A+ R A-
25 May 2020

Gabatarwa: Imam Ali bn Abi Talib (a.s)

Gabatarwa:

________________________

 

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, Ubangijin talikai gaba daya, Wanda Ya halicce mu daga laka kana Ya tsara mana cikakken tsari kana kuma Ya fifita mu sama da dukkan halittu, sannan kuma Ya arzurta mu da hankali don mu yi amfani da shi wajen bambance gaskiya da karya. Sannan tsira da amincinSa su tabbata ga Annabin rahama, Cikamakin Annabawa kana kuma Shugaban Manzanni, Shugabanmu Annabi Muhammadu dan Abdullahi sw (s) tare da tsarkakan Mutanen gidansa, Ahlulbaiti, wadanda Allah Ta'ala Ya zabe su su zama taurari masu shiryarwa da kuma haskaka hanya ga dukkan muminai kana kuma Ya wajabta soyayya da kuma kaunarsu ga dukkan muminai. Tare da zababbun sahabbansa wadanda suka kasance tare da shi kana kuma suka taimaka masa tun daga farko har karshe ba tare da sun juya da baya ba, da kuma dukkan mabiyansu wadanda suke farin ciki da farin cikin-su kana kuma suke bakin ciki da bakin cikinsu, suke abuta da abokansu kana kuma suke gaba da makiyansu.

Bayan haka, shakka babu tarihin magabata ya kasance mana wani babban kogi dake shayar damu da kuma tabbatar damu kan abin da muka sa a gaba, bugu da kari kan kara mana karfin gwuiwa kan hakan. Su wadannan magabata sun kasance wata babbar fitila ce wacce take haskaka mana hanya da kuma tafarkin da muka zaba a rayuwarmu. Sannan kuma sun kasance wani babban tudu da kowa yake kwadayin ya hau shi don hango abubuwan da suka shiga masa duhu ko kuma suka yi masa nisa. Baya ga haka kuma, ta hanyar irin ayyukan da suka yi, muka sami cikakken karfin gwuiwa, sanin yadda zamu gudanar da rayuwarmu da kuma amfani da abubuwan da muke da shi da kuma wadanda muke tsammanin samunsu. Hakika, in ba don irin wadannan magabata ba, da mun fada cikin damuwa da dan da na sani, wanda aka ce wai keya ne.

Sannan kuma a matsayinmu na musulmai, wadanda suka yi imani da kadaitakan Ubangiji da kuma annabcin ManzonSa (s.a.w.a) da kuma littafinSa mai tsarki, mun san cewa Allah Madaukakin Sarki da ManzonSa (s.a.w.a) sun umurce mu da mu yi dubi cikin tarihi da rayuwar magabata don daukan darasi daga rayuwarsu, don mu taka inda suka taka suka tsira, sannan kuma mu guji inda suka taka, amma suka fada cikin rami. Koda yake, ko shakka babu, a lokacin da muke son tsara rayuwarmu kamar yadda Allah da ManzonSa Suke so, to dole ne mu yi koyi da irin rayuwar manyan bayin Allah, wadanda suka rayu cikin yi maSa da'a da biyayya, kana kuma suka koma gare Shi akan wannan tafarki ba tare da sun juya da baya ba. To lalle irin wadannan su ne zasu kasance akan gaba a lokacin da muke son yin koyi da magabata. Koda yake duk da cewa lokaci da kuma yanayi ya raba mu da su, to amma lokacin da kuma yanayin ba su raba mu daga sauraron kalamominsu ba, haka nan kuma ba su hana mu ganin abubuwan da suka bari ba.

To daga cikin irin wadannan magabata bayin Allah da suka kasance mana abin koyi kana kuma Allah da ManzonSa suka yi umurnin mu bisu, babu shakka Amirul Muminina Aliyu bn Abi Talib (a.s.) yana daga cikinsu, ko kuma ma a bayyane muna iya cewa shi ne ma na farkonsu - amma fa in ka cire dan'uwansa kana kuma sirikinsa, Manzon Allah (s.a.w.a.) - don kuwa babu wani musulmi da yake kokwanton fifikon Manzon Allah (s.a.w.a.) akan duk wata halitta da Allah Ya halitta ko kuma ma zai halitta a nan gaba.

Hakika rayuwar Amirul Muminina Aliyu (a.s.), wacce take cike da biyayya ga Allah da kuma ManzonSa (s.a.w.a.), sadaukarwa mai girman gaske wajen kare addinin Allah da kuma rayuwar ManzonSa (a.s.) da kuma musulmai gaba daya, rayuwa mai sauki da kuma tabbatar da adalci hatta ga wanda ba musulmi ba, da dai sauran duk wasu siffofi na gari, ta kasance mana da kuma duk wani ma'abucin gaskiya da adalci abin koyi da kuma jinjinawa.

To saboda irin wannan matsayi da yake da shi, ya sa manyan-manyan malumma da masana, musulmansu da ma wadanda ba musulmai ba, suka yi rubuce-rubuce kan wannan bawan Allah. A'a me zai hana su yin hakan, bayan kuwa shi ne mutumin da yafi kowa tsoron Allah. Me zai hana su yin hakan, bayan kuwa shi ne wanda yafi kowa yin hidima wa Musulunci da kuma 'yan Adam. Me zai hana su yin hakan, bayan kuwa shi ne mutumin da yafi kowa jarunta. Me zai hana su yin hakan, bayan kuwa shi ne mutumin da yafi kowa daraja da daukaka a wajen Allah da ManzonSa. Me zai hana su yin hakan, bayan kuwa shi ne mutumin da masoyansa suka boye falalolinsa saboda tsoro, sannan makiyansa kuma suka boye su saboda kiyayya, amma sai da falalolinsa suka kere na kowa. Me zai hana su yin hakan, bayan kuwa shi ne kofar ilimi da hikimar Manzon Allah (s.a.w.a.). Me zai hana su yin hakan, bayan kuwa shi ne………. Me zai hana su yin hakan, bayan kuwa shi ne…………….Me zai hana su yin hakan, bayan kuwa shi ne…………

Hakika duk da irin wadannan rubuce-rubuce da aka tayi kan Amirul Muminin (a.s.), to amma abu ne wanda yake a fili cewa wadannan rubuce-rubuce sun gagara kana kuma sun gaza su bayyanar da hakikanin yanayi da kuma matsayin wannan Jan gwarzo. A'a, yaya ma za su iya rubuta hakikanin mutumin da dan'Adam ya gaza wajen sani da kuma fahimtar hakikaninsa? Yaya za su iya bayanin mutumin da babu wanda ya san hakikaninsa in ban da Allah da ManzonSa?

To saboda la'akari da wannan matsayi da Amirul Muminin (a.s.) yake da shi da kuma dan karamin binciken da nayi kansa da kuma dan abin da na fahimta na daga matsayinsa….ya sanya ni na ga cewa ni ma ya kamata in bi sahun wadannan marubuta, duk kuwa da cewa alkalami na bai kai ko kusan irin nasu ba, don ni ma in dan rubuta wani abu kan Amirul Muminin Ali (a.s.).

To don haka ne ya sa na dauki wannan gutsurarren alkalami nawa, ina mai dogaro da Allah da kuma neman izinin ManzonSa (s.a.w.a) wajen rubuta wani abu kan wannan Shugaba nawa wanda yafi soyuwa a gare Su akan kowa kana Su kuma Suka fi soyuwa a gare shi sama da komai da kuma kowa.

Ina rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya bamu daman ganin gaskiya da kuma riko da ita, koda kuwa daga wajen wanene ta fito, kana kuma ya bamu daman ganin karya da kuma watsi da ita koda kuwa daga wajen wanene ta fito.

Amincin Allah Ya tabbata a gare ka Ya Amiral Muminin, ranar da ka aka haife ka, ranar da ka yi shahada da kuma ranar da za a tasheka rayayye kana mai ceton wadanda suka yi riko da tafarkinka.

 
ALHAMDU LILLAHI RABBIL ALAMIN.