A+ R A-
23 July 2019

Me Ya Kawo Wannan Yunkurawa Na Imam Husaini (a.s)

Yayin bin rayuwar Imam Husaini (a.s.) da irin sabbin abubuwan da ya shaida da yanayin da ya kewayu da shi, za ta bayyana karara gare mu cewa bai mallaki na'urorin zahiri da za su samar masa da nasara a yayin yakinsa da azzaluman mahukuntan Umayyawa ba. Sai dai tare da masaniyar da yake da ita na mutuwa, ya dage a kan fara wannan yunkuri da ci- gaba da shi har zuwa karshe.

Abin tambaya a nan shi ne mene ne sababin wannan naciya kuma don me dole sai ya yi fito-na-fito?

Hakika da ba don yunkurin Imam Husaini (a.s.) ba da irin surar da mahukuntan Umayyawa suka bayar na batanci, fasadi da zalunci ne zai zama hoton Musulunci a zukatan mutane har zuwa yau din nan.

Jinin Husaini (a.s.) shi ne ya kankarewa Musulunci wannan hoto ya kau da shi, ya kuma tona asirin irin barnar mahukuntan Umayyawa da irinsu ga tarihin dan' Adam baki daya, ya bar Musulunci bisa tsarkinsa da aka san shi da shi.

A matsayinsa na jikan Annabi Muhammadu (s.a.w.a), da ga Ali (a.s.) kuma abin wasicinsu, Imam Husaini (a.s.) ya kasance wani kyakkyawan shafi daga shafukan sakon Musulunci, kuma wata rayayyar fassara ta dukkanin bangarori da tunace-tunacensa (Musulunci); abin da ya sa ya zama farkon mai amsa kiran sakon na Musulunci a lokacinsa, don da haka ya tabbatar da lizimtarsa gare shi.

Haka kuwa al'amarin ya kasance, domin lizimtar sharia'ar Allah Madaukaki ce ta farlanta masa bin tafarkin arangama; ba wata hanya face wannan. Saboda ba tare da gabzawa ba da ba'a fatan samun wani gyara. Bayanin yunkurinsa na farko na bayyana wannan hakika da duk ma'anoninta, inda yake cewa:

"Ni ban fito domin girman kai ko alfahari ba, ba kuma domin barna a bayan kasa ko zalunci ba. Abin da kawai ya fito da ni shi ne neman gyara a cikin al'ummar kakana, Manzon Allah (s.a.w.a.). Ina nufin yin umurni da kyakkyawan aiki da hana mummuna, in kuma bi irin rayuwar kakana da babana Aliyu bn Abi Talib".

Wadannan su ne manyan hujjojin da suka ba Husaini (a.s.) da Sahabbansa hakkin sanar da gwagwarmayarsu da ke matsayin magani a duniyar dan'Adam, mai dawwamar da Musulunci, mai yin ilhama ga 'yan gwagwarmaya a tsawon tarihin, don jayuwa zuwa ga gaskiya da ka'dojin 'yan'Adamtaka masu girma, da jan daga don jihadi da ma'abuta dagawa da azzalumai.