A+ R A-
22 February 2024

Dakarun IRGC Za Su Ɗau Dukkan Matakan Da Suka Dace Wajen Kare Manufofin Iran

Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na ƙasar Iran (IRGC) sun bayyana cewar ba su taɓa yin ƙasa a gwuiwa wajen kare nasarorin da juyin juya halin Musulunci ya samu bugu da ƙari kan manufofin ƙasar Iran da al’ummarta ba.

Dakarun na IRGC sun bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da suka fitar a ranar Alhamis (30/07/2020) bayan kammala gagarumin atisayen sojin da suka gudanar da aka ba shi sunan Atisayen Payambar-e A’azam 14 (Manzo mafi girma) inda suka ce zaratan sojojin ba za su yi dukkanin abin da za su iya wajen kare manufofin ƙasar.

Har ila yau sanarwar ta bayyana cewar an cimma gagarumar nasara da kuma manufar da ake son cimmawa a yayin atisayen da aka gudanar ɗin da ya haɗa da harba makami mai linzami mai cin dogon zango daga ƙarƙashin ƙasa da aka yi, wanda a karon farko kenan da wata ƙasa ta yi hakan, tarwatsa na’urorin sadarwa na maƙiya, nasarar harba wasu makamai masu linzami da ake harba su daga gaɓar ruwa zuwa cikin tekun da kuma waɗanda ake harbawa daga teku zuwa tekun da dai sauransu.

Shi dai wannan atisayen ɓangaren kare sararin samaniyya da kuma sojojin ruwa na dakarun IRGC ɗin ne suka gudanar da shi a lardin Hormozgan da ke yammacin mashigar ruwan nan Hormuz mai muhimmanci da kuma Tekun Fasha.

Har ila yau an gudanar da atisayen ne ƙarƙashin sanya idon tauraron ɗan’adam ɗin nan Nour 1 wanda shi ne tauraron ɗan’adam na soji na farko da dakarun IRGC ɗin suka harba sararin samaniyya a watan Aprilun da ya gabata.

Har ila yau tauraron ɗan’adam ɗin ya ɗauko hoton sansanin sojin saman Amurka na al-Udeid da ke ƙasar Кatar, wanda shi ne sansanin sojin Amurka mafi girma a Yammacin Asiya lamarin da ya tada hankalin Amurkawan. Wasu rahotannin sun ce a yayin da dakarun na IRGC suke gudanar da wannan atisayen da kuma harba makami mai linzami mai cin dogon zango, jami’an Amurkan sun buƙaci sojojin da suke wannan sansani na al-Udeid da kuma al-Dhafra da ke Haɗaɗɗiyar Daula Larabawa da su ɓuya a ƙarƙashin ƙasa kamar yadda kuma suka sanya sansanonin cikin halin ko ta kwana don tsoron abin da zai iya faruwa.