A+ R A-
22 February 2024

Ayatullah Gorgani: Wilayatul Fakih Alama Ce Ta Wilayar Imamai (Amincin Allah Ya Tabbata A gare Su)

Ayatullah Sayyid Muhammad Ali Alawi Gorgani, daya daga cikin maraja’an duniyar Shia dake zaune a birnin Qum na Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya bayyana cewar manufar halittar mutum ita ce don ya kai ga kamala, yana mai cewa: wilaya cika ce ta addini da kuma ni’ima (ta Ubangiji), don haka ibada ba ta da wata kima in ba tare da wilaya ba.

Ayatullah Gorgani ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da wasu jami’an tsaro na lardin Qum inda ya ce Allah Madaukakin Sarki, cikin Alkur’ani mai girma, ya yi bayanin hanyoyin da mutum zai bi don kai wa ga kamala.

Ayatullahi Gorgani ya ci gaba da cewa: wajibi ne a kan mutum ya yi kokari wajen neman ilimi da kuma masaniyar abin da ya shiga masa dubu a dukkanin bangarori.

Haka nan kuma yayin da ya ke ishara da ayar nan mai girma ta cikan addini da ta zo cikin Alkur’ani da ke cewa: (الْيَوْمَ أَكْمَلْتُ لَكُمْ دِينَكُمْ وَأَتْمَمْتُ عَلَيْكُمْ نِعْمَتِي وَرَضِيتُ لَكُمُ الْأِسْلامَ دِيناً) Ayatullah Gorgani ya ce: Wilaya dai cikamaki ne na addini da kuma ni’ima ta Ubangiji, don haka ibada ba ta da wata kima in ba tare da wilaya ba. Wannan ne ya ke wajabta yin kokari wajen fahimtar wilaya.

Ayatullah Gorgani ya kirayi al’ummar musulmi da su ba da himma wajen gudanar da bukukuwan girmama wannan rana mai girma ta Ghadir gwargwadon yadda za  su iya yana mai cewa: Ranar Ghadir rana ce mai girma. Sannan kuma wilayar Amirul Muminin (a.s) tana sama da dukkanin wata wilaya, kamar yadda kuma Wilayatul fakih wata karamar alama ce ta wannan wilayah ta Amirul Muminin (a.s).

Ayatullah Gorgani ya ci gaba da cewa: Imam Mahdi (a.s) ya wajabta wa mutane biyayya ga malamai da fukaha’u, sannan kuma shugaban wadannan fukaha’un shi ne jagoran juyin juya halin Musulunci, don kuwa saba wa umurninsa sai sanya farin ciki cikin zukatan makiya.