A+ R A-
23 July 2019

Imam Husain (a.s) A Karbala

A ranar biyu ga watan Muharram mai alfarma na shekarar hijira ta 61 ne Imam Husaini (a.s.), shi da mutanen gidansa da Sahabbansa suka isa sararin Karbala, wanda zai zama wani dauwamammen tsaiko ga 'yantattu, kuma take ga masu ra'ayin juyi a tsawon tarihi da zamuna.

Mahukuntan Umayyawa kuwa karkashin jagorancin Ubaidullahi bin Ziyad a Kufa, sun shiga aikawa da dakarunsu da duk wani iko na su na soji. Sai Ibn Ziyad ya nada Umar bin Sa'ad a matsayin kwamandan rundunar. Da farko Umar bin Sa'ad ya nemi uzuri, saboda ya san matsayin Imam Husaini (a.s.) a wajen Manzon Allah (s.a.w.a); sai dai bayan barazanonin Ibn Ziyad na cewa zai kwace mulkin Rayyu da aka rubuta cewa shi aka ba, sai ya mika kai bori ya hau. An ji Umar bin Sa'ad na maimaita wasu baitoci da cewa:

Shin zan bar mulkin Rayyu alhali ita nake kwadayi.

Ko zan koma abin zargi ne ta hanyar kashe Husaini.

A cikin kashe shi akwai wuta wadda a tare da ita.

Babu shamaki, alhali ga mulkin Rayyu sanyin ido(1).

Umar bin Sa'ad bai kasance ba face misalin irin mutanen da suka yaki Imam Husaini (a.s) saboda wasu wulakantattun manufofi da abin duniya da bai taka kara ya karya ba.

Haka dai ya wulakantar da kansa ya karbi wannan aiki, ya jagoranci rundunarsa da ke kunshe da mayaka dubu hudu da suke dauke da niyyar yaki da Husaini (a.s.).

Umar bin Sa'ad ya isa Karbala, sai ya yi wa hemomin Imam Husaini (a.s.) kawanya da sojojinsa. Da farko dai Imam Husaini ya bude kofar tattaunawa da shi, har suka tsaya a kan cewa zai kyale Imam Husaini ya isa Kufa ba tare da yaki da zubar da jini ba.

To sai dai kuma don neman izini, Umar bin Sa'ad ya aika da wannan shirin zuwa ga Ibn Ziyad, don jin mene ne ra'ayinsa. Da farko dai Ibn Ziyad kamar zai amince da hakan, to amma sai Shimr bn Zil-Jaushan, wanda ke cikin wadanda suka fi tsananin kiyayya da Ahlulbaiti (a.s.), ya nuna masa cewa hakan ba zai taba sabuwa ba. Don haka sai Ibn Ziyad ya rubuta wa Ibn Sa'ad jawabin wasikarsa ya ba wa Ibn Zil-Jawshan da ya kawo masa. Ga abin da wasikar ta kunsa:

"Ka duba ka gani, idan Husaini da Sahabbansa sun sassuto sun mika wuya ga mulkina to ka aiko min da su hankali kwance. Amma idan suka ki to ka ja daga da su har sai ka kashe su ka wulakanta gawawwakinsu, domin haka suka fi cancanta. Idan aka kashe Husaini ka yi sukuwar salla da dawaki a kirjinsa da bayansa(2)".

Haka jahilin tunanin Ibn Ziyad ya sa shi nacewa a kan zubar da jininsa wulakanta gawawwakin wadanda aka kashe, kamar yadda haka ya kasance dab'ar magabatansa a lokacin jahiliyyar Kuraishawa, wadanda suka wulakanta gawar Hamza baffan Annabi (s.a.w.a).

Kenan babu makawa sai an gwabza. Imam Husaini dai ba zai sassauto daga kudurin nan shi na: "Irina ba ya mubaya'a ga irin su Yazidu " ba duk kuwa abin da zai kasance. Don haka bai gushe ba yana maimaita fadar cewa:

"Ni ba na ganin mutuwa face dacewa, rayuwa da azzalumai kuwa (ba komai ba ce) sai kunci da tabewa".

Bai gushe ba yana rike da takensa da ya gada daga Manzo (s.a.w.a), wanda ya yi magana da Umayyawa da shi a 'yan kwanakin da suka gabata da cewa:

Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: "Duk wanda ya ga ja'irin mai mulki, mai halalta abin da Allah Ya haramta, mai karya alkawarinSa, mai sabawa sunnar Manzon Allah (s.a.w.a), yana aiki, a cikin bayin Allah, da sabo da kiyayya; sannan [wanda ya ganin]bai canza abin da [mai mulkin] ke kai da aiki ko da magana ba, Allah na da hakkin Ya shigar da shi mashigarsa [azzalumin](3)".

Imam ya yanke kauna daga wannan gungu na taron marasa fahimta da irada, don haka sai ya bukaci dan'uwansa Abbas da ya tattauna da su a kan su ba Imam Husaini zuwa daren goma ga Muharram don ya ba su kudurinsa na karshe. Sai Abbas ya mika wannan bukata kuma Umar bin Sa'ad da manyan jami'an rundunarsa suka jinkirtawa Imam Husaini (a.s.) na dare daya.
 ____________
1- Al-Kamil fil-Tarikh, na Ibn Athir, juzu'i na 4, shafi na 52 da na 53.

2- Shaikh al-Mufid, cikin Kitab al-Irshad, shafi na 229.

3- Ibn al-Athir, cikin al-Kamil Fi al-Tarikh, juzu'i na 3, shafi na 48.