A+ R A-
22 February 2024

Rusa Kusheyin Malaman Tambutu: Barna Ga Tahirin Ci Gaban Bakaken Fata

Daga

 Mujtaba Adam

   This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.

  1. Kotun Binciken Akida (Inquisition Court):

Babu yasasshen zance maras ma’ana kamar baiwa lalata wuraren tarihin birnin Tambutu fuskar akida, da daukar cewa  rusa  kabarukan malaman da su ka yi daruruwan shekaru a kwance, wata gwagwarmaya ce ta masu jihadi da su ke son tsarkake musulunci daga shirka, alhali birni ne wanda   “Ba’a taba gurbata shi da bautar gumaka ba, ba a kuma taba yi wa wanin Allah sujjada akan doron  kasarsa ba.”  Kamar yadda daya daga marubutan tarihinsa na farko-farko Abdurrahman Bin Abdullah Assa’adi ya rubuta a cikin littafinsa mai suna: “Tarikh Sudan” a shekarar miladiyya ta 1655.  Gabanin wannan zancen kuwa ya fara da cewa: “Timbuktu, Matsayinta a kasashen bakaken fata daidai ya ke da fuska a jikin mutum”

Wannan tasirin mai karfi na  Tambutu akan kasashen yammacin Afrika da babu yadda za a yi wani manazarci ya  kau da kai daga gare shi ne ya sa Dr. Ibrahim  Sulaiman, ya fara  bijiro da  shi a farkon littafinsa na tarihin jihadin Shehu Usman Dan Fodio “ The Revolution In History”  Ya kuma ware masa babi  mai zaman kansa  da ya kira: “Tsarin Timbuktu” da ya tabbatar yadda tsarin ilimi  da tarbiyyar tsarkake zuciya na malaman Tambutu su ka yi  tasiri akan gwagwarmayar  Shehu Usman Dan Fodiyo, tare da yin furuci da wannan hakikar ta ‘Tsarkin Tauhidi” na  mazauna Tambutu  ta hanyar nakalto Dr.John Hunwick   da ya ke cewa “ Mazaunansa  su na  yin alfahari da cewa ba a taba bautawa gumaka  a cikin ganuwarsa ba

Binne matattau a masallatai kuwa,  sunna ce wacce ta rika tafiya tun daga lokacin da aka dora harsashin ginin wannan birnin -Wanda ba a taba yi wa wanin Allah sujjada akan doron kasar ba- kamar yadda ya zo a cikin babi na goma sha daya na littaafin Assa’adi da  ambaton sunansa ya rigaya.

“Amma babban masallaci, sarkin malli Alhaji Musa shi ne ya gina shi da hasumiyoyinsa guda biyar a jere cikin sahu, kuma da akwai kabarurruka a damfare da shi daga waje, ta hannun hagu da kuma yamma. Wannan kuwa sunna ce ta mutanen Sudan da  kuma mutanen Magrib cewa ba su binne matattunsu sai a jikin masallatansu daga waje”

Masallacin “Djingarey Ber” shi ne wanda Assa’adi ya ke nufi da “Babban masallaci”. Gininsa na kasa ne, kuma bagirensa  shi ne yammacin tsohon birnin Tambutu. Sarkin Daular Mali Mansa Musa ( 1280 -1337)  shi ne ya baiwa kwararren injiniya kuma mawakin nan dan asalin Andulus, Abu Ishak Assahili kwangilar gininsa akan kudi zinari  mai nauyin kilo 200.  ( mithqal 40 a ma’aunin larabawa) ko kuma mithqal 120 kamar yadda Ibn Khaldun ya ambata a cikin Labarin tafiye-tafiyensa na uku.  An kuma kammala gininsa a tsakanin  shekarun 1326/7 , abinda ya maida shi zama mai shekaru  679/700  a cikin wannan shekara ta 2012 da aka rushe shi.

Ba kuma salloli biyar kadai ake yi a cikin wannan masallaci ba, yana a matsayin tsangaya ce ta ilimi ( Jami’a) da dubban malamai da dalibai su ke karatu a cikinsa.  ( kamar yadda za mu gani anan gaba yayin magana akan  sauran masallatai biyu na sankore da Sidi Yahya masu tarihi  da kuma yadda manhajar karatu ta ke  a cikinsu.).

Idan mazauna Tambutu-zuriya bayan zuriya- suna ganin daraja da kima ta malaman da kabarukansu su ke kwance a masallai da kusuruwowin birninsu, ba saboda saukin kai ko jahilci ba ne.! Kuma tabbas, ba romansiyyar sufanci wacce ta ke tafiyar da alakar muridi da shehu ba ce kadai ta ke sa ‘yan baya girmama wadannan malaman da ci gaba da kare wauraren tarihinsu bayan gushewar zamani mai tsawo.

Na’am, hakika ce rubutacciya akan goshin tarihi cewa wadannan malaman sufaye ne. Da kuma za a tambayi  Aliyu Namangi ya siffata  ko su wanene malaman Sufaye da  an sami jawabi a cikin  Littafi Na Biyar Na Infirajinsa da cewa:

“Malaman Sufi takiyyai”

“Masu albarkar waliyyai” !

 Mutum zai iya yin tarayya da marigyi Namangi akan wannan  siffar da ya baiwa Malaman Sufaye ta cewa su; “Masu albarkar waliyai ne, ko kuma ya yi watsi da ita bisa gamsuwarsa ta akida, amma ba zai iya goge shaidar da aka rubuta akan allon dutsen tarihi ba cewa; wannan ajin na mutane, su ne manzannin da  su ka keto sahara  akan dawakai da rakuma zuwa  nahiyar arewa dauke da sakon musulunci. Sun kuwa shigo  kasar Hausa ne kodai  daga Daular Sanghai da su ne wangarawa da mallawa, ko kuma daga yankin Magrib, da ya hada kasashen arewacin Afirka da su ne sharifai. Farfesa Abdallah Uba Adamu ya yi jawabi dalla-dalla akan zuwan wadannan  nau’in na malaman cikin kasar Hausa a littafinsa mai taken: Kano Kwaryar Kira Matattarar Alheri. ( wanda ake bugawa a jaridar Aminiya mako-mako)

Ba kuma tallar sufanci wannan  kasidar ta ke yi ba, illa iyaka tana kokarin  bayyana abinda  ya ke shi ne hakika dangane da wannan ajin na malamai wadanda ta hannunsu ne musulunci ya iso gare mu. Sune asali da kuma tushe duk da cewa a yanzu  mafi yawancin musulmi  sun zama daidai da baitocin waken Shakepears a cikin wasan kwaikwayon Othello da ke cewa:

“ Kalankuwar maciya naman mutum’

Wadanda su ke cin naman junansu”

Irin (al’ummar) anthropophagi,”

“Da  girman  kawukansu bai kere kafadunsu.”

                                                                      Othello, Act 1. Scene III

Sufanci ba tuhuma bace  balle mai riko da tafarkinsa ya bukaci tsayuwa a gaban alkalin kotun binciken akida  (Inquisition Court) irin wacce ikilisiyar Spain ta kafawa musulimi da yahudawa da duk wanda ba dan darikar Roman Katolika ba a  Valencia da Granada da Cordoba da Seville a cikin karni na goma sha biyar. Idan alkali ya yanke hukuncin kafirci akan mutane, sai a jefa su da rai cikin wuta mai kuna  ( auto-da-fe) suna  ci suna  konewa, muminai kuma na tsaye na kallonsu suna tafi da shewa cikin annashawa.!

A shekarar 1591 daular  moroko ta mamaye birnin Tambutu ta kuma kashe malaman addini da dama. Daular moroko ta yi haka ne saboda da dalilai na siyasa da tattalin arziki ba addini ko akida ba.!  Kuma ba a sami wani malamin fada guda ba da ya halartawa gwamnati abinda ta yi ba ko kuma ya goyi baya. !

Yanzu ne bayan gushewar fiye da karni shida aka yi amfani da nassin addini wajen hukunta malaman addini bayan mutuwarsu.!   Da rusa  wuraren tahirin  da su ka gina bisa tsarkin zuciya da kyakkyawar manufa da aka gani a aikace.!  

 Idan ta hanyar fassara nassin addini za a rushe wuraren tarihi to abu ne mai  yiyuwa  a rusa  wannan irin daskararren tunanin ta hanyar nassin da fake da shi.  kamar yadda Cardinal Richelieu ( 1585 -1642) ya ke fadi ne cewa: “Ka bani sakin layi shida na rubutun  mutanen da su ka fi zama dattijai a duniya, zan iya samo gamsassun dalilai a ciki da zan rataye su da shi.” 

Hakika ce tabbatacciya, cewa rubuce-rubucen musulunci da masana da manazarta a duniya su ke karantawa su jinjinawa musulunci cewa ya taka rawa wajen samar da cigaba (civilization)   sun kushi ayyukan wannan ajin na malaman sufaye  ba masu adawa da su ba. A banza, masana irin su Bettrand Russell ( wanda bai yi imani da samuwar ubangiji ba balle  kuma addini) ba zai rusuna agaban musulunci ba, ya yi furuci a cikin littafinsa  mai taken “The History Of western Phillosophy” da gudunmawar da musulmi su ka bayar a fagen cigaban dokoki    ( fiqhu) da falsafa da sauran ilimomi.

Saboda haka, duk yadda za a  kafa kotun binciken akida   akan wannan ajin na mutane,  ba za  a iya  goge rubutacciyar  shaidar tarihin Kasar Hausa da ta ke cewa; wadanda su ka jaddada addinin musulunci a cikinsa bisa jagorancin Shehu Usmanu, a matakin farko su kansu sufaye ne: Da kuma za mu buda littafin shehu mai taken: al-Tafiqatu Baina Ilm al-Tasawwuf,  da mun ga yadda ya yi Magana akan sufanci da cewa:         “ Na tara maganganu akan sufanci da sun kai dubu, kuma dukkaninsu suna nufin fuskantar Allah da abinda  ya ke  yarda da shi cikin gaskiya. Kuma ka sani manufar sufanci da kuma amfaninsa shi ne zuciya ta kadaita da Allah madaukakin sarki”

 Kuma  ta hanyar duba littatafan  jagororin Jihadi a kasar Hausa,  za a iya ganin tasirantuwar da su ka yi daga manhajar karatun Tambutu da kuma malamanta.  Domin  malaman wannan birnin a lokacin da ya ke kan ganiyarsa sun kasance ma’abota halaye da dabi’un da su ka maida su zama wanzazzu ( Immortal) , abin koyi ga bil’adama. Marubucin littafin “Assa’Adatul-Abadiyyah Fit- Ta’arif Bi Ualama’i Tinbuktul Bahiyyah” ya siffata  malaman Tambutu  da ya riska da cewa:   “ Na sami salihan sankore , wadanda babu mai shiga gabansu a kyawun hali da ilimi, sai sahabban manzon Allah tsira da amincin Allah a gare shi.”

Akan wadannan halayen na tsayuwa akan gaskiya da kare ta ne a  wannan bangaren  na kasida zai maida hankali.

Ahmad Baba (1556- 1627)  wanda ake yi wa  lakabi da  Abul-Abbas al-Timbukti al-Tukruri, daya ne daga cikin dubban almajiran da Tsangayar  Sankore ta yaye su. Shi ne wanda  Dr. Ibrahim Sulaiman  ya  ce: Shehu Usman Dan Fodio ya kalle shi a matsayin cikakken hoto na yadda ya kamata ace  malamin addin   ya kasace a tsakanin al’umma.  A matakin farko  ya yi karatun ilimin addini har ya kai magaryar tukewa a cikin dukkanin  fannoninsa, sannan ya zama mai shiryar da al’umma a cikin bangarori mabanbanta, ya kuma zama mai yi wa dukkanin mutane hidima. Abin koyi na gaba daga Ahmad Baba wanda shehu Usman ya gani, shi ne  yin tsayin daka wajen kare manufofin al’umma da hana cin zarafin abubuwa masu kima na al’umma ( social Values) da akidunta da kuma cibiyoyoyinta. Ta haka ne, malamin addini ya ke zama  garkuwa na halayen kwarai da al’umma ta ke da su, da kuma tsarkinta da kuma mutunta cin gashin kai nata. Kuma shehu ya kalli Ahamd Baba a matsayin mai kare hakkin talakawa da wadanda ake zalunta  da kuma taimaka musu su cimma manufofinsu. Nauyi na hudu da ya hau kan malami wanda Ahmad Baba ya ke a matsayin hotonsa shi ne kare al’ummarsa da ganin cewa ta ci gaba da yin biyayya ga Allah da aiki da dokokinsa. Mataki na karshe wanda shi ma Shehu ya gani a matsayin abin koyi daga wannan malamin shi ne yi wa almajirai maza da mata tarbiyya wadanda za su ci gaba da shiryar da al’umma idan alamomin badala da lalacewa  sun fara bayyana acikinta.

Idan ana yi wa birnin katsina kirari da sunan daya daya daga cikin fitattun malaman da ta samar da  cewa: “Tudu Garin Dan Marina” to Dr. Ibrahim sulaiman ya samowa Tambutu kwatankwacinsa  da shi ne Ahmad Baba da ya baiwa lakabin  (Ruhin Tambutu). Kuma  daidai ya ke da yadda  Wali Dan Marina  ya bayyana matsayin ilminsa da kansa acikin wasu rubutattun baitocin wakensa da cewa:

(Kullu ilmin zuqtuhu mil’ani, Summa jalastu jalsata-s-shib’ani.)

“Na dandani kowane ilimi har cikina ya cika.

                            Sannan na yi zama irin na wanda ya koshi.”

Shi kadai ya rubuta littatafai da adadinsu ya haura arba’in a cikin fagagen dokoki (fikhu) da ilimin hadisi da tarihin fitattun malamai da siyasa da mandiki (logic). Abu Abdullah Muhammad Ibn Ya’kub al- marubucin littafin tarihin malaman moroko mai taken: “Al-Fihrisah” wanda kuma almajrin Ahamd Baba ne,  ya bayyana shi da cewa: “Dan’uwanmu Ahmad Baba yana daga cikin masana, malamin fikihu  kuma mai cikakkiyar fahimta. Kuma mawallafi ne wanda ya rubuta littatafai masu yawa kuma masu amfani. Sun kuma kunshi nazari na aqali da kuma naqali.”

Ilimomin  aqli, suna nufin wadanda ba na addini ba kai tsaye suna kuma bukatuwa da zurfin  tunani da kuma kirkira, kamar   mandiki da lissafi da ilimin taurari da sauransu. Wannan yana tabbatar da cewa, tsangayar Tambutu ba ilimin  naqali  kamar kur’ani da hadisi da fikihu da usulu kadai ta ke koyarwar ba. A cikin littafinsa na tarihin malamai  mai taken: Kifayatul-muhjat,  Ahmad Baba ya ambaci tarihinsa da na karatunsa. A ciki ya ce, ya yi karatun mandiki a hannun mahaifinsa.

Dangane da Ahmad ne Sa’adi a cikin littafinsa na Tarikh-Sudan  da ya ke ambaton malaman Tambutu ya ke  cewa:

“ Daga cikinsu da akwai malamin fikhu masani  mai yawan sani, wanda ba shi da tamka a zamaninsa, kwararre a cikin dukkanin fannonin ilimi, Abul-Abbas Ahamd Baba….  Ya sha kan dukkanin tsaransa, babu wanda ya ke  iya tattaunawa ta ilimi da shi sai malamansamai mika kai ne ga gaskiya koda kuwa daga  mutanen da su ke komabaya ne a cikin al’umma, kuma baya yin sassauci akan gaskiya koda kuwa a gaban shugabbanni ne da masu mulki”

Bayan karatun addini da dukkanin rassansa, Ahmad Baba ya shiga cikin tarihi a matsayin dan gwagwarmayar kare ‘yancin mutanen Afirka a lokacin da ake kamo su a matsayin bayi. Da akwai jan hankali a cikin sunan da ya baiwa littafinsa mai  taken: “Jalbul-Ni-Imah Wa Daf’ul-Niqmah Bi Mujanibatu al-Zalamah Ulil-zalama”  

Idan za a yi fassara ta kai tsaye ma’anarsa shi ne “jawo ni’ima da kuma kore bala’i ta hanyar nesantar azzalumai masu cuta.”  Yana kuma Magana ne akan yadda ‘yan siyasa masu mulki su ke kamo musulmi a matsayin bayi suna sayar da su. Ya kafa kwararan dalilai daga nassi na addini akan haramcin haka. Kuma ginshikin nazariyya  (Paradigm) wacce ya gina bayanansa akai ita ce cewa:” Dukkanin mutane ‘yantattu ne, a cikin wani kayyadajjen yanayi ne kadai su ke iya zama bayi.”

Bisa la’akari da zamanin da ya yi wancan rubutu da kuma la’aki da fikihun  mazhabar malakiyya wanda ya ke riko da shi, wancan littafin aiki ne mai girma wanda har yanzu manazarta a yammacin turai masu tattauna tsarin bauta a nahiyar Afirka ta yamma suna jinjina masa.

Muhimman littafai guda uku da ya rubuta akan littatafan tarihin rayuwar malamai, mafi yawancinsu na Afrika da ya rayu da su da kuma wadanda su ka gabace shi su ne:

1-Naylul Ibtihaj Bi Tatrizil-Dibaj,

2-  Kifayatul-muhtaj Li ma’arifati Man Laisa fil-dibaj,

3-Zayl Alal Kifayah

Sauran littatafansa sun shafi fikihu da ilimin hadisi da madinki da manhajar koyarwa da sauran fagage masu yawa. Littafinsa na tarihin Muhammad Abdulkarim al-maghili, wanda aka fassara shi zuwa faransanci a 1855 yana daga cikin muhimman madogarar yammacin turai wajen sanin tarihin cigaban dokoki a Afrika.

Ahamd Baba ba haye ya yi wa malunta ba.  Danginsa da aka fi sani da ‘Zuriyar Aqit” su ne masu samarwa Tambutu da  sauran garuruwan Daular Sanghai alkalai da limamai na tsawon  karni biyu a jere. Mahaifinsa shi ne malaminsa na farko  wanda ya koya masa mandiki kamar yadda mu ka gani a sama. Kuma a cikin littafinsa mai taken Zayl ya yi cikakken bayanin kakanninsa malamai da cewa:

“Ahmad Bin Umar Bin Muhammad al-aqit al-Tinbukti, kakana na wurin uba, ana kiransa da Alhaji Ahamd.Msanin fikihu ne da lugga da nahwu da arudh ( ilimin waka). A tsawon rayuwarsa ya maida hankali akan ilimi. Ya kuma rubuta littatafai masu yawa kuma masu amfani da  hannunsa. Ya kuma mutu ya bar littatafai guda dari bakwai wadanda ya gaje su daga kakansa na wurin uwa, masanin fikihu And Agh Muhammad, da kuma kawunsa masanin fikihu da nahwu, Mukhtar. Ya yi aikin Haji kuma ya hadu da Suyudi da Khalid al-waqqad na jami’ar Azhar wanda limami ne  ( farfesa) akan nahwu.”

A cikin wannan littafin kuma ya bada labarin wani kawunsa:

“Abubakar Dan Ahmad Dan Umar Dan Muhamad Aqit. Haifaffen Tumbuktu ne wanda kuma ya zauni madina. Kawuna ne. Mai zuhudu ne da gudun duniya. Mai yawan alheri, mai yawan alheri ne da yawan sadaka duk da cewa yana  da karancin abin duniya. A wurinsa na fara yin karatun nahwu.  Yayi rubuce-rubuce da su ka kunshi nasihohi da  sufanci.”

Daga cikin dangin Ahmad Baba ne  alkali Aqib Ibn Mahmud Ibn Umar Aqit  ya fito:. Shi ne wanda marubucin Tarikh al-Fatash  acikin babi na goma sha biyu ya bayyana da cewa:

Shi ne mafi girman adalci da ijtihadi a tsakanin alkalan da Tambutu ta yi, wanda kuma ba a taba samun kwatankwacinsa gabaninsa  ba, haka nan kuma a bayansa ba a sami daidai da shi ba. Ba kuma za a yi ba har abada!”!

Assa’adi a cikin littafin Tarikh Sudan  a karkashin babi na tara da ya ke ambaton malaman Tambuku da salihan bayinta, ya bayyana  wannan alkalin da  cewa: “ Shi ne wanda ya cika kasarsa da adalci ta yadda ba a sami kwatankwacinsa a ko’ina.”

 Ahmad Baba acikin littafinsa Naylul-Ibtihaj, da  ya kunshi  tarihin malaman musulunci na cikin Afrika da wajenta, ya bayyana wannan alkakin da cewa:  “Mai tsayin daka ne akan gaskiya, baya tsoron zargin mai zargi  akan tafarkin Allah.  Mai shigewa gaba ne wajen yin ayyuka masu wahala da waninsa ya ke kasawa. Yana da karfin guiwa kalubalantar sarki da wanda ya ke kasansa- sarkin. Masu mulki suna kaskantar da kai a gabansa acikin duk abinda ya ke so. Idan kuma ya ga an yi wani abu da baya so, to zai cire kansa daga alkalanci ya shige gida ya rufe kofa har sai sun shawo kansa.”

Alkali a karkashin tsarin Daular Sanghai yana a matsayin jami’in tafiyar da mulki ne, baya ga ayyukan shari’a da raba husumomi tsakanin mutane. Kuma tare da cewa  sarki daga cikin zuriyar Askiyawa ne ya ke nada alkali a cikin garuruwa, sai dai duk da haka, yana cin gashin kansa ne. masu iko ba su tsoma masa baki a cikin ayyukansa.

Malaman Tambutu ba malaman fada ba ne ko masu banbadanci ga masu mulki.  Malamai da alkalai  ba su zuwa fada  sai dai fada ta same su., idan ba wata lalura ba.

Mahmud Ka'ati a cikin littafinsa Tarikh-Fattash ya ambaci  cewa Sarkin Daular Sanghai  mafi girma a tarihinta, Asikya Muhammad  ( Askia The Great). Ya aike da fadawansa su yi masa wani aiki a cikin Tambutu. Alkali Mahmud  Bin Umar  Bin Muhammad Aqit,ya hana a  biyawa sarki bukatunsa, ya kuma kore su daga cikin ganuwa.  Sarki Askiya ya yo tattaki da kansa  ya rabu da fadawansa  ya koma wani wuri nesa da jama'a ya tsaya shi kadai. Ya aikewa da alkali dan sako akan cewa su yi mahada. Bayan haduwarsu ya yi wa alkali tambayoyi akan dalilin da ya hana fadawansa su yi aikin da ta turo su da shi. A karshe alkali ya yi wa sarki tuni da cewa a baya ya zo har gida ya same shi, ya roke shi akan idan ya ga yana aikata wani abu da zai iya kai shi ga shiga wutar jahannama, to ya shiga tsakaninsa da wuta.!  Lokacin sa sarki ya tuna  ya yi wa alkali godiya.

Duk da cewa marubucin littafin bai amabci abinda sarkin ya so aikatawa, sai dai daga jawabin alkali Mahmud za a iya fahimtar cewa wani abu ne da ya kaucewa shari'a, saboda haka ya hane shi.

Anan muna magana ne akan Sarki  Askiya ( Askia the Great)  wanda ya ci katsina da Zamfara da yaki ya kuma  kashe sarakunansu. Ya kuma dorawa  kano haraji na sulusin kudin shigrarta.

Wani abu da ya kamata a yi ishara da shi anan mai alaka da batun alkalanci shi ne: Duk da karfin ikon da alkali ya ke da shi, malaman Tambutu guje masa su ke yi sai ya zama dole su ke amincewa su karbe shi. Ga misali:

Wani malamin mai ban mamaki shi ne  Muhammad Bin Mahmud al-wankari Bagayogo . Ba shi da lokaci nashi na kanshi idan ba  koyar da ilimi ba da  kuma hidima ga mutane. Ga abinda Ahmad Baba ya ke fada akansa a cikin littafinsa na Zayl:

“ Yana daga cikin zababbun bayin Allah , kuma malamai masu aiki da ilim. Aikata alheri ya zamar masa jiki. Yana da kyakkyawan zato ga mutane ta yadda ya ke kallon kowa daidai da kowa, baya ganin  sharri a tare da wani mahaluki. Yaka kai da komowa wajen biya musu bukatu har yana cuta da kansa domin ya yi musu hidima. Yana yi musu nasihi akan neman ilimi. Yaka cinye lokacinsa tsakanin koyar da ilimi da kuma iyalansa, kuma yana da cikakken kaskantar da kai. Yana basu aron littatafai masu kima da ya ke da su ba tare da ya nemi a dawo da su ba. Asanadiyyar haka littatafansa da dama su ka bace. Wani almajiri zai iya zuwa wurinsa aron littafi ya ba shi ba tare da ya san wannan almajirin ba. Da akwai mamaki mai yawa akan wannan  irin halin nashi saboda yadda saye da kuma rubuta littatafai ya ke da tsada da kuma yadda ya ke son littatafai, sai dai yana  sadaukar da kai ne  saboda Allah. Wata rana na je wurinsa ina neman littafin Nahwu, sai ya duba taskarsa ta littatafai ya dauko mani duk wani littafi da ya samu na nahwu.

Na ji wasu mutane suna cewa( cikin mamaki)  “muna zaton wannan malamin ya sha ruwan zam-zam ne da niyyar kada ya gaji da yin karatu, da kuma yawaita ibada, da kuma kudurce alheri ga mutane hatta wadanda su ke azzalumai.” Yana maida hankali akan abinda ya ke yi, kuma ba ya shiga cikin abinda bai shafe shi ba.

A wajen  bada karatu baya gimsuwa da koyar da  sabbin almajirai da dakikai masu nawar fahimta.

Na riske shi, yana yin karatu tun daga farkon asuba har zuwa hantsi, sannan ya koma gidansa ya yi sallar walaha. Daga nan kuma ya tafi ya yi alkalanci, ya kuma yi sulhu a tsakanin mutane, sannan kuma ya yi karatu har zuwa tsakiyar rana, sannan kuma ya yi limancin sallar azahar. Daga nan kuma ya ci gaba da koyarwa har zuwa la’asar. Zai tashi zuwa wasu wuraren ya ci gaba da koyarwa. Bayan sallar magariba kuma zai ci gaba da koyarwa a babban masallaci har zuwa sallar isha. Daga nan ne ya ke komawa gida a makare.”!

A wani wurin cikin wannan littafin ya kara da cewa:

“Sarki ya bukace shi da ya zama mai tafiyar da sha’anin mulki a yankin da ya ke rayuwa  amma ya kiya.”

Wannan malamin daya ne daga cikin malaman Sankore, wadanda  su ke a matsayin taurari masu haske  a cikin  nahiyar Afrika a lokacin da duhu ya mamaye sassa masu yawa na duniya.

Marubuta tarihi suna cewa dalilai biyu ne kadai su ka ingiza daular moroko ta mamaye daular Songhai. Na farkonsu tattalin arziki ne wanda ya sa su ka mamaye ramukan hako gishiri ( wanda ya ke da kima ta tattalin arziki a wancan lokacin fiye da zamunan da su ka biyo biya) a garin Taghaza, da kuma ramukan hako zinariya  da su ke da yawa a karkashin dular Songhai. Dalili na biyu da marubuta tarihi ke Ambato shi ne na siyasar cikin gida. Suna cewa sarkin daular sa’adiyya ta moroko ya kafa rundunar soja mai karfi ta larabawa da kuma ta ‘yan asalin Andulus. Shi kanshi Judar Pasha dan asalin Andulus ne, kuma ba musulmi ba ne. wannan rundunar tana da karfin da ya sa sarki Mansur az-Zahabi ya ke tsoron ta ci gaba da zama a kusa da shi. Za su iya yi masa juyin mulki ko haddasa wani rikici a cikin gida. Saboda haka ya yanke shawarar tura su yaki waje.

Sai dai da akwai dalili na uku da marubutan tarihin ba su ambatawa  wanda shi ne  hassada ta larabwa akan bakaken fata.! Da kuma jin kyashin cewa sun kafa tsangayar ilimi mai karfi a Tambutu wacce ta ke daidai da ta birnin Fas da ta Qarawin a Tunusiya da Jami’ar Azhar a birnin Alkahira. Sanannen abu ne cewa daula ( empire ) kowace daula, a dauri da yanzu, ba ta son kishiya. Yin dubi ga tarihin dukkanin daulolin da su ka bayyana kuma su ka rushe a tsawon tarihi zai tabbatar da wannan.  Shi ne kuma abinda ya ke faruwa da Amerika a yanzu wacce ba ta son kishiya kamar yadda Noam Cheovsky  ya yi kokarin tabbatarwa a cikin littafinsa mai taken: “America Hagemony or Survival”

Abinda ya ke tabbatar da gaskiyar wannan zance shi ne girman barnar da sojojin mamayar moroko su ka yi a cikin birnin Tambutu.  Jurdar ya kirayi malaman Tambutu  da attaijranta ya shigar da bayi goma-goma  a karkashinsu.! Ya kallafa musu gina wa sojojinsa bariki, su kuma zama rika biyansu kudin aiki daga aljihunsu. An kuma rika yin aikin ne daga safiya zuwa sallar isha. Lokacin salloli ne kadai  ake hutawa. Muhammad Ka’ati marubucin littafin Tarikh-sudan yana cewa:

“Ba za a iya ambata masifun da su ka fadawa Tambutu da mutanenta ba. Ba kuma za a iya mabata nuna fin karfi da girman kai da ( sojojin morko) su ka nuna ba. Da sare bishiyoyi suna yin jiragen ruwa da su, kuma da aka kamala su ka sa aka dauke su zuwa bakin ruwa.”

A cikin gari kuwa Judar ya saki sojojinsa su ka rika shiga gidajen mutane suna yin sata da rana. Sun maida ‘yan’tattun ‘ya’ya su ka zama bayi. Sun  kuma ci zarfin mata da yi mu su fyade.

A cikin mawuyacin hali irin wannan malaman addini su ne alkiblar mutane. Alkali Umar Bin Mahmud  na daga cikin malaman da sunasu ya shiga cikin shafukan tarihi wadanda kuma aka rubuta sunayensu da  ruwan zinari.  Lokacin da Judar Pasha ya ke son gina barikin soja ya je wurin wannan alkalin  ya gaishe shi, ya sumbaci kansa da hannunwansa cikin fadanci. Sannan ya bukaci ya bashi gidan da zai kafa sansanin soja a ciki. Shehin malamin ya fada masa kai tsaye tsaye: “ Ni ba sarki ba ne kuma bani da ikon da zan mallaka maka gidan wani”

Karfin soja da bindigogin da  sojojin Moroko su ke da shi bai hana alkali Umar kare talakawa ba.  Shi ne su ke sanyawa a gaba domin ya rage musu wahalar da su ka fada a ciki.  Da shi su ka kama kafa a lokacin da Juddar pasha yaso rushe gidajensu saboda ya gina barikin soja. Ya kuma taka ya samar musu da lokaci mai tsawo da za su yi haka cikin kwanciyar hankali ba tare da sun zama ‘yan gudun hijira ba.

A cikin wani dare daga cikin darare, sojojin Moroko sun yi bazaranar yi wa mazauna Tambutu kisan kiyashi.  Washe gari babu wanda bude kofar gidansa saboda tsoro har zuwa lokacin azahar.  Bayan idar da sallar azahar a cikin masallacin Sankore alkali Umar ya kirayi taron dukkanin manyan gari da su ka hada da  malamai  zuwa gidansa  domin tattauna matakin da za su dauka.

Ganin cewa malamai na shirin daukar matakin da zai iya kawo wa ‘yan mamaya cikas, daya daga cikin kwamandojinsu mai suna Mami ya shiga cikin masallaci ya same su. Ya gaishe su ya yi musu fadanci sannan ya nemi gafara akan abinda sojojinsu su ka aikata na cin zarafin mutanen gari. Ya kuma rantse da cewa su ba su kwamandoji ba ne su ka bada umarni a yi musu hakan.

Lokacin da mutanen gari su ka ga Mami ya shiga gidan alkali sai su ka dauko kibau da takubba da dukkanin makaman da su ke da su, su ka zagaye gidan. Wasu kuma su ka hau kan  rufin masallacin sankore  da ya ke kusa da gidan. Muhammad Bagayogo wanda yana cikin mahalarta taron ya umarnci mutane su kwance damarar yaki saboda abinda su ka ji daga bakin kwamanda Mami.

A kan hanyarsa ta komawa bariki Kwamanda Mami ya ci karo da wani gungun sojojinsu suna yi wa wani mazaunin Tambutu kwacen. Ya nufi inda su ke bisa dokinsa ya sa takobi ya sare kafadar daya daga cikinsu sannan ya bada umarni aka rataye kansa a tsakiyar gari saboda kowa ya gani.

Mutane sun yi farin ciki saboda a zatonsu zaluncin ‘yan mamaya ya        kare. A cikin kwanaki uku daga wannan lokacin, inji mai littafin Tarikh- Fattash, rayuwa ta koma daidai. “Yan mamaya sun ci gaba da hulda da mutane da ciniki a tsakaninsu ba tare da  wata matasala ba.

Sai dai a farkon watan  Muharram na shekarar hijira ta dubu daya da biyu, wani sabon kwamandan sojan mamaya mai suna  Pasha Mahmud ya shigo cikin Tambutu.  Kuma ga dukkanin alamu ya zo ne da wani sabon umarni daga moroko. A ranar ashirin da hudu ga wannan watan ya tara malamai da manyan mutanen gari a cikin masallacin Sankore, sannan kuma ya zo da alkur’ani mai girma da kuma littafin hadisi na Buhari a ajiye a gabansa. Ya bukaci cewa su yi wa sarkin daular Moroko mubaya akan biyayya.!

Malamai sun jagoranci tawaye.! Iyalan Aqit su ne a gaba wajen kin amincewa da mamaya balle su yi wa sarkin moroko mubaya’a. Muhammad Ka’ati ya siffata abinda ya  faru a a wannan lokacin  kamar haka:

“An rufe kofofin masallaci.  Maharba ( ‘yan mamaya)  sun ja daga a bakin kofa. Wasu kuma su ka hau kan rufi. Abinda ya faru ba za a iya bada labarinsa ba. Zuciya ba za ta iya daukar abinda ya faru a wannan wurin ba.Ko kuma bada labarin yadda aka kama alkali Umar da ‘yan’uwansa (iyalan aqit.) Inna Lillahi wa Inna Ilaihi Raji’un.. bala’i ne mai girma wanda ya faru akan musulunci.”

Sun fita da su daga cikin masallaci zuwa barikin soja,bada alkali Umar. Sun dora shi akan farin doki sannan su ka sanya wani soja yana jan dokin. A tare da shi da akwai wasu  malamai biyu wangarawa. Sojojin mamaya sun so sarkafa musu igiya a wuya amma su ka kiya, kuma daya daga cikinsu ya zare takobinsa ya cakawa soja. An kwace wannan yakobin aka kashe wannna malamin da shi. An kuma kashe mutane goma sha hudu. Daga cikinsu da akwai wani babban malami daga zuriyar Aqit mai suna alkali Muhammadul Amin Bin Muhammad Bin Mahmud Bin Umar Bin Muhammad Aqit, da kuma wani Malamin Muhammad al-mukhtar.

Muhammad Ka’ati da ya ke bada labarin abinda ya faru da malaman Tambutu a wannan rana ta ashirin da hudu ga watan Muharram ya ci gaba da cewa:

“Na ji labara daga wa’ad Bin Mukhtar cewa:”A lokacin da maharba su ka fito da alkali Umar daga cikin masallaci da akwai yaronsa mai yi masa hidima a tare da shi. Shi ne kuma mai kula da gidansa. Lokacin da ya ga abinda ya faru da alkali sai ya fara kuka. Sai wani daga cikin maharba ya zare takobi ya sare shi da ita nan take ya mutu. Shi kuwa alkali Umar sai ya yi dariya! Sai aka tambaye shi dalili cikin mamaki. Sai ya ce: Na kasance ina zaton cewa ni ne mafifici akan wannan yaron! Yanzu fifikonsa akaina ya bayyana. Ya rigaye ni isa aljanna.”

An aike da wadannan malaman da aka kama a matsayin fursunoni zuwa moroko. Tare da ‘ya’yansu da matansu da adadinsu ya kai saba’in da doriya. Ahmad Baba da ya ke cikin wannan tawaga ya bada labara kamar haka:

“Akan  hanyarsu ta zuwa moroko rashin lafiya mai tsanani ya kama alkali Umar. Sun bukaci kwamandan da ya ke yi musu rakiya da su dakata da tafiya na wuni guda har ya sami sauki, sai ya kiya. Ya fada musu cewa ba za su tsaya ba daidai da sa’a guda. Su dora shi akan rakumi idan kuma ya mutu a jefar da shi a yi gaba.!”

Wallahil-Azim” inji Ahmad Baba , “Ba mu kara tafiyar mil guda ba muka isa wani wuri mai duwatsun da dawakai ba su iya hawa cikin sauki. Wannan kwamandan ya shige gaban tawaga yana tafiya. Bai yi nisa ba sai dokinsa ya taka duwatsu ya goce ya fadi. Shi ma da ya ke kan dokin ya fado ta ka. Kansa ya fashe ya rugurguje da karfin Allah, ya mutu. Tawaga ta tsaya aka yi masa jana’iza. Mun kuma yada zango a wannan wurin na tsawon kwanaki biyu. Allah kuwa ya baiwa alkali lafiya ya warke.”

 Ga dukkanin alamu, sarkin Moroko ya fuskanci matsin lamba daga malaman addini a cikin masarautarsa akan yadda ya sa aka kamo malaman Tambutu a matsayin fursunonin yaki. Domin kuwa a cikin Tambutu  kwamandan  soja  mamaya Mahmud Pasha ya tara duk wasu masu fada a ji ya basu takardar da ya rubuta sa sanya hannu a kanta a matsayin shaidu. Abinda takardar ta kunsa shi ne kamar haka:

“ Muna sanar da sarki Abul Abbas, wanda mu ke yi wa Allah godiya saboda mulkinsa cewa: Ba mu kama wadannan malaman fikihun da kuma alkali Umar da ‘yan’uwnsa da magoya bayansa ba, sai bayan da su ka bayyana mana abinda ya ke boye a cikin zukatansu na  kiyayya ga sarki( sarkin moroko). Kuma mun yi bincike mun gano cewa suna tare da sarakunan Askiya, suna kuma tara musu  mayaka domin su yake mu. Suna hada baki domin su yi barna!  Kuma sun riga sun kashe sojojin sarki ( sarkin moroko) saba’in da bakwai. Kuma manyan mutanen Tumbuktu da su ka hada da alkali Muhammad su ne shaida akan hakan.”

 Wannan takardar ce Mahmud Pasha ya mikawa Muhammad Bagayogo ya ce masa ya sa hannu akanta. Jawabin farko da ya fito daga bakin wannan malamin shi ne: “ Ina neman tsari a wurin Allah daga shaidan akan in sanya hannu akan wannan takarda”

Pasha ya ce masa: “Dole ka sanya hannu, domin kuwa duk wanda bai sanya hannu ba to za mu guture hannunsa tun daga kan gabarsa ta kafada.”

Malam Bagayoga ya yi dariya sannan ya ce: “ Yanke hannun da za ka yi shine mafi alheri a gare ni akan in yi shaidar zur. Ina neman tsari a wurin Allah. Wallahi yanke kai shi ne mafi soyuwa a gare ni.”

Pasha ya sauya salon magana, ya fara lissafowa malam Bagayogo sunayen manyen mutanen da su ka rattaba hannu akan takarda , sannan ya tamabaye shi.”Shin kai fi duk wadannan mutanen ne zama mutumin kwarai? “

Malamin ya maida jawabi da cewa: “Dukkaninsu sun fi ni zama mutumin kwarai, amma watakila sun ganewa idanunsu abinda ban gani ba. Ba zan bada shaida ba akan abinda ban gani ba”

Lokacin sallar la’asar ya riga ya shigo ana ta takaddama da malam Bagayogo yaki yin shaidar zur. Ya kime ya yi sallar la’asar cikin nutsuwa. Yana gama salla, pasha ya mike cikin karkarwa ya gaishe shi, sannan ya ce masa: “Ka koma gida! Kuma muna bukatar addu’arka, ka kuma yi wa sarki addu’ar ya sami nasara. Allah kuma ya kara yawaita mutane irinka.”

A kan hanya zuwa Moroko daga Tambutu Ahamd Baba ya fado daga kan rakukmi ya karye kafafunsa.  Kuma shi da sauran danginsa a daure su ke cikin sasari. Kuma ba a fito da su daga cikin Tambutu ba sai da aka yi musu ta’adin  littatafansu. Tsakanin wadanda su ka rubuta da hannuwansu da kuma na wasu. Almajirin Ahmad Baba dan kasar Tunis Ahmad al-susy ya fada a cikin littafinsa mai taken: “Bazalul-Munasaha” cewa; an lala littatafan da Ahmad Baba ya mallaka da su ka dai dubu daya da dari shida.!

An shigar da su kurkuku a farkon watan azumin Ramadhan na shekarar hijira ta 1002 zuwa ta 2004. A wannan tsakanin kuwa da dama daga cikin iyalan Aqit sun mutu. Daga cikinsu akawai dansa Muhammad da kuma kawunsa Abdullah Bin Mahmud Bin Aqit. Sarki Mansu bai sake su daga cikin kurkuku ba sai ya da kafa musu sharadin cewa ba za su koma Tambutu ba. Saboda haka aka yi musu daurin talala har  zuwa mutuwar sarki masur. A bangare na uku na wannan kasida a karkashin tsarin ilimi a Tambutu za mu ga yadda Ahmad Baba ya kafa tsangaya a cikin Mokoro wacce dubban almajirai su ke karatu.

Da ya ke muna magana ne akan kutun binciken akida wacce masu daskararren tunani su ka kafawa malaman Tambutu bayan daruruwan shekaru da mutuwarsu, bari kitse wannan bangaren da wata kotu ta lamiri (Conscience) da Ahmad Baba ya kafawa sarkin Moroko a cikin fadarwa.

A lokacin da su ka shiga Moroko an kai Ahmad Baba  cikin fadar sarki  Mansur Al-Zahbi. Shi kuwa wannan sarkin bisa al’adarsa  baya ganawa da talakawa gaba da gaba sai an sanya shamaki a tsakninsa da su. Bas u ganinsa sai dai su rika jin maganarsa.

 Ga yadda  ta kaya tsakaninsu.

Ahamd Baba:  “Allah madaukaki yana fadin cewa: “Ba zai yiyu ga mutum Allah ya yi  zance da shi ba sai ko Allah ya yi masa wahayi ko a bayan shamaki” Kai, kana kwatanta kanka da ubangijin talikai. Idan har kana da bukatar ka yi magana da mu to ka fito fili.”

Sarki Mansur ya fahimci cewa  mutum irin Ahmad Baba ya sha banban da sauran mutane Ya san cewa wanda duk zai iya kalubalantarsa har haka, ya gaskata kansa. Ba kuma jinsin mutanen da kwarjinin mai mulki ya ke yi wa tasiri ba ne.! Ba kuma matsoraci ba ne, domin kuwa babu daren da jemage bai gani ba.! Shi ne wanda aka kamo a matsayin fursuna daure cikin sasari tun daga Tambutu har nan cikin fadarsa. Akan hanya babu azabar da bai sha ba. Kuma kafafunsa a karye su ke. . Ya sa an kawo shi  ne cikin fadarsa domin ya yi masa hukunci, mai makon haka sai ya zama shi ne wanda Ahamd Baba ya ke hukuntawa.  Babu wani zabi a gaban sarki idan ba ya sa fadawansa su dauke shamaki ba, saboda ya fuskanci Ahmad Baba gaba-da gaba. Kafi kuma ya bude baki ya sake yin magana Ahamd Baba ya sake y masa tamaba.

“Da wane dalili za ka sa a kamo ni daga Tambutu zuwa nan? “

Wannan tambayar ta karshe tana nufin hukunta sarki  Mansur da aikata laifin yaki.! Kuma shakka babu idan har yana da rayayyen lamiri laifukan da sojojinsa su ka yi a Tambutu zai fado masa a zuci.!  Jawabin da ya baiwa Ahmad Baba na kare kai ne.

 “Saboda kada a sami rabuwar kawuna”!

Bai san cewa mutumin da ya ke zaune a gabansa cikin radadin karayar kafafu ba, daga gidan alkalanci ya fito ba. Kuma shi kanshi kusa ne ta fuskar sanin doka domin ya yi wa littatfin Mukhtasrul-Khalil sharhi. Ya  yi masa wata tambyar wacce ta rusa dalilin da ya kafa. Ta kuma sake tabbatar da cewa shi mai laifin yaki ne.

“Shin ka same shi yanzu ta hanyar kwace mani kayana-littatafai da kuma fado dani daga kan doki da karya kafafuwana? Kuma me ya sa ka kyale Tilmisan? - tsangyar ilimi wacce ta ke tafiya kafada-da kafada da Tambutu.

Gwargadon yadda sarki ya ke ci gaba da magana laifukansa su ke kara fitowa fili. Da kuma nuna jahilcinsa a gaban wannan malamin wanda shi ne ruhin Tambutu.

kamar yadda Ahmad Baba ya hukunta sarkin moroko, barnar da masu rusa kabarukan malaman Tambutu su ke yi, suna hukunta kansu ne da kansu. Duniya baki daya ta shaida cewa su mabarnata ne, kuma malaman da su ke kwance cikin kusheyinsu su ne wadanda aka zalunta.