A+ R A-
23 July 2019

Gudummawar Imam Husain (a.s) Wajen Dawwamar Musulunci

Mai bin tarihin rayuwar Husaini bin Ali (a.s.) zai zurfafa wajen riskar cewa gudunmawarsa a rayuwar Musulunci ta fara ne da wuri. Domin ya taka muhimmiyar rawa a yunkurin Musulunci mai bunkasa a lokacin da bai fita daga matakin yaranta ba, a lokacin rayuwar mahaifinsa kenan da kuma gefen dan'uwansa Imam Hasan (a.s.)

Tare da cewa bayan dan'uwansa Hasan ya koma ga Allah, aikinsa ya dauki wani sabon salo daidai da sababbin abubuwan da suka faru a tafiyar rayuwar al'umma; kuma saboda kasancewar kowane Imami aikinsa na iyakantuwa ne daidai da dabi'ar yanayin zamantakewa, tunani da siyasa.

Hakika Imam Husaini (a.s.) ya kalubalanci wani mummunan shiri na Umayyawa mai nufin cutar da rayuwar Musulmi, a wani mawuyacin lokaci da al'umma ke raye a ciki. Haka ya rayu tare da abubuwan da suka biyo bayan sa hannu a yarjejeniyar sulhu da ya gudana tsakanin Imam Hasan (a.s.) da Mu'awiya. Wannan tsarin adawa - na Umayyawa - ya mayar da hankali a kan wadannan abubuwa ne:

1-Yaduwar ta'addanci da kawar da duk wata kungiyar da ke hamayya da mulkin Umayyawa, musamman mabiya Ali (a.s.), da yi musu bi-ta-da-kulli da kashe su ta mafi munin hanya. Domin an ruwaito cewa Mu'awiya ya rubutawa wakilansa cewa:

"Duk wanda ku ka tuhuma da bin wadannan mutane (Alhlulbaiti) ku dankwafe shi kuma ku rushe gidansa(1)".

Imam al-Bakir (a.s.) ya siffanta wannan tashin hankali na zubar da jini cikin takaitacciyar magana, yayin da ya ce:

"Sai aka kashe Shi'armu a kowane gari. Aka yanke hannuwa da kafafu a bisa zato. Ya kasance duk wanda aka ji yana kaunar mu da zuwa wajen mu za a jefa shi a kurkuku ko a kwace dukiyarsa ko a rushe gidansa. Haka al'amarin ya ci gaba da tsananta da karuwa har lokacin Ubaidullahi bin Ziyad, wanda ya kashe Husaini(2)".

Yayin da yake magana kan irin zubar da jinin da ya gudana a lokacin Mu'awiyya, malamin tarihi, Ibn Athir ya ce:

"Lokacin da Ziyad (gwamnan Mu'awiya a Kufa) ya wakilta Samrata a Basra ya aikata mafi yawan kashe-kashe da aka yi a can. Ibn Sirin ya ce: 'Samrata ya kashe mutum dubu takwas a bayan idon Ibn Ziyad, sai Ibn Ziyad ya ce masa: Ba ka jin tsoron ko watakila ka kashe wanda bai ji ba bai gani ba? Sai ya ce: Da ace na kashe irinsu tare da su da ban ji tsoro ba'. Abul-Siwari al-Adawi ya ce: 'A dare daya Samrata ya kashe mutum arba'in da bakwai daga mutanen da dukkan su mahardata Alkur'ani ne'(3)".

2- Watsi da dukiya da nufin sayen lamirin mutane. A aikace sun iya sayen wasu masu wa'azozi da ruwayar hadisi, wadanda ke da hannu dumu-dumu wajen yi wa Mu'awiya aiki da kirkirar hadisan karya suna dangana su ga Manzon Allah (s.a.w.a) don cin zarafin Ali da mutanen gidansa (a.s.). Haka ya iya sayen masu fada a ji cikin mutane da shugabannin kabilu.

3- Kuntatawa ta fuskar tattalin arziki da yin amfani da hanyar yunwata mutane, musamman a garuruwan da ba su mika wilayarsu gare su ba da kuma sauran masu hamayya da su. Don cimma wannan buri wata rana Mu'awiya ya rubutawa gwamnoninsa cewa:

"Ku lura da duk wanda shaida ta tabbatar da cewa yana son Ali da mutan gidansa, ku share sunansa daga jerin sunaye, kuma ku janye ba shi abincin(4)".

Wannan ya zo a daidai lokacin da mahukunta ke wasa da dukiyar al'umma, suke bushasharsu da abin da suka wawure daga mutane. Malaman tarihi sun ambaci misalai masu yawa a kan haka, daga ciki akwai cewa:

Dukiyar Amr bin أs, gwamnan Masar a lokacin Mu'awiya, tsaba kawai sun kai dinari dubu dari uku da ashirin da biyar (325,000); kudaden takardu ma yana da dubbbai, kudaden da ke shigo masa daga kadarori kuwa sun kai dinari dubu dari biyu a Masar. Kimar kadarorinsa da ke Masar sun kai dirhami miliyan goma(5).

4- Rushe tushen ginin al'ummar Musulmi ta hanyar tayar da jin kabilanci da bangaranci, da rura wutar kabilanci a wajen larabawa a kan wadanda ba larabawa ba daga Musulmi.

5- Kashe Imam Hasan bin Ali (a.s.) duk da matsayin da ya ke da shi na halattaccen jagoran Musulmi a duniyar Musulunci.

6-Nadin da Mu'awiya ya yi wa dansa Yazidu a matsayin shugaban Musulmi a bayansa, alhali kuwa Yazidu sananne ne da fajirci, shan giya da caca. Ya nada shi ta hanyar danniya, kama-karya, kwadaitarwa da barazana.

Mika akalar mulki ga Yazidu don ya shugabanci al'ummar Musulmi da iyakance mata makomarta na nufin gamawa da Musulunci a aikace da yin ridda daga addinin Allah da komawa jahiliyya amma ta wani sabon salo.

Wannan Yazidun, kamar yadda tarihi ke tabbatarwa, lalacewa ta yi galaba a kansa, ta duk bangarorin tunaninsa da ayyukansa, wadanda ke nuna tarbiyyar jahiliyya mai rassan fasadi da fajirci, irin wadanda wannan da na Mu'awiya ke tafkawa a gaban idon Musulmi masu yawa a garin Sham; kamar wasannin banza, shan giya, bin 'yan mata da wake-wake. Ya kasance yana sanyawa karnukansa mundayen zinari, kuma ko yaushe yana tare da birai. Dangane da hakan, malamin tarihin nan, Balazuri na cewa:

"Yazidu na da wani biri da yake rike shi a hannunsa, ya sa masa suna Abu Kais. Yana shayar da shi giyar dabino ya yi ta yin dariyar bankaurar da ya ke yi. Ya kasance yana dora shi a kan alfadari ya tura shi tare da dawaki(6)".

Ibn Kathir ya ruwaito cewa:

"An ruwaito cewa Yazidu ya shahara da kade-kade, shan giya, wake-wake, farauta, 'yan kama, mawaka, karnuka da wasan karo tsakanin raguna da dabbobi da birai. Babu wata rana face ya wayi gari cikin maye. Ya kasance yana daura biri a kan doki bisa sirdi da igiya ana jansa (dokin). Yana sa wa birai hulunan zinari, haka ma 'yan kama. Ya kasance idan biri ya mutu sai ya yi bakin ciki. An ce ma sababin mutuwarsa shi ne cewa yana rike da wata biranya yana sa ta rawa sai ta cije shi(7)".

Idan wannan shi ne halin halifa, to yaya halin wasu zai kasance kuma? Masa'udi ya bayyana haka da cewa:

"Abin da Yazidu ya kasance yana aikatawa na fasikanci ya yi galaba a kan ma'aikatansa. A lokacinsa ne wake-wake suka bayyana a Makka da Madina, aka shiga aikata wasannin banza, mutane suka shiga bayyana shan giya(8).

Yayin da Mu'awiya ya kuduri aniyar ayyana wannan da nasa Yazidu, sabanin ka'idojin Musulunci da hukunce-hukuncensa; kudurin na sa ya sabawa ra'ayin gama-garin Musulmi, musamman kuma masu fada-a-ji a cikin al'umma. Haka al'umma ta sami kanta a wani sabon yanayi na tarihinta, ya zama ba ta da zabi sai dayan biyu:

(a)- Ko dai ta rungumi siyasar hamayya don tsige tushen barna da lalacewar da aka danfara mata; ko me hakan zai kallafa mata kuwa.

(b)- Ko kuwa ta mika kai bori ya hau dangane da halin da aka shiga, inda kenan dole ta yi sassauci da addininta, sakonta, girmanta da daukakarta a wannan rayuwa; sai ta karbi wulakanci, kaskanci, tabewa da tsiraici.
 ____________
1- Ibn Abil-Hadid, Sharhin Nahjul-Balagha, juzu'i na 11, shafi na 45.

2- Kamar na sama, shafi na 43.

3- Al-Kamil Fit Tarikh na Ibn Athir juzu'i na 3, shafi na 462.

4- Ibn Abil-Hadid, Sharhin Nahjul-Balagha, juzu'i na 11, shafi na 45.

5- Muruj al-Zahab na Al-Mas'udi, juzu'i na 3, shafi na 23.

6- Ansabul-Ashraf, na Balazuri juzu'i na 4, shafi na 1 da 2.

7- Al-Bidayatu wal-Nihayatu na Ibn Kathir, juzu'i na 8, shafi na 236.

8- Mas'udi, cikin Murujul-Zahabi, juzu'i na 3, shafi na 67.