A+ R A-
25 May 2020

Nokewar Mutanen Kufa

Da farko 'yan kungiyar Umayyawa masu mulkin Kufa sun sami kadawar hanji mai tsananin gaske a lokacin da suka ga alamun nasara na nufin bangaren Imam Husaini. Don haka sai suka rubuta wasika zuwa shugabansu Yazidu a Sham, suna fahimtar da shi sabon yanayin da Kufa ta shiga.

Hankalin Yazidu ya tashi da wannan labari, don haka sai mai ba shi shawara na musamman ya ba shi shawara da ya ba Ubaidullahi bin Ziyad shugabancin Kufa, saboda irin kaushin zuciyarsa da yadda yake jin dadin kisan kai, ga shi da ma bai san ma'anar tausayi da jinkai ba, ga kuma bakar kiyayyar da yake da ita ga Iyalan Manzon Allah (s.a.w.a).

Ibn Ziyad ya karbi aikin da Yazidu ya ba shi, sai shi kuma ya nada dan'uwansa a mulkin Basara shi kuwa ya nufi Kufa da wata runduna mai sojoji dari biyar, kamar yadda ya tafi tare da wasu shugabannin Basara tare da shi, wadanda ke da tasiri mai karfi a tsakanin kabilun Kufa saboda dangantakar da ke tsakaninsu.

A Kufa Ibn Ziyad ya gaggauta tara mutane ya yi musu jawabinsa na farko, wanda ya kunshi fadadden yaudarar nan da suka saba tare da baraza kala-kala da basu kasa na kisa ba ga duk mutumin da ya mike don yin hamayya da zaluncin Umayyawa.

Daga nan sai ya hori shugabannin kabilu da mutane da su gabatar da sunayen duk wadanda suka kauce daga tafarkin Umayyawa da aka shata, da cewa ukubarsu za ta kasance ratayewa ne a kofar gidan kowane mutum aka samu da haka.

Haka Kufa ta shiga wani yanayi na mummunan firgici; sai al'amura suka sauya daidai da muradin Umayyawa, yayin da aka kashe shugabannin 'yan Shi'ar Ahlulbaiti da masu jibintar yunkurin Musulunci da Imam Husaini (a.s.) ke jagoranta.

Ta hanyar 'yan leken asiri da mabiyansa, Ibn Ziyad ya yada karyar cewa akwai tarin sojojin Umayyawa jibge a kofofin Kufa. Wannan ya haifar da yaduwar jita-jita a garin, kuma hakan ya girmama a zukatan da suka raunana. Don haka sai halin dar-dar ya karu kuma tsoro ya yadu, ta yadda sai mace ta hana mijinta fita da tilasta masa gudu, mutum ya hana dansa ko dan'uwansa(1)har dai mafi yawa daga sojojin Muslim suka gudu, tsoro kuma ya fi karfin wadanda ba su gudun ba.

Bure-buren duniya ma na da nasu gudummawar, don haka sai kokarin janyewa ya yi nasara, ta yadda babu wanda ya saura tare da Muslim ban da wasu 'yan tsiraru daga masu kyakkyawar niyya, wadanda suka saura tare da shi cikin yakinsa, suka koma suka ja tunga a Kindah da ke Kufa.

Muslim ya nuna gwarzontakar da irinta ya karanta, ya yi yaki irin na gwaraza har zuwa lokacin da raunuka suka yi masa yawa, sai aka kama shi aka kashe, inda ya yi shahada a saboda Allah da SakonSa. Da haka sai yunkurin ya rasa daya daga manyan jagororinsa na farko a Iraki.

Haka Ibn Ziyad ya kashe Hani bin Urwah, wanda ya kasance daga shugabannin Kufa da suka taimaki Muslim.
 ____________
1- Abdurrazak Mukarram, Maktalul-Husaini, shafi na 193.