A+ R A-
22 February 2024

Кulla Alaƙar UAE Da ‘Isra’ila’.. Кoƙarin Samun Tasiri A Кasashen Larabawa Ko Barazana Ga Iran?

Tun dai bayan ga aka sanar da ƙulla alaƙa, a fili, tsakanin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa a ranar Juma’ar da ta gabata ya zuwa yanzu ake ci gaba da tofin Allah tsine ga hakan a kusan dukkanin duniya kama daga yankin gabas ta tsakiya zuwa sauran ƙasashen musulmi.

Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ita ce ƙasar Larabawa ta uku, bayan Masar da Jordan, da ta sanar da ƙulla alaƙa a fili da haramtacciyar ƙasar Isra’ila, duk kuwa da cewa shekara da shekaru kenan wasu ƙasashen larabawan suka ƙulla alaƙa ta ɓoye da Isra’ilan. Ɗaya daga cikin abubuwan da suke tabbatar da hakan kuwa akwai ziyarar da firayi ministan ‘Isra’ilan’ Benjamin Netanyahu ya kai ƙasar Oman a shekarar da ta gabata da ganawar da yayi da sarkin ƙasar, haka nan da kuma rahotannin da suke tabbatar da yadda Saudiyya ta dinga ba wa jiragen saman Isra’ilan izinin ratsa sararin samaniyarta don zuwa wajajen da suke son zuwa da dai sauransu. A ɓangare guda kuma ga maganganun da suke yawo na shirin gwamnatin Sudan na ƙulla alaƙa da Isra’ilan. Saɓanin yadda Sudan ɗin ta kasance a baya a matsayin ɗaya daga cikin ƙasashen da suke goyon bayan al’amarin Falasɗinu da ƙungiyoyin gwagwarmaya.

Ita kanta Saudiyya, bayan ɗarewa karagar mulkin Sarki Salman da ɗansa Muhammad Bin Salman a matsayin yariya mai jiran gado, Saudiyyan ta gudanar da wasu abubuwa waɗanda suke nuni ga ƙoƙarinta na kusantar Isra’ila da kuma biya mata buƙata. Cikin ‘yan shekarun baya-bayan nan Saudiyyan tana ƙoƙarin nuna kanta a matsayin ƙasa mai ƙarfi da tasiri alal aƙalla a duniyar musulmi wacce abin da take so shi za a yi, babban misalin hakan shi ne yaƙin da ta ƙaddamar a kan ƙasar Yemen, to sai dai kisan gillan da aka yi wa sanannen ɗan jaridar ƙasar Jamal Khashoggi da ake zargin da hannun Bin Salman ɗin a ciki da irin Allah wadai da aka yi da Saudiyyan, hakan ya ɗaure hannayen Sarki Salman da ɗan nasa, lamarin da a ɓangare guda kuma ya ba wa Amurka da Isra’ila wata dama na ci gaba da yi mata matsin lamba da kafa mata sharuɗɗa matuƙar tana son ta fita daga cikin wannan abin kunyar da kuma ci gaba da samun irin goyon bayan da suke ba ta.

Bayan yaƙin Larabawa da Isra’ila a shekarar 1967 da irin kashin da larabawan suka sha, hakan ya buɗe wani sabon shafi na alaƙar gwamnatocin larabawan da Isra’ila. Wannan nasarar da sahyoniyawan suka samu a kan larabawa, bisa taimakon Amurka, ya sanya Isra’ilan ta samun gindin zama da kuma tasiri mai girman gaske cikin abubuwan da ke gudana a yankin Gabas ta tsakiya. Bayanai na sirri da na bayyane suna nuni da irin rawar da ƙasar Masar, musamman tsohon shugaban ƙasar Anwar Sadat ta taka wajen tabbatar da ikon Isra’ilan kai hatta ma wasu bayanan suna nuni da irin rawar da ta taka wajen irin kashin da larabawa suka sha a hannun yahudawan. Sadat dai shi ne shugaban larabawa na farko da ya sanya hannu kan yarjejeniyar sulhu da Isra’ila wato yarjejeniyar Camp David. Bayan wannan yarjejeniyar kuma sai yarjejeniyar Oslo waɗanda su ne tushen alaƙar larabawa da Isra’ila a bayyana da kuma a ɓoye.

Kamar yadda wasu tsoffin jami’an ma’aikatar harkokin wajen haramtacciyar ƙasar Isra’ilan suka faɗi ne cewa abin da aka cimma a halin yanzu na sanar da ƙulla alaƙa da UAE ɗin ba lamari ne na yau ba, face dai wani ƙoƙari da shige da fice na shekara da shekaru da aka dinga yi a ɓoye da ƙasashen larabawan.

Wani lamari da ke da muhimmanci shi ne cewa kafin nasarar juyin juya halin Musulunci a ƙasar Iran, Isra’ila ta kasance tana da irin wannan alaƙa ta ƙut da ƙut da gwamnatin Iran na wancan lokacin, duk kuwa da cewa mafi yawanta a ɓoye ne, wacce manufarta ita ce ƙarfafa gwamnatin Shah ta Iran ta wancan lokacin a matsayin wacce za ta zamanto mata tamkar wata ‘yar sanda da za ta kare mata manufofinta a yankin da kuma ƙoƙari wajen raunana ƙasashen larabawan. Amma bayan nasarar juyin juya halin Musulunci da kuma irin farkawa ta Musulunci da aka samu a kusan dukkanin ƙasashen musulmi da na larabawa, Isra’ila da Amurkan sun koma ga larabawan da nufin raunana Jamhuriyar Musuluncin da mayar da ita a matsayin babbar abokiyar gaba maimakon haramtacciyar ƙasar Isra’ilan wacce take mamaye da Masallacin Al-Aƙsa.

To sai dai abin da ya bayyana a halin yanzu shi ne cewa abubuwan da suka faru cikin ‘yan shekarun nan, waɗanda dukkanin alamu suna nuni da cewa an so a yi amfani da su ne wajen raunana Iran da kuma sansanin gwagwarmaya, kama daga harin 11 ga watan Satumba zuwa ga mamayar da Amurka ta yi wa Afghanistan da Iraƙi da kifar da gwamnatin Saddam, zuwa ga yaƙin da Isra’ila ta ƙaddamar kan Labanon a 2006 zuwa ga yunƙurin juyin juya halin da suka faru a ƙasashen larabawan a shekara ta 2011, dukkanin waɗannan abubuwan sun zamanto abubuwan da suka ƙara ƙarfafa Iran da kuma sansanin gwagwarmayar a yankin, saɓanin yadda Amurka da Isra’ilan da wasu larabawan suka so.

Don haka ne ma da dama suke ganin baya ga batun Falasɗinu da kuma cimma manufofinsu a Falasɗinun, amma ƙulla wannan alaƙa da sahyoniyawan suka yi da UAE wani ƙoƙari ne na raunana Iran da sansanin gwagwarmaya sakamakon kusanci na iyaka da ke tsakanin Iran da UAE ɗin. A tunaninsu hakan zai ba su damar cimma wannan manufa da suke da ita da kuma cike giɓin irin kashin da suka sha a hannun Iran ɗin a Siriya da Labanon.