A+ R A-
05 December 2021

Halayen Imam Hasan al-Mujtaba (a.s)

Halayen Imam Hasan al-Mujtaba (a.s)

Asalin tanajin da aka tanada don Imam Hasan (a.s.) ya tabbatarwa samuwarsa ta ruhi wata kololuwar daukaka. Kusancinsa ga Allah da ta’allakursa da Shi wani al’amari ne da ke girgiza zuciya kuma hankali ke mika wuya a kai. Imam al-Sadik (a.s.) yana cewa:

Imam Hasan bin Ali ya kasance mafi bautan mutanen zamaninsa, kuma ya fi su gudun duniya da daraja”.

Haka nan ya zo cikin littafin Raudhatul-Wa’izina cewa: “(Imam Hasan) Ya kasance idan yana alwala sai jikinsa ya rika kakkarwa kuma launinsa ya canza, da aka tambaye shi dalilin haka sai ya ce:

Hakki ne aka duk wanda ya tsaya a gaban Ubangijin Al’arshi launinsa ya canza kuma gababunsa su kada”.

Ya kasance idan ya isa kofar Masallaci ya kan daga kansa ya ce:

“Ya Allah! BakonKa ke kofarKa. Ya Mai yawan kyautatawa hakika, mai munanawa ya zo maKa, to Ka ketare munanan abubuwan da ke gare ni da kyawawan abubuwan da ke gare Ka, Ya Ma’abucin karimci”.

Ya kasance idan yana karanta Alkur’ani, duk lokaci da ya zo ayar da da ke cewa: (Ya ku wadanda suka ba da gaskiya) yakan ce: “AmsawarKa! AmsawarKa!! Amsa-warKa!!!

An ruwaito daga Imam al-Sadik (a.s.) cewa:

Imam Hasan bin Ali (a.s.) ya tafi hajji har sau 25 da kafa. Ya kuma raba dukiyarsa biyu ya ba Allah rabi ([1])”.

Kyawawan dabi’unsa kuwa wani abu ne mai misalta dabi’un Alhlulbaiti (a.s.). Littafan tarihi sun hakaito cewa: “Imam Hasan ya taba bi ta wajen wasu mutane matalauta, a lokacin suna tsintar guntattakin gurasa da aka ci aka rage kuma aka watsar a hanya, suna ci. Da suka gan shi sai suka yi masa tayin ya zauna ya ci tare da su. Sai kuwa ya amsa musu da cewa: ‘Hakika Allah ba Ya son masu girman kai.’ bayan da ya gama da su sai ya gayyace si bakuntarsa, sai ya yalwata su da dukiya mai yawa, ya kuma ciyar da tufatar da su”.

Wata rana an taba ce masa: “Me ya sa ba mu taba ganin ka ki amsawa mabukacin da ya tambaye ka ba?” sai ya amsa da cewa:

Hakika ni ma mai rokon Allah ne, kuma mai kwadayi gare Shi; don haka ina kunyar in zama mai roko alhali kuma ina hana mai roko. Kuma Shi (Allah) Ya sabar da ni da bayar da ni’imarSa gare ni, haka ni ma na sabar da Shi in bayar da ni’marSa (da Ya ba ni) ga mutane; to ina tsoron in na yanke al’adata Shi ma Ya yanke al’adarSa”.

Haka nan Imam Hasan (a.s.) ya taba sayen wani lambu daga wasu mutane Ansarawa da kudi dirhami dari hudu, sai labari ya zo masa cewa (wadanda suka sayar masa din) sun koma suna bukata daga mutane, sai ya koma musu da lambun ba tare da ya karbi kudinsa ba.

Wannan kadan ne daga daga siffofinsa (a.s.), kuma wani bangare ne na matsayinsa tare da daidaikun wannan al’umma. Dabi’unsa sun kasance mafi tasiri wajen misalta kyawawan dabi’un Musulunci([2]).

 

 


([1]). Don karin bayani ana iya duba littafin Kashaful-Gummah, juzu’i na 2; da Manakibu Ãli Abi Dalib, juzu’i na 3; da al-majalis al-Siniyyah, da Ahlul-bait na Taufik Abu Ilm; da Tazkiratul-Khawas da wasunsu.

([2]). Don karin bayani ana iya duba littafin Ahlul-bait na Taufik Abu Ilm; da wasunsa na daga littafan Sirah.