A+ R A-
05 December 2021

Gudummawar Imam Hasan (a.s) Cikin Al’umma

Gudummawar Imam Hasan (a.s) Cikin Al’umma

Ayyuka da gudummawar Imam Hasan (a.s.) sun fara bayyana a duniyar musulmi da wuri. Mai bin yadda Imam Hasan (a.s) ya tafiyar da rayuwarsa zai riski cewa nauyin da suka hau kansa sun hadu ne a zangogi biyu cikakku, su ne kuwa kamar haka:

Na Farko: A lokacin Mahaifinsa (a.s):

Aikin Imam Hasan (a.s.) a wannan lokacin ya misaltu da cikakken biyayya ga mahaifinsa Imam Ali (a.s.) a matsayin shi (Imam Ali din) na abin koyi kuma Imam. Ya kasance yana mu’amala da shi ba kawai a matsayin da mai biyayya ba, har ma a matsayin soja mai bin oda.

Imam Hasan (a.s.) ya halarci dukkan yakoki tare da mahaifinsa Imam Ali (a.s.) a Basra, Naharwan da Siffin, ya kuma taka muhimmiyar rawa a cikinsu, inda ya shiga cikin wadannan yakoki, ya kashe wannan fitina ba bisa wata manufa ba face son Musulunci da tafarkinsa.

Littafan tarihi sun ruwaito cewa Imam Hasan (a.s.) ya kasance yana wakiltar Imam Ali (a.s.) a wurare da dama, ya kasance ko da yaushe cikin yunkurawa da kazar-kazar a karkashin hukumar (mahaifinsa), kamar yadda ya kasance yana gabatar da lakcoci ga mutane don bayyana ra’ayoyin Imam da kan gaskiyar matakan da ya dauka a duk lokacin da al’amura suka shige wa jama’a duhu.

Na Biyu: A Lokacin Imamancinsa (a.s):

Zango na biyu na aikin Imam Hasan (a.s.) a duniyar Musulunci ya fara ne daga lokacin da mahaifinsa ya mika masa akalar Imamanci, wato lokacin da Imam Ali (a.s.) ya yi masa wasici da cewa:

Ya kai dana, hakika Manzon Allah (s.a.w.a) ya hore ni da in yi wasici da kai kuma in ba ka littafaina da makamaina kamar yadda shi ya yi wasici da ni kuma ya ba ni littafansa da makamansa. Haka ya hore ni da in hore ka da cewa idan mutuwa ta zo maka ka bayar da su ga dan’uwanka Husaini”.

Sannan ya waiwaya ya dubi Husaini (a.s.) ya ce:

Manzon Allah (s.a.w.a) ya hore ka da ka bayar da su ga wannan dan naka (Imam Zainul Abidin) ”.

Sai ya kama hannun Imam Ali Zainul-Abidin (a.s.) ya ce:

Kai kuma Manzon Allah (s.a.w.a) ya hore ka da ka bayar da shi ga danka Muhammadu; ka isar da gaisuwa gare shi daga Manzon Allah da ni ([1])”.

Bayan Imam Ali (a.s.) ya koma ga Ubangijinsa, al’ummar garin Kufa sun nufi masallci cikin gigita da rudewa saboda zafin masifar da ta zo, sai Imam Hasan ya mike tsakanin wannan cincirindon mutane ya gabatar da bayani na farko bayan wafatin babban Jagora, Ali (a.s.), ya ce:

Hakika a wannan daren an karbi ran  mutumin da na farko ba su wuce shi ba, kuma na baya ba za su cim masa ba. Hakika ya kasance yana jihadi tare da Manzon Allah (SAW) don ya rika ba shi kariya da ransa. Manzon Allah ya kasance yana nufansa (wato yana ba shi) da tutarsa, sai Mala’ika Jibrilu ya rufa masa ta daman shi kuma Mika’ilu ta hagunsa, ba ya dawowa har sai Alah Ya yi budi a hannunsa. Hakika ya rasu a wannan daren da aka dauke Annabi Isa dan Maryam (a.s.) a irinsa, aka kuma karbi ran Yusha’u bin Nun –wasiyyin Musa (a.s.)-,  alhali (Imam Ali) bai bar zinari ko azurfa ba face dinari dari bakwai ([2])”.

Imam Hasan (a.s) na gama hudubarsa sai Ibn Abbas ya shiga kwadaitar da mutane a kan yi masa mubaya’a, hakan kuwa aka yi, sai aka yi wa Imam (a.s.) bai’a.

Da haka aka yi wa Imam Hasan (a.s.) mubaya’a a matsayin halifa kuma ja-gaban Muminai a Kufa da sauran garuruwa daga baya.  Sai labarin rasuwar Imam Imam Ali (a.s.) da ciratar halifanci zuwa dansa Hasan ya shiga yaduwa.

A garin Sham kuwa, da labarin wafatin Imam Ali (a.s.) ya isa kunen Mu’awiya sai ya cika fadarsa da bukukuwa, ya lullube helkwatarsa da farin ciki, sai dai al’amarin bai’ar Imam Hasan (a.s.) ya daga masa hankali, don haka sai ya kira taron gaggawa da masu ba shi shawara a dakin taronsu don tattaunawa a kan sabbin sauye-sauyen da suka faru da tsara wata siyasa da za a fuskanci Imam Hasan (a.s.) da ita. Sai taron ya kudurta watsa ‘yan leken asiri a cikin al’ummar Musulmi da ke karkashin jagorancin Imam Hasan (a.s.) don a jefa tsoro da yada karerayi dangane da gwamnatin Ahlulbaiti (a.s.); kamar yadda masu halartar taron suka kuduri cewa jam’iyyar Mu’awiya ta aiwatar da wani aiki mai fadi na jan hankulan masu fada-a-ji cikin gudunar da al’amuran Iraki, wannan kuwa ta hanyar bayar da rashawa, alkawurra masu ruda hankali, kyaututtuka, tsoratarwa, barazana da dai sauransu.

Sai dai cibiyoyin tsaron Imam Hasan (a.s.) masu karfi da kokarin gina gwamnati tabbatacciya, nan da nan suka gano wannan shiri na Umayyawa. Wannan ya sa aka rika samun musayar wasiku tsakanin Imam (a.s.) da Mu’awiya. Sai dai wannan bai samar da wani kyakkyawan sakamako ba, domin Mu’awiya ya ki mika wuya ga Imamin zamaninsa, ya dage a kan sabawa; wannan ne ya samar da kusantowar rikici, wanda ya fara daga bangaren Mu’awiya, yayin da ya aika sojojinsa Iraki.

Labarin yunkurin Umayyawa zuwa Iraki ya isa kunnen gwamnatin Musulunci, abin da ya sa Imam (a.s.) ya gaggauta yekuwar kariyar kai wajen kalubalantar abokan gaban da suka daura damara. Sai Imam ya watsa bayanin da a ciki ya kira al’umma da ta tara karfi da ikonta don yakin dakatar da azzalumai. Ya zo, a cikin bayanin, cewa:

Bayan haka, lallai Allah Ya farlanta jihadi a kan bayinSa, Ya kira haka da ‘abin ki’ (wato sai dole ake yin shi). Sannan ya cewa Muminai masu jihadi:Ku yi hakuri, lallai Allah na tare da masu hakuri. Ya ku mutane, hakika ba za za ku iya samun abin da ku ke so ba sai da hakuri a kan abin da ba ku so.. ku fita zuwa rundunarku a Nakhila (sunan wuri ne da ke kusa da Kufa a hanyar Sham) har mu gani kuma ku gani..([3])”.

Wani abin takaici shi ne cewa mafi yawan wadanda suka saurari bayanin Imam Hasan (a.s.) sun riga sun tasirantu da kage-kage da farfagandar Umayyawa, don haka maimakon su gaggauta kare gaskiya bayyananniya, sai suka shiga dimuwa da rudu, sai suka nokewa Imaminsu na gaskiya, ba su sami dacewar amsa kiransa na daura damarar yaki da sauke nauyin jihadi ba. Duk da haka, alamun sadaukar da kai da yarda da wannan al’amari sun bayyana daga wadansu, a daidai lokacin da dukiyar Umayyawa ta rufewa wasu ido.

Imam Hasan ya fuskanci yanke kauna yayin da hakikanin mutanen da yake shugabanta ta bayyana, wadanda ya kasance yana kallo a matsayin wani tushe da zai iya dogara da shi a lokacin runtsin hadurran da ke fuskantar sakon Musulunci daga makirce-makircen jam’iyyar Umayyawa ‘yan adawa, wadanda ke aiki tukuru don sauya hukumar Musulunci zuwa daular jahiliyya da tsagwaron son zuciya da ta’assubancin kabilanci ke shugabanta.

A irin wannan matsanancin yanayi mai sa yanke kauna ne wasu masu kyakkywan niyya a kan Musulunci da shugabancinsa na hakika a hannun Ahlulbaiti (a.s.) suka yi kira, yayin da suka bayyana kyakkyawar niyyarsu ba ta san ja da baya ba, suka nuna kyamarsu ga wancan gungu na wulakantattu, suka dauki matsayi da dukkan karfi da dagewa; sai suka yi tattaki cikin gaggawa suka hada runduna a Nakhila, kamar yadda Imaminsu (a.s.) ya yi horo. Hakika kuma Imam ya biyo bayan wadancan masu kyakkyawan niyya da sojin da wasu ruwayoyi suka ce adadin su ya kai mayaka dubu hudu, a kan cewa sauran mutane za su same shi.

Imam Hasan (a.s.) ya kasance yana fatan mutane za su dawo wajen taimakon gaskiya da amincewa da kare Musulunci; sai dai nokewarsu ta sa dole Imam ya sake dawowa helkwatarsa a Kufa don kwadaitar da mutane a kan tafiya tare da shi.

A karshe dai haka waccan runduna mai yawa, amma mai raunin zuciya, ta tafi cikin rauni a warwatse, har suka isa Nakhila. Sai Imam ya shirya sojoji, ya gabatar da tsare-tsare ga kwamandojin kananan bataliyoyi. Daga nan sai ya tafi yankin Dair Abdul-Rahman, inda ya shirya aikawa da bataliyar farko a matsayin mai share fagen shi zuwa Sham, ya kuma zabawa wannan bataliya dan baffansa Ubaidullahi bin Abbas a matsayin kwamandanta. Wannan bataliya ta yi sansani a wani wuri da ake kira Makin da ke gabar ruwan tekun al-Dajila da ke Iraki. A lokacin da Imam (a.s.) ya taso sai ya yi sansani a wani waje da ake kira Muzlim Sabat da ke kusa da Mada’in.

Ba a dauki wani lokaci mai tsawo ba sai duk illolin da ke addabar dakarun Imam Hasan (a.s.) suka bayyana a fili, ta yadda hakan ya kacancana rundunar ya raunana ta, fitinu da rikice-rikice suka yadu tsakanin kwamandojin kansu. Wannan ne ya tilastawa Imam Hussan rattaba hannu a yarjejeniyar sulhu cikin wani mawuyacin yanayi.

 


([1]). Duba Hayat Imam al-Hasan na Bakir Sharif al-Karashi; da Sheikh al-Dabrisi, cikin A’alam al-Wara, shafi na 206 a babin dake magana a kan nassosin dake tabbatar da Imamancin Hasan (a.s.) kamar yadda ya fitar daga  Kashf al-Gummah fi Ma’arifatul-A’immah, juzu’i na 2, shafi na 155.

([2]). Sheikh al-Dabrisi, cikin A’alam al-Wara, shafi na 208; da Hayat Imam al-Hasan na Bakir Sharif al-Karashi, juzu’i na 2, shafi na 31, kamar yadda aka fitar daga littafi al-Futuh da dan bambanci lafazi kadan.

([3]). Ibn Abil-Hadid, cikin sharhin Nahajul-Balagha, juzu’i na 16, shafi na 38.