda da ita. Wajibi ne mu tambayi kanmu me ya sa jinin dan’adam a irin wadannan al’ummomin yake da matsayi mai girma amma a kasashen musulmi zubar da shi ya zamanto abu mafi sauki. A yau idan ka kalli kasashen musulmi za ka ga cewa babu abin da ya fi saukin zubarwa kamar jini, dan sabani kadan sai kisa, kisan nan kuwa babu bambanci shin a masallaci ne ko a kasuwa ko a makaranta ko a tashar mota da dai sauran wajajen taron jama’a inda gomomi kai wasu lokuta ma daruruwa suke rasa rayukansu ba tare da sun ci ko sun sha ba

A nan ba wai muna cewa ba a take hakkokin bil’adama a irin wadancan kasashe da al’ummomi ba ne, a’a su ma ana yi a wasu lokuta ma a mafi munin yanayi, amma abin da muke cewa shi ne irin yadda ake yi a kasashen musulmi din ne ya dara irin na su din nesa ba kusa alhali kuwa mu din nan muna da koyarwar Ma’aiki (s.a.w.a) a tattare da mu, muna da koyarwar Alkur’ani mai girma da ke cewa: “lalle ne wanda ya kashe rai ba da wani rai ba, ko barna a cikin kasa, to kamar ya kashe mutane duka ne” haka nan kuma “wanda ya raya rai, to, kamar ya rayar da mutane ne gaba daya” ko kuma koyarwar Shugaban Muminai Imam Amirul Muminin Ali (a.s), dake cewa: shi dan’adam “ko dai dan’uwanka ne a addini ko kuma tsaranka a halitta”.

Wannan dai ita ce koyarwar Musulunci, sannan kuma haka Ma’aiki (s.a.w.a) ya bi wajen tabbatar da mutumci da karamar dan’adam wanda ko shakka babu idan muka bi irin wannan koyarwa ta Ma’aiki (s.a.w.a) ba wai kawai musulmi ba hatta dukkanin bil’adama za su rayu cikin lafiya da kwanciyar hankali.

Sai a biyo mu a mako na gaba.