A+ R A-
25 May 2020

Ali Lokacin Halifofi

Ali (a.s) Da Halifofi:

________________________

Ran Manzon Allah (s.a.w.a) ya fita a lokacin yana kwance a cinyar Ali (a.s), ya tafi zuwa ga Ubangijinsa alhali yana cikin damuwa da irin halin da sako da al'umma za su shiga nan gaba. Domin a sa'ar karshe ta rayuwarsa ya bukaci a ba shi tawada da takarda ya rubutawa al'umma abin da ba za ta bata ba a bayansa har abada matukar dai suka yi riko da shi, amma sai aka hana haka, don haka ya yi wa Ahlubaitinsa wasici da alheri(1).

Lokacin da Ali (a.s) da sauran iyalan Manzo (s.a.w.a) suka shagaltu da shirya Manzo don bisne jikinsa mai tsarki a makomarsa ta karshe, sai wasu jama'a daga Ansar suka kira wani taro a zauren taron Sakifa na Bani Sa'idah don su nasabta wanda zai halifanci Annabi wajen jagorancin Musulmi.

Labarin na isa kunnen Muhajirai sai suka gaggauta halartar wajen taron; bayan ka-ce-na-ce- mai karfi da tsawo wanda ke tattare da wani yanayi na rashin jituwa, sabani da rikici, sai halifa Umar dan Khaddabi ya gaggauta yi wa Abubakar mubaya'a, ya kuma bukaci wadanda ke wurin da su yi haka, sai wasu suka yi mubaya'a yayin da wasu suka ki yarda.

Har zuwa wannan lokacin Imam Ali (a.s) da sauran iyalan Annabi ba su gushe ba suna shagalce da aikin jana'izar Manzon Allah (s.a.w.a), domin gawarsa mai daraja ta saura har na kwanaki uku ba tare da an bisne ba, wannan kuwa don ya ba Musulmi daman yi masa salla da yi masa gani na karshe.

Saboda rashin amincewar Imam Ali (a.s) da abin da ya faru, ya ci gaba da zama cikin halin amanna da hakkinsa na halifanci, ya kuma janye daga mutane da harkokinsu har na tsawon watanni shida, ba a jin sunansa cikin abin da ake kira da Yakokin Ridda da wasunsu(2).

Hakika wasu al'amurra masu hadurra sun bayyana wadanda kuma suka so yin barazanar rusa Musulunci da al'ummarsa; yayin da al'amarin masu da'awar annabcin karya ya karfafa a bayan rasuwar Manzo (s.a.w.a), Hadarin su ya tsananta a tsibirin larabawa. Haka nan harkokin munafukai ma ya karfafa, inda suka kara kaimi a cikin Madina; a wani bangare ga Romawa da Farisawa sun ja daga suna jiran Musulmi, duk wadannan na daga cikin rikice-rikicen siyasar da ke barazana ga al'ummar Musulmi a sakamakon bai'ar Sakifa.

To sai duk da haka Imam Ali (a.s) ya fuskanci harkar halifanci daidai da yadda maslahar Musulunci ke hukuntawa, don kare Musulunci da kare jama'ar Musulmi daga kacancanewa da lalacewa, da kuma tabbatar da babbar maslahar Musulunci wadda ya dade yana jihadi don ita; dangane da hakan an ruwaito shi yana cewa:

"Sai na kame hannuna har sai da na ga inda mutane suka dosa, sun kauce daga Musulunci, ana kiran su zuwa danne addini Muhammadu (s.a.w.a); sai na ji tsoron in har ban taimaki Musulunci da mutanensa ba, zan ga baraka ko gibi a cikinsa, (wanda) musifar haka a kaina za ta fi tsanani fiye da kufcewar shugabancinku, wadda ba ta kasance ba face jin dadin kwanaki kadan, abin da ya kasance daga gare shi zai wuce kamar rairayi, ko kamar yadda girgije ke yayewa; don haka sai na yunkura a cikin wadannan rikice-rikice har sai da barna ta kau, addini ya natsu ya zauna da gindinsa(3)".

Hakika ana jin sautin Imam Ali (a.s) a duk lokacin da aka nemi shawararsa, yana bayani a duk lokacin da aka nemi fatawarsa; ya himmatu da fuskantar da rayuwar Musulunci dai-dai da yadda sakon Allah Madaukaki ya yi tanaji a fagagen shari'a da hukunci.

A duk wannan lokacin, tun daga rasuwar Manzon Allah (s.a.w.a) har zuwa lokacin da ya zama halifa, Imam Ali (a.s) ya kasance yana tsaye wajen sauke babban nauyin Musulunci da ke kansa a lokacin halifofi; ba abin da ke yunkura shi a kan haka face kyakkyawar niyyarsa ga sakon, kiyaye hadin kan Musulmi da kare ci-gaban Musulunci daga karkacewa.

Don haka mai nazarin tarihin wannan lokacin, zai ga wasu halaye masu yawa da fare-fare da al'amurra da in ba Imam Ali (a.s) ba, babu mai iya gyara su da magance su bisa shari'a da bayyana hukuncin Allah a cikin su da kiyaye sunnar Annabi (s.a.w.a).
 ____________

(1)- Bukhari, cikin littafin Ilimi, juzu'i na 1, shafi na 21; da Muslim, a karshen littafin Wasiyyah, juzu'i na 3, shafi na 259, da Ahmad bin Hambali, cikin Musnad, da wasun wadannan.

(2)- Shaikh Ridha al-Muzaffar, cikin al-Sakifa, shafi na 160.

(3)- Nahajul-Balagha, shafi na 451,tsarin Subhi Saleh.