A+ R A-
22 February 2024

Ayatullah Mudarrisi Yayi Kakkausar Suka Ga Hukumcin Zaluncin Da Saudiyya Ta Yanke Wa Sheikh al-Nimr

Ayatullah Sayyid Muhammad Taqi al-Mudarrisi, daya daga cikin maraja’an Shi’a da ke kasar Iraki yayi Allah wadai da hukuncin zaluncin da gwamnatin Saudiyya ta yanke wa sanannen malamin Shi’a na kasar Ayatullah Allamah Sheikh Nimr Bakir al-Nimr yana mai cewa zartar da wannan hukunci zai sanya kasar Saudiyyan cikin mawuyacin hali.

Ayatullah Mudarrisi ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ofishinsa ya fitar a yau din nan asabar (18-10-2014) inda ya ce cikin mamaki ya sami labarin hukuncin da wasu jahilan alkalai suka yanke wa babban malami Ayatullah Sheikh Nimr Bakir al-Nimr bayan zaman kotu na jeka na yi ka.

Ayatullah Taqi Mudarrisi ya ci gaba da cewa: Ko shakka babu irin wannan hukunci na zalunci zai sanya kasar Saudiyya cikin mawuyacin hali kamar yadda irin sa ya haifar da zubar da jinin da ke faruwa a kasashen musulmi.

Har ila yau Ayatullah Mudarrisi ya kara da cewa: yakin kabilanci da mazhaba da ke faruwa a halin yanzu a kasashen musulmi wanda kuma tun da jimawa  masu fatan alheri ga duniyar musulmi suka jima suna jan kunne dangane da hakan, daya ne daga cikin makirce-makircen sahyoniyawan duniya a kan kasashen musulmi.

Sayyid Taqi Mudarrisi ya ci gaba da cewa: Sheikh al-Nimr dai ya kasance daga cikin fitattun malamai na addini mai fatan ganin alheri da duniyar musulmi, don haka zarginsa da irin wannan tuhuma maras tushe da kuma yanke masa hukumci yana a matsayin keta hurumin addini da sakon da Ma’aiki (s.a.w.a) ya zo da shi.

Ayatullah Taqi Mudarrisi ya kammala sanarwar tasa da cewa: A daidai lokacin da muke Allah wadai da keta hurumin ababe masu tsarki na Musulunci da kuma malaman addini na kowace mazhaba ce kuwa, muna rokon Allah Madaukakin Sarki da ya taimaki al’ummarmu a fadar da take yi da irin wannan hukunci na zalunci, sannan kuma ya kare duniyar musulmi daga bakar aniyar masu rura wutar kabilanci da kuma kafirta musulmi.