A+ R A-
05 December 2021

Imam Hasan (a.s) Cikin Alkur’ani Da Sunna

Imam Hasan (a.s) Cikin Alkur’ani Da Sunna

Kamar sauran Ahlulbaiti (a.s.), Hasan (a.s.) na da babban matsayi a cikin Littafin Allah Madaukaki da Sunnar ManzonSa mai girma (s.a.w.a). Za mu wadata da yin ishara da wasu nassosi da suka zo daga Manzo (s.a.w.a) dangane da Hasan (a.s.) da daukakar matsayinsa.

A cikin Alkur’ani mai girma, wanda shi ne kundin tsarin al’umma kuma dawwamammen mu’ujizar Musulunci, akwai bayyanannun ayoyi da ke magana game da matsayin Ahlulbaiti (a.s.) a wajen Allah Madaukaki, daga cikinsu kuwa har da Imam Hasan (a.s.). Daga cikin wadannan nassosi akwai Ayar Tsarkakewa, wadda Allah Madaukakin Sarki ke cewa:

“Lallai Allah Na nufin kawai Ya kawar da kazanta ne daga gare ku Ahlulbaiti, Ya kuma tsarkake ku tsarkakewa”.

Bayanai sun zo dangane da dalilin saukar wannan aya cewa Manzon Allah (s.a.w.a) ya sa da a kawo masa wani mayafi sakar Khaibara, sai ya lullube Ali, Fatima, Hasan da Husaini da shi, sannan ya ce:

Ya Allah! Wadannan ne kebabbun gidana (Ahlul-baiti),to Ka kawar da kazanta daga gare su Ka kuma tsarkake su tsarkakewa ([1])”.

Sai ayar tsarkakewa ta sauka tana amsa addu’ar Manzo (s.a.w.a). Wannan aya dai na dauke da shedar Allah Madaukaki kan tsarkin Ahlulbaiti (a.s.) da kare su daga zunubai (Isma), haka tana bayyana girman matsa-yinsu. Akwai wadansu ayoyi, kamar Ayar Mubahala (Surar Ma’ida, 5:61) da Ayar Kauna (Surar Shura, 42:23) da wasunsu.

Ta bangaren hadisan Annabi (s.a.w.a) ma za mu ambaci wasu kamar haka:

1- Bukhari da Muslim sun ruwaito daga Barra’u ya ce: Na ji Manzon Allah (s.a.w.a), a lokacin yana dauke da Hasan dan Ali a kafadarsa, yana cewa: “Ya Allah, lallai ni ina son mai sonsa”.

2- Tirmizi ya ruwaito daga Ibn Abbas ya ce: Manzon Allah (s.a.w.a) ya kasance yana dauke da Hasan dan Ali (a.s.), sai wani mutum ya ce: ‘Ka hau mafi alherin abin hawa yaro’, Sai Manzo (s.a.w.a) ya ce: “Kuma shi mafi alherin mai hawa ba”.

3- An ruwaito daga Anas bin Malik ya ce: An tambayi Manzo (s.a.w.a) da cewa: ‘Wa ka fi so daga mutan gidanka?’ Sai ya ce: “Hasan da Husaini”.

4- An ruwaito daga A’isha ta ce: Manzon Allah (s.a.w.a) ya kasance yana daukar Hasan ya rungume shi yana cewa: “Ya Allah wannan dana ne kuma ina sonsa don haka ina son wanda ke sonsa”.

5- An ruwaito daga Jabir bin Abdullahi, ya ce: Manzon Allah (s.a.w.a) ya fadi cewa: “Duk wanda ke son ya ga shugaban samarin gidan Aljanna sai ya kalli Hasan bin Ali”.

6- Abu Hamid al-Gazzali ya fitar, a cikin Ihya’u ulumul-din, daga Manzo (s.a.w.a) yana ce wa Hasan (a.s.): “Ka yi kama da ni a halitta da halayya”.

7- Manzo (s.a.w.a) ya ce: “Hasan da Husaini Imamai ne sun yunkura (sun nemi hakkinsu) ko sun zauna”.

 

 


([1]). Muslim, Tirmizi, Nasa,i da wasunsu duk sun fitar da wannan hadisi.