A+ R A-
22 February 2024

Haihuwar Imam Muhammad bn Ali Al-Baqir (a.s)

A cikin watan Rajab shekara ta 57 bayan hijiran Ma’aiki (s.a.w.a) ne gidan sakon Musulunci ya cika da farin ciki mai girman gaske saboda haihuwar Muhammadu bn Ali bn Husain al-Bakir (a.s), wato Imami na 5 daga cikin Imaman gidan Manzon Allah (s.a.w.a).

Imam Bakir (a.s) dai ya rayu sama da shekaru uku tare da kakansa Imam Husaini (a.s), don haka ya ga waki’ar nan ta Karbala mai tada hankali. Bayan nan kuma ya ci gaba da rayuwa karkashin kulawar mahaifinsa Imam al-Sajjad (a.s) duk tsawon lokacin imamancinsa har lokacin da ya yi shahada, a yayin wannan lokaci dai Imam Bakir (a.s) ya sami ilmummuka na Musulunci da kuma gadon Annabawa (a.s) daga mahaifinsa (a.s).

Wannan yanayi dai ya sanya Imam Bakir (a.s) ya kai wani matsayin na ilmi, daukaka, tunani, kwawawan halaye da dai sauransu da za su ba shi damar jagorantar al’umma gaba daya bayan mahaifinsa.

An ruwaoito al-Zubair bn Muslim al-Makki yana cewa: “Wata rana mun kasance a wajen Jabir bn Abdullah al-Ansari, daya daga cikin sahabban Ma’aiki, sai ga Aliyu bn Husain ya iso tare da dansa Muhammadu al-Bakir, a lokacin yana dan karami, sai Aliyu ya ce wa dansa Muhammadu: ‘Sumbanci kan baffanka’.

Sai Muhammadu ya je ya sumbanci kan Jabir.

Sai Jabir, wanda a lokacin ya makance, ya tambaya cewa: ‘Wane ne wannan?’.

Sai Imam Ali bn Husain ya ce: “Ai dana ne Muhammad”.

Nan take sai Jabir ya rungume shi ya ce: ‘Ya Muhammad! Kakanka Manzon Allah (s.a.w.a) yana gaisheka”.

Sai suka ce: ‘A’a ta ya ya Ya Aba Abdallah?’.

Sai ya ce: “Wata rana na kasance a wajen Manzon Allah (s.a.w.a) a lokacin kuwa Husaini yana zaune a kusa da shi yana wasa da shi, sai ya ce min: ‘Ya Jabir! Za a haifa wa dana Husaini da da za a kira da sunan Ali, a ranar tashin kiyama za a yi kira cewa shugaban masu ibada ya tashi, a lokacin Aliyu bn Husain zai mike. Shi ma Aliyu za a haifa masa da mai suna Muhammad. Ya Jabir! Idan ka hadu da shi ka isar da gaisuwata gare shi, ka sani cewar idan har ka ganshi to sauran kwanakin da suka rage maka ba su da yawa”.

Haka kuwa ya faru, don bayan kwanaki uku da wannan ganawa ne Jabir ya rasu([i]).

Saboda irin dimbin ilmin da yake da shi ne ya sa ake masa lakabi da al-Bakir, wato wanda ya kekketa ilmi, wanda yake bayyana dukkan abubuwan da suka shiga wa al’umma duhu da kuma bayyanar da sirrorin da suke cikin ilmi.

 


([i]). Al-Irshad na Mufid da al-Fusul al-Muhimma na Ibn Sabbag al-Maliki.