Dabi’un Imam Sajjad, Zainul Abidin (a.s)
- Details
- Published Date
- Written by Muhd Awwal Bauchi
- Category: Imam Sajjad Zainul Abidin (a.s)
- Hits: 2078
Dabi’un Imam Zainul Abidin (a.s)
Hakika masana da manyan mutane daga cikin al’ummar musulmi sun kasance suna bayani da fadin irin girma da daukakar da Imam (a.s) yake da ita saboda irin matsayin da ya ke da shi na daukaka, ilmi da takawa. An ruwaito al-Zuhri yana cewa: “Ban riski wani daga cikin mutanen wannan gida da ya fi Aliyu bn Husaini daukaka ba([i])”.
An ruwaito daga Sa’id bn al-Musayyab, yayin da ya ke amsa tambayar da wani saurayi Bakuraishe ya yi masa kan Imam (a.s), yana ce masa: “Wannan shi ne shugaban masu bautan Allah Aliyu bn Husain bn Ali bn Abi Talib([ii])”.
Ibn Hajar cikin littafin Sawa’ik al-Muhrika yana cewa: “Zainul Abidin shi ne wanda ya gaji mahaifinsa wajen ilmi, gudun duniya da kuma ibada([iii])”.
Imam Malik yana cewa; “An sanya masa suna Zainul Abidin ne saboda yawan ibadansa([iv])”.
A halin yanzu bari mu dan yi bayani kan bangaren yanayi da dabi’un Imam Zainul Abidin a takaice:
1- Imam Muhammadu Bakir (a.s) yana cewa: “Ba a taba ambaton wata ni’ima ta Ubangiji ba face sai ya yi sujada, haka kuma ba a taba karanto wata aya daga cikin Littafin Allah ba da take da ayar sujada a cikinta, face sai ya yi sujaba, haka nan kuma bai taba idar da wata salla ta farilla ba face sai ya yi sujada, haka nan bai taba sasanta wata husuma tsakanin mutane biyu ba face sai ya yi sujada. Ya kasance ana ganin alama ta sujada a dukkan gabobinsa na sujada, don haka ne ma ake kiransa da al-Sajjad (mai yawan sujada)([v])”.
2- Har ila yau kuma an ruwaito Imam Bakir (a.s) din yana cewa: “Tsayuwar Aliyu bn Husain (a.s) a yayin salla ta kasance tsayuwa ce ta kaskantaccen bawa a gaban Madaukakin Sarki, gabobinsa sun kasance sukan yi karkarwa saboda tsoron Allah Madaukakin Sarki. A lokacin da yake salla yana yinta ne kamar sallar ban kwana tamkar ba zai sake yin wata salla ba bayanta”.
3- Ibn Ishak yana cewa: Akwai wasu iyalai a garin Madina da suke samun dukkan abubuwan da suke bukata a ko da yaushe sai dai ba su san daga ina wadannan abubuwa suke zuwa musu ba, to amma lokacin da Aliyu bn Husaini ya rasu sai suka rasa wadannan abubuwa([vi]).
4- Abu Ja’afar (a.s) yana cewa: “(Aliyu bn Husaini) Ya kasance ya kan fita cikin dare yana dauke da wani buhu a bayansa (cike da abubuwan bukatun yau da kullum) ya kan je gidajen mabukata ya buga kofa idan mai gidan ya fito sai ya ba shi abin da ya ke so alhali kuwa fuskarsa na rufe don kada mutumin ya gane shi([vii])”.
5- Wata rana wani mutum ya kasance ya zagi Ali (a.s), sa yayi shiru bai ce masa komai ba, sai mutumin ya ce masa: Da kai fa nake yi, sai Imam (a.s) yace masa: “Ni kuma a gare ka nake rufe ido (kan abin da ka aikata min).
Wata rana ya riski wasu mutane suna zaginsa, sai ya tsaya a gabansu ya ce musu: “Idan har kuna da gaskiya kan abin da kuke fadi, to Allah Ya gafarta min, idan kuwa har karya kuke fadi, to Allah Ya gafarta muku”.
([i]). Al-Irshad na Mufid, shafi na 240.
([ii]). Kamar na sama.
([iii]). Ahlulbaiti na Tawfik Abu Ilm (Awlad al-Imam al-Husain).
([iv]). Tazkirat al-Khawas na Ibn al-Jawzi.
([v]). Al-Majalis al-Siniyya na Muhsin al-Amin, juzu’i na 2.
([vi]). Al-Irshad na Mufid, shafi na 242.
([vii]). Manakib Aali Abi Talib na Ibn Shahriashub, juzu’i na 3.