
Yadda Jagora Imam Khamenei Yake Kallon Rikicin Da Ke Faruwa A Iran
- Details
- Published Date
- Written by Muhd Awwal Bauchi
- Category: Rayuwar Magabata
- Hits: 2048

An jiyo daya daga cikin jami'an Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci na Iran (IRGC) yana fadin cewa: A yayin wata ganawa da Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei yayi da wasu kwamandojin IRGC din, Jagoran yayi magana dangane da rikicin baya-bayan nan da ke faruwa a Iran inda ya ce:
"Lalle ni kan ba na cikin damuwa ko kadan (kan wannan abin da ke faruwar), ina ganin lamurra ne ido bude kuma kamar yadda suke. A lokacin da sojojin Fir'auna suka hadu da Bani Isra'ila (mutanen Annabi Musa), lalle Bani Isra'ila sun tsorata da kuma girgiza sosai, don haka sai suka ce wa Musa, mene ne abin yi. Sai ya ce musu: Lalle Allah Yana tare da ni, ni kuma ina gaya muku cewa lalle Allah Yana tare da mu".