A+ R A-
08 December 2023

Muslim Ibn Akil, Jakadan Imam Husain (a.s)

Muslim bn Akil da yake wa baffan Imam Husain (a.s) wato Akil bn Abi Talib, kamar yadda kuma ya kasance yana da girman matsayi a wajen musulmi musamman ma mabiya tafarkin Ahlulbaiti (a.s) saboda irin rawar da ya taka wajen kare gaskiya a lokacin halifancin baffansa Ali bn Abi Talib (a.s) da kuma dan baffansa Imam Husain (a.s). An haifi Muslim bn Akil ne a garin Madina, a shekara ta 22 bayan hijira.

Muslim bn Akil ya kasance daga cikin fitattun mutane masu gaskiya da rikon amanna bugu da kari kan sadaukarwa wajen taimakon gaskiya da daukaka kalmar Musulunci. Ya samu irin wadannan siffofi ne kuwa sakamakon irin gidan da ya tashi da kuma irin tarbiyyar da ya samu. Don kuwa mahaifinsa shi ne Akil bn Abi Talib wanda ya kasane daga fitattun mutane kana kuma daga cikin wadanda Ma'aiki (s.a.w.a) ya ke tsananin kauna. Kamar yadda wata  riwaya da take komawa ga Ibn Abbas take fadin cewa: "Wata rana Imam Ali (a.s)  ya kasance yana zaune kusa da Manzon Allah (s.a.w.a) sai Akil ya zo ya wuce. Sai Imam Ali (a.s) ya ce wa Manzo (s.a.w.a): Ya Rasulallah, lalle kana son Akil. Sai ya ce masa: Na'am, Ya Ali. Lalle ina kaunarsa, kauna biyu: saboda kaunarsa da kuma kaunar mahaifinsa Abu Talib. Daga nan sai ya ci gaba da cewa: Ya Ali, lalle za a kashe dansa saboda son da yake wa danka Husain. Idanuwan muminai za su zubar da hayawe, haka nan ma Mala'ikun Allah za su yi kuka. Daga nan sai Annabi (s.a.w.a) yayi kuka mai tsanani har sai da hawaye suka zubo kan kirjinsa, yana cewa: Allah ina kai kuka na gare ka dangane da abin da Zuriya ta za ta fuskanta a baya na.

Wannan yana gwada mana irin matsayin da Akil da dansa Muslim suke da shi a wajen Ma'aiki (s.a.w.a).

Muslim bn Akil ya kasance tare da Amirul Muminin Ali (a.s) a yakin Siffin da ya gudana tsakanin Imam Ali (a.s) da Mu'awiyya a shekara ta 37 bayan hijira; inda ya kasance daga cikin kwamandojin Imam Ali (a.s) a yakin tare da 'ya'yansa Hasan da Husain (a.s); inda ya nuna gagarumar jaruntaka a yayin wannan yakin. Don haka taimakon gaskiya karkashin jagorancin zuriyar Ma'aiki (s.a.w.a) ba bakon abu ba ne a  wajen Muslim.

To sai dai tauraruwar Muslim bn Akil da kuma gagarumar sadaukarwar ta fi fitowa fili ne a lokacin yunkurin Ashura na Imam Husain (a.s) don fada da lalatacciyar gwamnatin Umayyawa karkashin jagorancin la'anannen Ali Yazid bn Mu'awiyya.

Sakamakon lalacewar yanayi da kuma bayyanar fasadi da lalata a fili tsakanin mahukunta da kuma yin watsi da duk wata doka ta Musulunci da Umayyawa suke yi musamman a lokacin mulkin Mu'awiyya da kuma nada asharari Yazid da Mu'awiyya yayi a matsayin halifan Musulmi da kuma neman tilasta wa Imam Husain (a.s) yin mubaya'a ga wannan sabuwar gwamnati ta Yazid, Imam Husain (a.s) ya kaddamar da wannan yunkuri na sa na 'yanto Musulunci da kuma musulmi daga wannan lalata ta Umayyawa daga garin Makka, lamarin da ya samu karbuwa a duniyar musulmi musamman a kasar Iraki a garuruwan Kufa da Basra inda mutane suka ta rubuto masa wasikun yin masa mubaya'a da kuma neman ya taho garin Kufan don kafa gwamnatin Musulunci ta hakika a can.

Don tabbatar da hakikanin wannan lamari, Imam Husain (a.s) yana bukatar aikewa da wani amintaccen mutum daga cikin mutanensa da za su gano masa hakikanin lamari. Don haka sai Imam (a.s) ya ba wa Muslim bn Akil wannan jan aiki, wanda hakan yana nuni da irin matsayin da yake da shi a zuciyar Imam Husain (a.s) da kuma irin yardar da yayi masa. Don haka sai ya rubuta wasika ya ba wa Muslim bn Akil ya kai wa mutanen Kufan yana ce masa: : Ka kama hanya zuwa Kufa, idan har abin da suka rubuto gaskiya ne to ka sanar da ni sai in same ka a can.

Don haka Muslim bn Akil ya bar bar garin Makka zuwa kasar Iraki ne a ranar 15 ga watan Ramalana shekara ta 60 bayan hijira tare da wasu mutane guda biyu wadanda za su dinga nuna masa hanya. Daidai wannan lokaci kuwa ana cikin tsananin zafin bazara, rana tana da zafin gaske ga kuma zafin hamada, ga kuma nisan wuri.  Wannan tafiya dai ta dauke su kimanin kwanaki 20 daga Makka zuwa Kufan, don kuwa Muslim ya isa Kufan ne ranar 5 ga Shawwal, inda ya sauka a gidan Mukhtar bn Abi Ubaidah al-Thakafi da kuma daukar wurin a matsayin helkwatar ayyukansa na siyasa a garin Kufa; inda ya ci gaba da ganawa da mutane da kuma karbar mubaya’arsu ga Imam Husaini (a.s), inda ya karbi mubaya’a mai yawan gaske daga mutanen garin; kamar yadda Al-Mas'udi cikin littafinsa na Muruj al-Zahab ya ce adadin mutanen da suka yi bai’ar sun kai mutane dubu goma sha takwas.

Lokacin da Muslim ya ga irin wannan yanayi da kuma irin wannan adadi na jama’a da suka mika wuya, nan take sai ya rubuta wa Imam Husaini (a.s) wasika da bayyana masa yadda al’amurra suke a Kufa da kuma irin ayyukan da ya gudanar, da bukatar ya iso. A bangare guda kuma ko shakka babu irin wannan yanayi ba zai buya wa Yazid da kuma gwamnansa na Kufan wato Nu’uman bn Bashir ba. Da farko dai Nu’uman bn Bashir ya so kawo karshen irin wannan yanayi ta hanyar ruwan sanyi sai dai abin ya ci tura. Irin siyasar da Nu’uman din dai ya dauka wajen magance wannan matsala ba ta yi dadi wa wasu daga cikin ‘yan amshin shatan wannan hukuma ba, suna masu tsoron rasa matsayin da suke da shi na siyasa da kuma zamantakewa, don haka sai daya daga cikinsu mai suna Abdullah bn Muslim (da ma wasu na daban irin su Ammara bn Ukbah da Umar bn Sa’ad bn Abi Wakkas) ya rubuta wa Yazid wani rahoto yana mai bayyana masa yadda al’amurra suke gudana da kuma irin hatsarin da ake ciki, don haka ya bukace shi ya da tsige Nu’uman bn Bashir a matsayinsa na gwamna da kuma aiko wani mutum mai kaushin hali wanda zai yi maganin lamarin da karfin tuwo.

Bayan isowar wadannan sakonni, sai Yazid ya fara tunani da kuma neman wani mutum wanda ya yi kaurin suna wajen ayyukan ta’addanci da rashin tausayi da imani, mai tsananin son mulki ko ta  yaya, haka nan kuma wanda ya fi kowa tsananin gaba da Ahlulbaiti (a.s). Don haka bayan bincike da shawarwari, bai ga duk wani mutumin da ya dace da wannan matsayi in ban da Ubaidullah bn Ziyad, wanda a wancan lokacin shi ne gwamnan Basra. Don haka sai ya ba shi wannan aikin, yana mai umartansa da ya yi amfani da tursasawa da kuma kaushin hali bugu da kari kan zubar da jinin duk wani dan’adawa har sai an kawo karshen wannan adawa ga hukumarsa.

Ba tare da bata lokaci ba Ubaidullah bn Ziyad ya kama hanyar Kufa zuciyarsa cike da fushi da mugunta, su kuwa mutanen Kufa suna nan cikin shirin tarbar Imam Husaini (a.s) duk kuwa da cewa da dama daga cikinsu ba su ma taba gani ko haduwa da shi ba. Don haka sai Ibn Ziyad ya yi amfani da wannan damar ya boye kansa ya shigo cikin garin sanye da bakin rawani ya kuma rufe fuskansa. Koda ya shigo garin sai ya dinga zagawa tituna-tituna na garin, su kuwa mutane (suna zaton Husain ne) sai suka fito suna ta masa barka da zuwa da kuma gaishe shi, suna cewa: “Amincin Allah ta tabbata a gare ka Ya Dan Manzon Allah”.

Wannan abin da ya gani dai ya ishe shi shaida kan irin kaunar da mutanen Kufa suke wa Husaini (a.s) da kuma gabarsu ga Yazid da hukumarsa; don haka sai ya wuce zuwa fadar mulki.

Da gari ya waye sai Ibn Ziyad ya mike yana mai gabatar da jawabi ga al’umma wadanda suka taru don salla, inda ya yi alkawarin aminci ga duk wadanda suka yi biyayya (ga hukumar Yazid) sannan kuma ya yi barazanar azabtar da duk wani wanda ya yi kokarin yin bore da kuma adawa da hukumar' wato yayi amfani da tsananin barazana da razanarwa. A bangare guda kuma ya baza 'yan leken asiri wajen nemo masa bayanai kan 'yan adawa da kuma inda Muslim bn Akil yake.

To fa daga nan ne lamurra suka fara sake zani, yanayi ya fara canzawa da dauka shakali na daban, tsoro da fargaba suka fara shiga zukatan mutanen Kufa da shuwagabanninsu. Ta haka ne jama'a suka fara gudu da kuma janyewa Muslim bn Akil, lamarin da ya tilasta masa sake tunani da kuma canza salon yadda yake gudanar da ayyukansa, sannan kuma ya kaura daga gidan Mukhtar al-Thakafi zuwa gidan daya daga cikin sanannun shuwagabannin mutanen Kufa kuma mabiyin Ahlulbaiti (a.s) wato Hani bn Urwah, ya ci gaba da zama a can a boye ba tare da kowa ya san inda ya ke ba. To amma dai daga baya sai da ‘yan leken asirin hukuma suka gano inda ya ke, kana kuma suka kai labari.

 

Jin haka sai Ubaidullah bn Ziyad ya kira Hani bn Urwah fadarsa ta yadda ba za a yi tunanin ko akwai wani abin da ya faru ba, ya aika masa kan ya zo su tattauna tsakaninsu don magance wasu matsalolin da suka taso. To amma shigan Hani fadar ke da wuya sai kawai ya gan shi a gaban kotu ana tuhumarsa, ga ‘yan leken asiri kuma suna shaidawa kan cewa shi yana daga cikin mabiya Imam Husaini (a.s), yana kuma shirya gagarumin yunkuri na yin bore wa hukuma da kuma tara kudade, makamai da jama’a ga Imam Husaini don yin bore wa hukuma sannan kuma ya boye Muslim bn Akil a gidansa. Hani dai ya yi kokarin musanta hakan da kuma kare kansa, to sai dai kuma Ubaidullah bn Ziyad ya fada masa da duka a fuskarsa da kuma zubar masa da jini, ya yi kokarin kare kansa da kuma mayar da martani ga Ubaidullah bn Ziyad din to amma an ce wai sarkin yawa ya fi sarkin karfi, nan take jami’an tsaron da ke gurin suka ci karfinsa suka kama shi. Daga nan sai Ibn Ziyad ya ba da umarnin a rufe shi a daya daga cikin dakunan gidan.

Ko da labarin kama Hani ya fito, sai ‘yan kabilarsa suka taru a kofar fada suna kira da a sako shi, to amma sai Ubaidullah ya yi amfani da wata hanya ta makirci ya tura Alkali Shurayh da ya fita zuwa gare su da bayyana musu cewa ba kama Hani a ka yi ba suna tattaunawa ne da sarki kan matsalolin al’umma kuma nan ba da jimawa ba zai fito, ta haka ne jama’an suka watse kuma aka kawo karshen wannan bore na ‘yan kabilar Hani.

Garin Kufa dai ya shiga cikin wani irin yanayi na tashin hankali da kuma zubar da jini tsakanin bangarori biyu. Labarai kala-kala kuwa sai yaduwa suke yi tsakanin al’umma da kuma batun kama Hani da dai sauransu, a waje guda kuma ‘yan leken asiri suna nan suna ta yada labarin cewa nan ba da jimawa wasu sojoji za su iso daga Sham (Siriya) don murkushe wannan bore da kuma azabtar da Muslim bn Akil da mabiyansa. A takaice dai tsoro, fargaba da rauni sai suka fara shiga zukatan masu yunkurin da kuma haifar da gibi a tsakanin wannan harka ta yunkuri da kawo canji.

A cikin irin wannan hali da ake ciki dai, Muslim bn Akil yana nan a boye yana darasin yadda lamurra suke gudana. Daga karshe dai ya kuduri aniyar tara jama’arsa don kai hari kan fadar sarki da kuma kawo karshen hukumar Ibn Ziyad din. Don haka sai ya tara mutanensa da suka riga suka yi masa bai’a da kuma alkawarin kasancewa tare da shi, inda suka kai hari ga fadar mukin. Da farko dai mutanen Ibn Akil suna samun nasara a kan mutanen Ibn Ziyad. To amma sai Ibn Ziyad ya turo ‘yan leken asiri cikin mutanen Muslim bn Akil a boye da nufin razana su da kuma raunana musu gwiwa, lamarin da a sannu a sannu yayi tasiri har aka fara samun wadanda suke gudu suna barinsa. Daga karshe dai duk suka gudu suka bar shi shi kadai a cikin masallacin Kufa bai san inda zai je ba kuma ba shi da wani wanda zai taimaka masa ko kuma kula da shi.

Haka dai Muslim ya fuskanci wannan sabon canji da karfin gwuiwa da kuma zuciyar da ba za taba mika wuya ba, ya fito yana ta yawo a kan titunan garin Kufan ko zai sami wata mafita, ko kuma ya sami hanyar da zai fice daga garin kafin a kama shi don ya samu damar isa zuwa ga Husaini (a.s), wanda ya ke kan hanyarsa ta zuwa Kufa, don sanar da shi halin da ake ciki da kuma hana shi isowa. 

Haka dai Muslim ya ci gaba da yawo a kan tituna da lungunan garin Kufa da suka kasance tsit saboda tsoro da fargaba, a bangare guda kuma ga shi an baza jami’an tsaro da ‘yan leken asiri don kamo wakili kana kuma manzon Imam Husaini (a.s) wato Muslim bn Akil. Yana cikin tafiya sai ya kai ga wani gida da wata mace take tsaye a kofarsa mai suna Taw’a, sai ya tsaya a kofar gidan cikin damuwa da jin kunya, ya bukace ta da ta taimaka masa da ruwan sha, ta shiga ta kawo masa ruwan. Bayan da ya sha ruwan sai kuma ya zauna a bakin kofar, cikin damuwa bai san inda zai je ba. A tattare da shi dai ga alamu na wahala da bakunta, wannan zama da ya yi a bakin kofar sai ya janyo hankalin wannan mata, inda ta matso kusa da shi ta ce masa; a a ashe ba ka gama shan ruwan ba? To ka tafi gidanka mana? Sai ya amsa mata da ce shi bako ne ba shi da gida kuma ba shi da iyalai a wannan gari, daga nan sai ya bayyana mata ko shi wane ne: “Ni ne Muslim bn Akil bn Abi Talib, wakilin Husaini kana kuma manzonsa ga mutanen Kufa”. Nan take ta bude masa kofa ta shigar da shi gidan don ya kwana a ciki daga baya kuma a ga mai zai faru washegari.

To sai dai kafin a samu hanya din, dan wannan mata ya gano inda Muslim din yake boye, don haka sai ya sanar da Ibn Ziyad, yana mai tsoro da kuma kwadayin samun kyautar da aka ce za a ba wa duk wanda ya kawo labarin inda Muslim ya ke. Don haka Ibn Ziyad ya turo sojojinsa karkashin jagorancin Muhammad bn Ash'as don su kamo shi. Koda suka shigo gidan Muslim dai bai mika kai ba inda ya fuskance su da yaki, yayi kaca-kaca da su, wasu bayanan sun ce sai da ya kashe sojoji 150, ganin haka ya sanya Ibn Ziyad ci gaba da karo sojoji. Daga karshe dai sun sami nasarar kama Muslim bayan wasu dabaru da suka yi amfani da su ta hanyar yin masa ruwan duwatsu da itatuwa daga saman gidan da yake suka tafi da shi  fadar mulki wurin Ibn Ziyad. A nan ma da Muslim bai mika kai ba don kuwa ya ci gaba da fadin kausasan maganganu ga Ibn Ziyad; wanda ya  kuduri aniyar kashe Muslim inda ya bukace shi in yana da wata wasiyya. Muslim ya amince da gabatar da wasiyyar tasa wacce ta kumshi abubuwa uku: (1). A sayar da takobi da garkuwarsa don biyan masa bashin da ke kansa. (2). A yi masa jana'izar da ta  dace. (3). Yana son a aike wa Imam Husain da sako cewa kar ya zo Kufa. Ibn Ziyad dai ya amince ya aikata na farkon amma ya ki ya  aiwatar da na biyu da ukun.

Daga karshe dai Ibn Ziyad ya umarci sojojinsa da su hau da Muslim kololuwar fadar, ya kuma ce wa Bakr bn Hamran al-Ahmari, wanda daman Muslim ya ji masa rauni mai girman gaske: ‘Karbi wannan takobin ka sare kansa, sannan kuma ka turo jikinsa da kan nasa kasa. Daga nan sai suka daure Muslim suka haura da shi kan soron yana fadin Allahu Akbar da kuma tsarkake Ubangiji don shirin gamuwa da wannan daraja mai girma ta shahada. Hakan kuwa ta faru ne a ranar 9 ga watan Zulhajji shekara ta 60 bayan hijira.

Ta haka ne dai aka kawo karshen wannan yunkuri na garin Kufa, wanda ya bude babban shafi cikin tarihi, kana kuma ya haifar da gagarumin yunkuri a nan gaba don rayar da Musulunci da kuma kawo canji da shiriya.