
Ayatullah N. Hamedani: Babu Wani Karfi A Duniyan Nan Da Ya Isa Hana Iran Amfanuwa Da Makamashin Nukiliya
- Details
- Published Date
- Written by Muhd Awwal Bauchi
- Category: Marajaai
- Hits: 3031

Ayatullah Noori Hamedani, daya daga cikin manyan maraja’an duniyar Shia da ke zaune a birnin Qum na Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ya bayyana cewar mallakar fasahar nukiliya daya ne daga cikin alamu da tsayin dakan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, don haka babu wani da ya isa ya hana Iran amfanuwa da makamashin nukiliyan.
Ayatullah Noori Hamedani ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a wajen darasin fikihu da yake bayarwa a birnin Qum inda ya ce a bisa mahangar Alkur’ani mai girma kafirai da munafukai da sahyoniyawa abokan gaban Musulunci da musulmi ne na har abada don haka ya ce: A saboda haka ne wadannan kusurwoyi uku suka tsaya kyam wajen fada da gaskiya. Hakan kuwa yana wajabta mana farkawa da kuma yin taka tsantsan.
Babban malamin ya ci gaba da cewa: Wajibi ne a koda yaushe mu zamanto cikin shiri wajen tinkarar wadannan kungiyoyin. Ayatullah Noori Hamedani ya kara da cewa a halin yanzu dai kungiyoyi masu kafirta musulmi sun zamanto wani kayan aikin wadannan mutanen.
Ayatullah Noori Hamedani ya ci gaba da cewa abin da Iran ta samu a fagen fasahar nukiliya ya samo asali ne albarkacin kokari da tsayin dakan masanan kasar matasa. Don haka sai ya ci gaba da cewa: Iran ta sami mallakar fasahar nukiliya ne albarkacin falala ta Ubangiji Madaukakin Sarki da kuma aiki ba dare ba rana na al’ummar Iran ma’abota imani. Don haka babu wani da yake da karfin hana su amfanuwa da wannan fasahar.