A+ R A-
22 February 2024

Jagora Imam Khamenei Ga Ismail Haniya: Iran Ba Za Ta Yi Kasa A Gwiwa Wajen Taimakon Falastinawa Ba

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta taɓa yin ƙasa a gwuiwa ba wajen tabbatar da haƙƙoƙin al’ummar Falasɗinu da kuma kare su daga sharrin sahyoniyawa ba.

Jagoran ya bayyana hakan ne cikin wata wasiƙa da ya aike wa shugaban ɓangaren siyasa na ƙungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas, Malam Isma’il Haniya a ranar 4 ga watan Yulin 2020, a matsayin amsar wasiƙar da ya aiko masa a kwanakin baya.

Abin da ke tafe fassarar amsar wasiƙar ne:

 

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Ƙai

Ɗan’uwa mujahidi kuma abin ƙauna Mai Girma Malam Isma’il Haniya

Shugaban ɓangaren siyasa na ƙungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Falasɗinu, Hamas.

Assalamu Alaikum.

Na karanta wasiƙar da ka aiko min da kyau dangane da abubuwan da ke faruwa a baya-bayan nan a Falasɗinu. Lalle da yayin da na ke godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki dangane da yadda yunƙurin al’ummar Falasɗinu da kuma tsayin dakansu wajen tinƙarar makirce-makircen Amurka da gwamnatin Sahyoniyawa ya haifar da rauni da kuma rashin nasararsu, a ɗaya ɓangaren kuma hakan ya haifar da ɗaukaka ga al’ummar Musulunci. Haka nan kuma ina godiya da kuma jinjina muku saboda ƙoƙari da kuma jaruntakarku.

Duk kuwa da irin shan kashin da ba za a iya cike giɓinsa ba da suka sha a fagage daban-daban, maƙiyan sun ci gaba da gudanar da siyasarsu ta mamaya da take haƙƙoƙin musulmi Falasɗinawa. Da fari dai ta hanyar matsin lamba na tattalin arziki da killace Zirin Gaza da ake zalunta daga nan kuma suka gabatar da batun yarjejeniyar sulhu ta yaudara. To sai dai ƙungiyoyin gwagwarmaya da kuma jaruman al’ummar Falasɗinu sun tsallake wannan barazana da kuma kwaɗaitarwa ta hanyar amfani da hankali da kuma ƙwarewar da suke da ita. Sannan kamar yadda a baya suka samar wa kansu ɗaukaka, ta hanyar tsayin daka maras tamka, a nan gaba ma za su ci gaba da tafiya bisa wannan miƙaƙƙen tafarki, insha Allah. Ko shakka babu hangen nesa da kuma haɗin kai da aiki tare tsakanin al’umma da kuma ƙungiyoyin Falasɗinawa sun taka gagarumar rawa wajen daƙile wannan makirci na maƙiyan. Lalle hakan zai ci gaba da janyo musu taimakon Ubangiji.

Jamhuriyar Musulunci ta Iran, kamar yadda ta saba, bisa nauyi na addini da kuma ‘yan’adamtaka da suka ginu bisa koyarwar juyin juya halin Musulunci, ba za ta taba yin ƙasa a gwuiwa wajen goyon bayan al’ummar Falasɗinu da ake zalunta da kuma tabbatar da haƙƙoƙinsu ba, haka nan da kuma kore sharrin haramtacciyar gwamnatin sahyoniyawa ‘yan fashin ƙasa. Ina roƙon Allah Maɗaukakin Sarki ƙarin ɗaukaka da ƙarfi a gare ka.

Wassalamu Alaikum wa rahamatullah

Sayyid Ali Khamenei.