A+ R A-
22 February 2024

Ayatullah Sistani Ya Bukaci ‘Yan Siyasar Iraki Da Su Zabi Firayi Ministan Da Zai Kawo Karshen Masu Kafirta Musulmi

Babban marja’in addini na kasar Iraki Ayatullah Sayyid Ali Sistani ya kirayi ‘yan siyasan kasar Irakin da su zabi firayi ministan da zai kawo karshen rikicin da kasar ta fada ciki sakamakon ayyukan kungiyar ta’addancin nan ta Da’esh (ISIS) masu kafirta al’umma a kasar.

Wakilin Ayatullah Sistanin, Sheikh Abdul Mahdi al-Karbala'i, ne ya sanar da hakan a lokacin da yake gabatar da hudubar sallar Juma’a a yau din nan inda ya ce sakamakon ci gaba da ayyukan ta’addancin da kungiyar Da’esh din take yi ya zama wajibi ‘yan majalisar kasar Irakin su zabi firayi ministan da ke da karfin kawo karshen halin zaman dardar da rashin tsaro da Irakin take fuskanta sakamakon ayyukan ‘yan ta’addan na Da’esh.

Wannan kiran ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da kace nace tsakanin ‘yan siyasar kasar dangane da zaban sabon firayi ministan kasar. Jam’iyyar Daulatul Qanun ta firayi minista Nuri al-Maliki wacce ita ce ta fi yawan ‘yan majalisu a majalisar kasar ta tsaya kyam kan sake gabatar da shi a matsayin firayi ministan, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanadar na cewa jam’iyyar da ta fi yawan ‘yan majalisu ita ce take da hakkin gabatar da firayi minista.

A bisa yarjejeniyar da aka cimma dai, firayi ministan Irakin zai fito ne daga cikin larabawa ‘yan Shi’an kasar, shi kuma shugaban kasa daga bangaren Kurdawa sannan shugaban majalisa kuma daga larabawa ‘yan Sunna.

Rahotanni daga Irakin suna nuni da cewa ‘yan kungiyar Da’esh din, da suke samun goyon bayan wasu kasashen larabawan yankin Tekun Fashan, suna ci gaba da kwace wasu yankuna na kasar Irakin, na baya-bayan nan su ne garuruwan Sinjar da Zumar da ke arewacin kasar Irakin inda suke ci gaba da gallaza wa musulmi da kiristocin wadannan yankunan.