A+ R A-
22 February 2024

Dabi'un Imam Muhammad al-Baqir (a.s)

1-    Imam al-Sadik (a.s) yana cewa: “Babana (Imam Bakir) ya kasance mai yawan zikiri, ya kasance mai ambaton Allah a lokacin da muke tafiya, haka nan idan muna cin abinci ya kasance mai ambaton Allah, haka kuma tattaunawa da mutane ba ta hana shi ambaton Allah. Na kasance ina ganin harshensa na haduwa da saman bakinsa yana mai fadin La’ilaha illallah, ya kan tara mu ya umarce mu da ambaton Allah har rana ta fito, ya kan umarce wadanda suka iya karatu daga cikinmu da su ta karatu, wadanda kuma ba su iya ba da su ta yin zikiri([i])”.

2-    Haka nan kuma Imam Sadik (a.s) na cewa: Wata rana na je wajen babana a lokacin kuwa yana ba da sadakan dinare dubu takwas ga mabukatan garin Madina, kana kuma ya ‘yantar da wasu bayi da suka kai kimanin goma sha daya([ii])”.

3-    Hasan bn Kathir yana cewa: Wata rana na isar da kuka ta ta wata bukata da kuma jafa’in ‘yan’uwa ga Abu Ja’afar Muhammadu bn Ali (a.s) sai ya ce min: Mummunan dan’uwa, dan’uwan da yake kasancewa tare da kai a lokacin wadata kana kuma ya kaurace maka lokacin rashi”. Daga nan sai ya umarci wani bawansa da ya zo da wata jaka da ke dauke da dirhami 700 ya ce: Ka ciyar da wannan, idan ya kare ka sanar da ni([iii])”.

4-    Sulaiman bn Karm ya ce: ‘Abu Ja’afar Muhammadu bn Ali ya kasance ya kan saka mana da dirhami 500 zuwa 600 zuwa 1000, kuma ba ya nuna goyon baya ga ‘yan’uwansa ko na kusa da shi (akan saura)([iv])’.

Imam Bakir (a.s) dai ya kasance yana daukan wadannan nauyi ne ba wai don yana da kudin da ya tara ba ne, face dai shi ya kasance ne kamar yadda dansa Imam Sadik (a.s) ya siffanta shi da cewa: Babana ya kasance mafi karancin kudi daga Ahlulbaitinsa, amma kuma wanda ya fi su nauyi mai yawa([v])”.

 


([i]). Kamar na sama.

([ii]). Kamar na sama.

([iii]). Al-Irshad na Sheikh al-Mufid, falalar Imam Bakir (a.s).

([iv]). Bihar al-Anwar na Majlisi, juzu’i na 46.

([v]). A’ayan al-Shi’a na Muhsin Amin, juzu’i na 4, shafi na 12.