A+ R A-
07 June 2023

Ziyarar Macron Labanon Da Kokarin Mai Da Hizbullah Saniyar Ware

A daren shekaran jiya Talata ce dai shugaban ƙasar Faransa, Emmanuel Macron ya sake dawowa ƙasar Labanon, kamar yadda yayi alƙawari bayan ziyararsa ta farko bayan faruwar fashewar sinadaran da ta faru a birnin na Beirut a farko-farkon watan Augustan da ta gabata. Da dama dai suna ganin akwai wata manufa da Macron yake son cimmawa cikin waɗannan ziyarar, wanda mafi ƙarancin hakan ita ce sake dawo da irin tasirin da ƙasar Faransa take da shi a kasar Labanon, duk kuwa da cewa wasu kuma suna ganin lamarin ya wuce nan.

Masu fashin baƙin magana dai suna ganin akwai wasu abubuwa guda biyu da suke faruwa a halin yanzu a Labanon waɗanda da wuya a ce ba su da alaƙa da junansu, waɗanda kuma daga dukkan alamu manufa guda ake son cimmawa da su. Na farko dai shi ne tasiri da tsoma bakin ƙasashen waje a fagen siyasar Labanon da nufin haifar da wani sabon yanayi ta hanyar gwamnatin da ake shirin kafawa a ƙasar. Na biyu kuma shi ne irin baƙar farfagandar da ake yaɗawa a ciki da wajen ƙasar Labanon ɗin a kan ƙungiyar Hizbullah musamman ta hanyar ƙoƙarin jingina mata batun sinadarin Ammonium Nitrate ɗin da ya fashe a tashar bakin ruwan birnin Beirut a kwanakin baya da yayi sanadiyyar mutuwa da kuma raunana dubban mutanen ƙasar.

Wasu majiyoyin kasar Faransa sun jiyo shugaba Macron ɗin yana faɗin cewa faruwar yaƙin basasa a Labanon dai wani abu ne da babu makawa sai ya faru matuƙar dai ƙasashen duniya suka yi watsi da ƙasar da barinta ita kaɗai ɗinta a hannun ‘yan siyasar ƙasar. Da dama dai suna sanya alamun tambaya kan me Macron yake nufi da wannan tunani da kalami na sa, musamman ganin babu wani lokacin da ƙasashen duniya suka yi wani abu don amfanin al’ummar Labanon ba tare da sun fara dubi da su kansu da amfanin da za su samu ba ko kuma don cimma wata manufa da suke da ita ba.

Da dama daga cikin masana harkokin siyasa da kuma abubuwan da ke faruwa a yankin Gabasa ta tsakiya sun san cewa waɗannan maganganu na Macron da kuma wannan ziyara da ya ke kawowa Labanon ba wani lamari ne da ƙasar Faransan ta yi na gaban kanta ba tare da sanya albarka ko kuma umurni daga wani waje na daban ba, abin nufi shi ne cewa a halin yanzu dai Faransan tana ƙoƙari ne wajen jagorantar wani sabon shiri da tsari na ƙasashen yammaci wajen haifar da wani sabon tsarin gudanarwa a fagen siyasar ƙasar Labanon da ya ginu bisa waɗannan abubuwan:

Na farko dai daga dukkan alamu ƙasashen yammacin sun fahimci cewa matsin lamba kan ƙasar Labanon da al’ummarta ba zai iya raunana ƙungiyar Hizbullah da ƙawayenta ba, kamar yadda abubuwan da suka faru cikin ‘yan watannin bayan nan suka tabbatar das hi bayan matsin lamba na tattalin arziki da turawan suka yi wa Labanon, don haka akwai buƙatar su shigo ta wata hanyar ta daban ta hanyar kafa wata sabuwar gwamnati wacce ta hanyarta za a iya nesanta Hizbullah ɗin daga harkokin gudanarwa da na gwamnati a kasar ta hanyar batun kafa gwamnati da za a ta kumshi abin da suka kira ‘kwararru kawai ba wai ɓangarori da ƙungiyoyi na siyasa na ƙasar ba, kamar yadda yake faruwa a halin yanzu.

Na biyu shi ne ƙoƙari wajen ganin an gudanar da zaɓuɓɓuka a ƙasar wanda a tunaninsu hakan zai iya haifar da wasu sauye-sauye a fagen siyasar ƙasar ta hanyar yin dukkanin abin da za su iya wajen ganin ƙungiyoyi da ‘yan siyasar da suke so su ne za su samu rinjaye a majalisar ƙasar ko da kuwa ta hanyar maguɗi ne wanda hakan zai ba su damar kafa gwamnati irin wacce suke so, ana iya ganin hakan kuwa a fili ta hanyar irin baƙar farfagandar da a halin yanzu ake ci gaba da yi kan ƙungiyar ta Hizbullah da ƙawayenta duk dai da nufin nesantar da al’umma daga gare su.

Na uku kuma shi ne ci gaba da tsoratar da al’ummar Labanon da cewa matuƙar suka ƙi amincewa da abin da turawan suke so, to kuwa za su fuskanci matsanancin matsin lamba na tattalin arziki da zamantakewa a ƙasar, wanda watakila batun barazanar faruwar yaƙin basasa da Macron ya ke magana a kai yana iya shigowa cikin wannan ɓangaren na tsoratar da al’ummar.

Dubi cikin fagen siyasa na Labanon cikin ‘yan watannin baya-bayan nan zai iya tabbatar da wannan lamarin musamman idan aka yi la’akari da irin baƙar farfangandar da ake yaɗawa kan kungiyar ta Hizbullah ta bangarori daban-daban, wanda wasu majiyoyin sun  tabbatar da cewa Isra’ila ce take jagorantar wannan aikin kamar yadda wasu kafafen labaran Isra’ilan suka bayyana cewa halin yanzu musamman bayan faruwar fashewar tashar bakin ruwa ta Beirut wata dama ce ta samu wajen ganin an raunana ƙungiyar ta Hizbullah.

To sai dai kuma, dubi cikin tarihi da kuma abubuwan da suka faru a baya, za su tabbatar mana da cewa wannan dai ba shi karon farko da ƙungiyar take fuskantar irin wannan matsin lambar ba, to amma albarkacin irin hikima da hangen nesan jami’an ƙungiyar, a bangare guda da kuma dogaro da Allah da kuma gaskiya da suka yi, ƙungiyar ta tsallake irin waɗancan makirce-makirce da aka ƙulla mata, don haka a wannan karon ma, da yardar Allah, za ta tsallake.