A+ R A-
23 July 2019

Hanyar Imam Husaini (a.s) Zuwa Kufa

Damuwa ta kai wa mahukuntan Umayyawa ko'ina yayin da shugabanninsu suka riski cewa Imam Husaini (a.s.) ya hado, ko ya yi gab da ya hado, garin Makka tare da yunkurinsa, sai Yazidu ya aika da wata runduna daga Sham, ya nada mata Amr bin Sa'ad bin أs a matsayin babban kwamandanta.

Yayin da labarin daura damarar Umayyawa zuwa Dakin Allah mai alfarma ya isa ga Imam Husaini (a.s.), sai ya ki abin da zai keta hurumin Dakin saboda masaniyar da ya ke da ita na cewa Yazidu da sojojinsa ba sa girmama hurumin Dakin balle mahajjatansa; don haka sai ya kudurta fita daga Makka da fuskantar Iraki, tare kuwa da cewa shi ya san sakamakon da zai biyo bayan hakan, kamar yadda haka ke bayyana daga hudubarsa yayin da ya fito daga Makka, inda ya ce:

"Godiya ta tabbata ga Allah. Kuma (ba abin da ke kasancewa) sai abin da Allah Ya so. Haka ba wani karfi sai ga Allah. Allah Ya yi tsira ga ManzonSa. Zanen mutuwa a wuyan 'yan Adam kamar zanen sarka ne a wuyan budurwa. Bakin cikina a kan magabatana (na rabuwa da su) bai kai kaunar (Annabi)Yakubu ga (Annabi) Yusuf ba. Abin da ya fi alheri gare ni shi ne tashin hankalin da zan hadu da shi. Kamar gani nan masu suka na daddatse gabbaina a Karbala su cika min ciki da suka, da lullube ni da kaifin takobi. Ba makawa da wata rana da aka rubuta da Alkalami (na kudura)(1)".

A ranar takwas ga watan Zul-hijjah na shekarar hijira ta 60 ne Imam Husaini (a.s.) ya jagoranci tawagarsa.

A hanyar zuwa Iraki ya kasance yana haduwa da matafiya yana tambayar su halin da mutane ke ciki a Iraki. To sai dai amsar da ya samu ita ce: "Takubban mutane na tare da Umayyawa alhali zukatansu na tare da kai."

Tare da cewa Imam Husaini (a.s.) na da tabbas cewa al'ummar nan ba za ta farka ba sai wani babban al'amari ya girgiza ta; to bari girgizawar shahadarsa tare da wadanda ke tare da shi na daga zuriyar Manzon Allah (s.a.w.a) ta zama mai girgizawar.
 ____________
1- Kamar na sama.