A+ R A-
22 February 2024

Shika-Shikan Musulunci A Wajen Shi'a

 

Ginshikan (Shika-Shikan) Musulunci A Wajen Shi'a

Gabatarwa:

 

Tsawon tarihi musamman a wannan zamani na mu, dan'adam ya kan yi amfani da wasu hanyoyi ko kuma na'urori daban-daban na zamani wajen biyan bukatunsa da kuma gudanar da rayuwarsa cikin sauki kuma yadda ya ke so. Daya daga cikin irin wadannan na'urori ita ce na'ura mai kwakwalwa ko kuma kwamfuta wacce take gudanar da ayyuka masu ban mamaki kuma cikin sauri. A matsayin misali idan muka dauki aikin likitanci, za mu ga cewa a lokacin da wani likita yake neman wani bayani dangane da irin cuta da kuma tarihin cutar da wani mara lafiya da ya zo wajensa don neman magani, nan take daidai da irin bayanan da aka sanya mata, wannan na'urar za ta fito masa da wadannan bayanai don ya duba su da kuma sanin irin maganin da zai ba wa wannan mara lafiyan da sauransu. Haka nan dalibin jami'a ko kuma makaranta ta addini da sauransu, a duk lokacin da ya ke neman wani bayani na ilimi, cikin sauki wannan na'ura za ta fito masa da wadannan bayanai wadanda idan da a ce shi ne zai binciko su, to yana bukatar lokaci mai yawan gaske wajen gano su idan ma har zai iya gano su gaba dayan.

Wannan 'yan wasu misalai ne kawai, amma hanyoyin amfani da ita cikin rayuwar mutane suna da yawan gaske. Haka lamarin ya ke dangane da wasu na'urorin da kuma hanyoyin daban-daban da dan'adam yake amfani da su wajen ciyar da rayuwarsa gaba tun farkon halittarsa har zuwa karshen duniya, kowane zamani daidai da irin ilimi da ci gaban da ya ke da shi.

To abin tambaya a nan shi ne cewa shin hankali zai yarda da cewa wannan na'urar da irin ayyukan da take gudanarwa, haka kawai ta samar da kanta ba tare da wani shiri da kokari daga wani bangare ba? Ko shin irin wannan tsari da ke cikin wannan na'urar da kuma irin yadda take gudanar da ayyukanta masu ban mamaki, ba zai zamanto babban shaida da ke tabbatar da irin kwakwalwa da kuma ilimin da wanda ya samar da ita yake da su ba?

To daga nan za mu iya samun wani dalili na gaba daya sannan wanda kuma kowa zai iya fahimtarsa kan cewa: wajibi ne irin wannan tsari ya kasance ne daga wajen wani masani kuma mai karfi da iko, sannan kuma babu yadda za a yi tushen irin wadannan ababe masu ban mamaki ya zamanto haka kawai ya samar da kansa, don kuwa kowane abu yana da nasa tushen da ya dace da shi da kuma alamun da suke tabbatar da shi.

Kamar yadda lagawu ne a yi tunanin cewa ruwan sanyi zai iya zama tushen konewar wani abu, haka nan lagawu ne a yi tunanin cewa za a iya samun wani tsararren tsari haka kawai bisa arashi, ba tare da akwai wani da ya samar da shi ba. Alkur'ani mai girma yana nuni da wannan lamarin cikin fadinsa:

(أَمْ خُلِقُوا مِنْ غَيْرِ شَيْءٍ أَمْ هُمُ الْخَالِقُونَ)

"Shin, an halitta su ne ba daga kome ba, ko kuwa su ne masu yin halitta? (Suratud Dur 52:35).

A saboda haka kowane abu da ka gani musamman abu mai muhimmanci da kuma kima yana da wasu tushe da ginshiki da ya ginu a kansa. Addinin Musulunci, a matsayinsa na addinin da ya zo don ya 'yantar da bil'adama daga duhun zalunci zuwa ga haske na shiriya bisa irin tsare-tsare da hukumce-hukumcen da ya ke da su, ya ginu ne bisa kan wasu ginshikai ko kuma shika-shika guda biyar da wajibi ne kowane mumini ya sansu sannan kuma yayi imani da su.

Su ne kuwa:

 

Na Farko: Tauhidi:

 

Akwai kuskure cikin tunanin da wasu suke yin a na tunanin cewa Allah Madaukakin Sarki ya samar da wannan duniya sannan kuma ya bar ta haka nan kawai ba tare da damuwa da ita ba. A'a, duk wani yunkuri na wannan duniyar da kuma ci gaba da samuwarta suna karkashin iko da kuma mashi'a ta Ubangiji ne. Babu wani abin da samuwarsa mai yiyuwa ne da ci gaba da wanzuwarsa zai kasance ba tare da izini da irada ta Ubangiji ba. A saboda haka Allah Madaukakin Sarki shi ne mai samarwa da kuma ci gaba da dawwamar da abubuwan da ya samar bugu da kari kuma kan sa ido kansu.

A saboda haka mutumin da ya yi imani da girma da daukakar Allah Mahalicci sannan kuma ya tabbatar da wannan imani cikin zuciyarsa wacce take cike da kaunar Ubangiji Madaukakin Sarki, to kuwa ba zai taba jin kadaitaka da jin cewa an yi watsi da shi ba, face dai hasken Ubangiji zai ci gaba da haskaka zuciyarsa da kuma bayyanar da shi cikin dukkanin bangarori na rayuwarsa. A fili yake cewa irin wannan mutumin da ya yi imani da Allah Madaukakin Sarki zai sami kansa cikin farin ciki da kuma shaukin rayuwa wacce take cike da daukaka da kuma kamala.

Hankali dai yana tabbatar da cewa wajibi ne Allah Madaukakin Sarki ya zamanto shi kadai, ba tare da wani abokin tarayya ba wajen gudanar da wannan duniyar don ta tafi yadda ya kamata ba tare an ta samun karo da juna ba, kamar yadda Allah Madaukakin Sarki ya ke fadi cikin Suratul Anbiya 21: 22 cewa:

( لَوْ كَانَ فِيهِمَا آلِهَةٌ إِلَّا اللَّهُ لَفَسَدَتَا)

"Da wadansu abubuwan bautawa sun kasance a cikinsu (sama da kasa) face Allah, hakika, da su biyun sun baci ".

A hakikanin gaskiya Tauhidi (kadaita Allah) a ma'anarsa ta hakika yana tarbiyya da kuma shiryar da mutum 'yantacce mai ingantaccen tunani da kwanciyar hankali ne, sannan kuma ba zai bar shi ya fada cikin damuwa da tsaka mai wuya, bata da sabani da bautar wani ba. Haka nan Tauhidi ya kan ba wa mutum 'yanci da daukaka da kuma karama, sannan kuma ya taimaka masa wajen tabbatar da adalci na zamantakewa da kuma daukaka.

Daga nan za mu iya fahimtar sirrin da ke cikin fadin Manzon Allah (s.a.w.a) cewa: "Ku ce La'ilaha Illallah, ku sami babbar rabo".

 

Na Biyu: Adalci:

 

Kamar yadda muka fahimci cewa Allah Madaukakin Sarki Shi ne Mahalicci Mai karfi da daukaka, ya arzurta bayinsa da sauran halittunSa da ni'imomi masu yawa da kuma tausayawa maras iyaka, sannan kuma shi kadai Yake, ba shi da abokin tarayya, babu wani Ubangiji in ba shi ba, ta haka ne ya ke tabbatar da adalcinsa a kan dukkanin halittu. A saboda haka ba ya bukatar ya yi zalunci – tsarki ya tabbata a gare shi daga aikata hakan – don kuwa babu wanda ya ke bukatar yin zalunci in ba mutum mai rauni ba.

Zalunci dai sakamako ne na jahilci da rauni da gasa da tsoro da rashi da kuma gazawa, Allah kuwa ya tsarkaka daga dukkanin  wadannan abubuwa. Allah Madaukakin Sarki, Masani ne sannan kuma Mai Karfi ta kowace fuska, da ba ya bukatar wani mutum ko wani abu ballantana ma ya ji tsoron cewa zai kubuce masa.

Irin bambance-bambancen da ake gani tsakanin 'yan al'umma guda ko kuma al'ummu daban-daban, ba wani abu ba ne face sai don a sami damar gudanar da rayuwa a bisa tafarkinta da aka shimfida ta a kai, don biyan bukatar bil'adama. Allah Madaukakin Sarki yana fadin cewa:

(وَرَفَعَ بَعْضَكُمْ فَوْقَ بَعْضٍ دَرَجَاتٍ لِّيَبْلُوَكُمْ فِي مَا آتَاكُم)

"Kuma Shi ne Wanda Ya sanya ku masu maye wa juna ga kasa. Kuma Ya daukaka sashenku bisa ga sashe da darajoji: domin ya jarraba ku, a cikin abin da ya ba ku" (Suratul An'am 6:165).

A saboda haka ya rage wa mutum ya fahimci hanyar gaskiya wacce za ta kai shi zuwa ga kamala a dukkanin bangarori na rayuwarsa, don ya rayu kamar yadda Allah Madaukakin Sarki ya so ya rayu cikin mutumci da ni'ima da alherori sannan kuma cikin mutumci a yayin mu'amalarsa da sauran bil'adama cikin gaskiya da kuma girmama juna, da kuma adalci da daidaito, da tsarkin zuciya da yafuwa, da dai sauran siffofi na alheri. Allah Madaukakin Sarki yana cewa:

(إِنَّ اللهَ يَأْمُرُ بِالْعَدْلِ وَالإِحْسَانِ)

"Lalle Allah na yin umurni da adalci da kyautatawa" (Suratun Nahl 16:90).

Shin yayi daidai da hankali da kuma hikima a ce Allah Madaukakin Sarki ya umurci bayinsa da aikata adalci, amma shi kuma ya nesanci hakan? Tsarki ya tabbata a gare shi daga abin da suke siffantawa.

 

Na Uku: Annabci:

 

Annabawa da Manzanni (amincin Allah ya tabbata a gare su) mutane ne, sai dai kawai sun bambanta da sauran mutane ne saboda irin karfi na zati da kuma kyawawan siffofi na kamala da suke da su sama da sauran mutane irin su kyakkyawar tarbiyya da suka samu, kyawawan halaye, riko da gaskiya da kuma aiwatar da adalci, amana da gaskiya da tsarkin zuciya da kaunar alheri ga dukkanin bil'adama da sauransu.

Saboda irin wadannan siffofi da suke da su ne suka zamanto sun dace da daukar wannan nauyi mai girma na jagorantar bil'adama zuwa ga alheri da kuma abubuwa masu kyau a gare su, sannan da kuma shiryar da su zuwa ga tafarkin gaskiya da kuma aiwatar da umurnin Allah da kuma nesantar abubuwan da ya hana, don ya tseratar da su daga sharrin duniya da azabar lahira.

A saboda haka ne ya zamanto wajibi a zabi Annabawa da Manzanni (a.s) don su dauki wannan nauyi mai muhimmanci da kuma hatsarin gaske, wanda shi ne jagoranci da ke cike da hikima da Allah Madaukakin Sarki ya tsara shi da kuma shata iyakokinsa.

Hisham bn Hakam yana fadin cewa Imam Sadik (a.s) ya gaya wa wani Zindiki da ya tambaye shi cewa: Ta ya ya zan tabbatar da Annabawa da Manzanni? Sai ya ce masa: "A lokacin da muka tabbatar da cewa muna da Mahalicci, Mai sana'antawa sannan kuma Madaukaki a kanmu da kuma dukkanin abubuwan da Ya halitta, sannan kuma wannan Mahaliccin ya kasance mai hikima kuma Madaukaki…..(Tun daga lokacin) Ya  tabbata cewa yana da jakadu cikin halittunSa, suna bayaninsa ga bayi da halittunsa, suna shiryar da su zuwa ga abubuwan amfaninsu da abin da aikata shi zai tabbatar da wanzuwarsu sannan kin aikatawa kuma zai kawar da su. Daga nan kuma aka tabbatar da masu umurni da hani daga wajen Mai hikima Masani a cikin halittunsa sannan kuma masu bayanin abin da ya ke so da abubuwan da ba ya so, su ne kuwa Annabawa (amicin Allah ya tabbata a gare su) sannan kuma zababbu cikin halittunsa, masu hikima da suka tarbiyantu da hikima, wadanda aka aiko su da ita, wadanda suka saba da mutane wajen halitta da tsari, sannan kuma wadanda Allah Mai hikima kuma Masani Ya tarbiyantar da su. Sannan kuma a cikin dukkanin lokuta da zamunna aka tabbatar da abubuwan da Annabawa da Manzanni (s.a.w.a) suka zo da su na daga dalilai da hujjoji, don kada kasar Allah ta zamanto ba tare da Hujja ba wanda zai zamanto yake da wani abin da ke tabbatar da gaskiyar abin da yake fadi da halalcin adalcinsa" (Usul al-Kafi: 168.)

Don karfafa wadannan Annabawa da Manzanni (a.s) da kuma da kuma tabbatar wa al'ummominsu cewa su din nan daga wajen Allah Madaukakin Sarki suke; don haka sai Allah Madaukakin Sarki ya ba wa Annabawa da Manzanninsa (a.s) mu'ujizozin da suka yi daidai da hankali da kuma yanayin mutanen zamaninsu, sannan kuma wadanda suka dara irin wadanda suka shahara a lokacin ta yadda za su zamanto gagarabadau. Daga cikin irin wadannan mu'ujizozin akwai mu'ujizar (ruwan) dufana na Annabi Nuhu (a.s); da kuma tsirar annabi Ibrahim (a.s) daga wutar da  aka sanya shi, da sandar Annabi Musa (a.s) da darewar teku a gare shi da al'ummarsa don su biya ta ciki don tsira daga Fir'auna da kuma nutsewar da ya yi a ciki; da kuma maganar Annabi Isa (a.s) a cikin zanin goyo da warkar da kutare da makafi da rayar da mamaci. Da mu'ujizar Alkur'ani mai girma da Allah Madaukakin Sarki ya kebance ta ga Annabinmu Muhammadu dan Abdullah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da Alayensa tsarkaka). An saukar da shi Alkur'ani ne a zamanin da larabawa suka kai koli na balaga wajen magana da fasaha ta zane. Sai Manzo (s.a.w.a) ya zo da Alkur'ani mai girma da ke cike da fasaha da tsarin jumloli da suka dara na masana da masu iya magana da mawaka da masu bayani na wancan lokacin yayin da suka gaza hatta zuwa da ko da aya guda ne makamanciyar wacce take cikin Alkur'ani.

Alkur'ani mai girma ya kalubalance su cikin fadinSa Madaukakin Sarki cewa:

(وَإِن كُنتُمْ فِي رَيْبٍ مِّمَّا نَزَّلْنَا عَلَى عَبْدِنَا فَأْتُواْ بِسُورَةٍ مِّن مِّثْلِهِ وَادْعُواْ شُهَدَاءكُم مِّن دُونِ اللهِ إِنْ كُنْتُمْ صَادِقِينَ)

"Kuma idan kun kasance a cikin shakka daga abin da Muka sassaukar ga BawanMu, to, ku zo da Sura guda daga cikin misalinsa (Alkur'ani). Kuma ku kirawo shaidunku, baicin Allah, idan kun kasance masu gaskiya" (Suratul Bakara 2:23).

Da kuma fadinsa cewa:

(قُل لَّئِنِ اجْتَمَعَتِ الإِنسُ وَالْجِنُّ عَلَى أَن يَأْتُواْ بِمِثْلِ هَـذَا الْقُرْآنِ لاَ يَأْتُونَ بِمِثْلِهِ وَلَوْ كَانَ بَعْضُهُمْ لِبَعْضٍ ظَهِيرًا)

"Ka ce, 'Lalle ne idan mutane da aljannu sun taru a kan su zo da misalin wannan Alkur'anin, ba za su zo da misalinsa ba, kuma ko da sashinsu ya kasance mataimaki ga sashi" (Suratul Isra' 17:88).

Hakan kuwa a daidai lokacin da masu fasaha da kwarewa wajen magana na wancan zamanin sun yi dukkanin wani kulli da za su iya wajen ganin sun yi galaba a kan wannan kalubalen, sai dai sun gaza. Hakan kuwa sakamakon mashi’a ta Ubangiji da kuma iradarsa, karfi da girmansa, hikima da adalcinsa. A saboda haka Allah Madaukakin Sarki cikin rahama da hikimarsa ne ya zabi Annabawa da Manzanni (a.s) don shiryar da bil’adama zuwa ga madaidaicin tafarki, ta hanyar irin wannan jagoranci da kuma shiryarwarsu da kuma jan kunnensu daga riko da tafarkin bata da kauce wa hanya.

Haka nan kuma don su sami damar shiryar da 'yan’adam don su sami matsayi na daukaka da karama da kuma kamala ta dan’adam da kuma kyawawan siffofi, don haka Allah Madaukakin Sarki ya tsarkake Annabawa da Manzanninsa (amincin Allah ya tabbata a gare su) daga dukkanin zunubai ko sabo, ko kuskure da mantuwa.

A takaice dai Allah Madaukakin Sarki Ya sanya su suka zamanto ma’asumai tsarkaka, don su sami damar jagorantar mutane zuwa ga kamala a dukkanin bangarori, da kuma yin biyayya da kuma da’a da mika wuya ga umurnin Allah Madaukakin Sarki da kuma haninSa.

Haka nan kuma su wadannan Annabawa da Manzanni (a.s) sun kasance masana wadanda iliminsu ya kasance ne daga wajen Allah Madaukakin Sarki, sannan kuma suna da masaniya cikakkiya dangane da ni’imomin lahira da kuma azabobinta, sannan kuma irin masaniyar da suke da ita dangane da mummunan sakamako da mai sabon Allah zai fuskanta a wancan duniyar hakan yana daga cikin manyan abubuwan da suke kare su daga aikata sabon Allah.

Allah Madaukakin Sarki yana fadin cewa:

(وَاذْكُرْ عِبَادَنَا إبْرَاهِيمَ وَإِسْحَقَ وَيَعْقُوبَ أُوْلِي الْأَيْدِي وَالْأَبْصَارِ * إِنَّا أَخْلَصْنَاهُم بِخَالِصَةٍ ذِكْرَى الدَّارِ * وَإِنَّهُمْ عِندَنَا لَمِنَ الْمُصْطَفَيْنَ الْأَخْيَارِ)

“Kuma ka ambaci bayinMu: Ibrahim da Ishaka da Ya’akub, ma’abota karfin (daukar umurninMu) da basira. Lalle Mu, Mun kebance su game da wata tsattsarkar aba: hukunce-hukuncen gidanduniya (mai tunatar da su Lahira). Kuma lalle su a wurinMu, tabbas, suna daga zababbu, mafifita” (Suratu Sad 38:45-47).

 

Na Hudu: Imamanci:

 

Wajibi ne ya zamanto al’ummar musulmi suna da wani jagora mai hikima, tsarkakakke wanda kuma ya dace, wanda zai maye gurbin Annabi (s.a.w.a) wajen gudanar da lamurran al’umma don kada a sami gibi ko kuma rugujewar wannan al’umma mai girma, sannan kuma wannan kokari da Manzon Allah (s.a.w.a) ya yi na kafa wannan al’umma ya tafi haka nan kawai.

 ‘Yan Shi’a sun yi imani da cewa rahamar Allah dai tana da fadin gaske, hikimarsa kuwa ta kai matsayi na koli sannan kuma tausayin da ya ke yi wa bayinsa ta wajabta masa rashin barin bayinsa haka kawai ba tare da wani jagora ma'abocin hikima, ma'asumi sannan kuma mai ilimi ba, lamarin da zai lamunce da kuma kare shi daga kauce wa hanya ta kowace fuska cikin maganganu da ayyukansa, don ya zamanto misali na gaskiya sannan kuma abin zabi daga wajen Allah Madaukakin Sarki. Haka nan kuma ya zamanto misali na kamalar dan'adam, don ya sami damar jagorancin wannan al'umma da shiryar da ita zuwa ga tudun na tsira.

Haka nan kuma hikimar Allah Madaukakin Sarki ta wajabta Ya zabi wasu mutane abin kwatance wadanda za su tsaya da kuma gudanar da lamurran addininsa don kiyaye wannan sako mai tsarki. Hakan kuwa shi ne abin da ya faru ta hanyar ayyanawa da tabbatar da nassi a kan wasu zababbu daga cikin bayin nasa.

Yayin da aka saukar da ayar (يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُواْ أَطِيعُواْ اللّهَ وَأَطِيعُواْ الرَّسُولَ وَأُوْلِي الأَمْرِ مِنكُمْ) "Ya ku wadanda suka yi imani! Ku yi da'a ga Allah, kuma ku yi da'a ga ManzonSa, da ma'abota al'amari daga cikinku" (Suratun Nisa' 4:59), sahabin nan mai girma Jabir bn Abdullah al-Ansari (yardar Allah ta tabbata a gare shi) yana fadin cewa: Na ce Ya Manzon Allah: Lalle mun san Allah da ManzonSa, to amma su wane ne wadannan ma'abota al'amurran wadanda Allah ya hada da'arsa da da'arsu?. Sai Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: "Su ne halifofina kuma shugabannin musulmi a bayana. Na farkonsu shi ne Aliyu bn Abi Talib sai Hasan da Husain, sai Aliyu bn Husain, sai Muhammad bn Ali wanda aka fi sani da Bakir, za ka hadu da shi Ya Jabir, idan ka hadu da shi, ka isar min da gaisuwa ta a gare shi, sai kuma Al-Sadik Ja'afar bn Muhammad, sai Musa bn Ja'afar, sai Aliyu bn Musa, sai Muhammad bn Ali, sai Aliyu bn Muhammad, sai Hasan bn Ali, sai kuma mai sunana da kuma alkunyata, Hujjar Allah a bayan kasarsa, sannan kuma wanzajjensa a cikin bayinsa, (Muhammad) Dan Hasan bn Ali"([i]).

Har ya zuwa yanzu musulmi suna ci gaba da zama cikin wannan kulawa ta Ubangiji, ba su rasa irin wannan jagora ba sakamakon ci gaba da kasantuwar Imami na goma sha biyu, wato Imam Mahdi al-Muntazar (Allah Ya gaggauta bayyanarsa). Yana raye sai dai ya faku daga idanuwan mutane, har lokacin da Allah Madaukakin Sarki zai ba shi umurnin bayyana don ya cika duniya da adalci da haske bayan ta cika da zalunci da duhu. Akwai riwayoyi da yawan gaske daga bangarori Shi'a da Sunna da suke magana kansa.

 

Na Biyar: Tashin Alkiyama:

 

Dukkanin saukakkun addinai sun tabbatar da wata hakika wacce ita ce cewa mutuwa ba ita ce karshen mutum ba, face dai bayan mutuwar mutum ya kan tashi daga wannan duniyar ce zuwa ga wata duniyar ta daban, inda za a yi masa hisabi kan ayyukan da ya aikata, a ba shi ladar kyawawan cikinsu da kuma yi masa ukuba kan munanan.

Dukkanin Annabawan Allah da Manzanninsa (a.s) sun sanar da mabiyansu cewa wannan duniyar da dukkanin tsari da yanayinta, ba a samar da ita haka kawai don wargi  ba. Sannan da kuma cewa dukkanin abubuwan da suke gudana a cikinta na daga ayyuka da mu'amaloli, za a baje su a teburin hisabi bayan an yi kaura daga wannan duniyar zuwa wancan duniyar.

A saboda haka ne suka kasance suka shirya kansu da kuma mabiyansu zuwa ga wannan makomar da babu makawa cikinta. Ayoyin Alkur'ani mai girma da yawa sun yi magana kan tabbacin ranar tashin Kiyama da kuma hisabi, lada da ukuba, Aljanna da kuma wuta.

Daga cikinsu akwai fadinSa Madaukakin Sarki cewa:

(وَعَدَ اللهُ الْمُؤْمِنِينَ وَالْمُؤْمِنَاتِ جَنَّاتٍ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا وَمَسَاكِنَ طَيِّبَةً فِي جَنَّاتِ عَدْنٍ وَرِضْوَانٌ مِّنَ اللهِ أَكْبَرُ ذَلِكَ هُوَ الْفَوْزُ الْعَظِيم)

"Kuma Allah Ya yi wa'adi ga muminai maza da muminai mata da gidajen Aljanna koramu suna gudana daga karkashinsu, suna madawwama a cikinsu, da wuraren zama masu dadi a cikin gidajen Aljannar. Kuma yarda daga Allah ce mafi girma. Wancan shi ne babban rabo, mai girma" (Suratut Tauba 9:72).

Da fadinsa Madaukaki cewa:

(فَادْخُلُواْ أَبْوَابَ جَهَنَّمَ خَالِدِينَ فِيهَا فَلَبِئْسَ مَثْوَى الْمُتَكَبِّرِينَ)

"Sai ku shiga kofofin Jahannama, kuna madawwama a cikinta. Sa'an nan tir da mazaunin masu girman kai" (Suratun Nahl 16:29).

Haka nan da kuma fadinsa Madaukakin Sarki:

(إِنَّ اللهَ يُدْخِلُ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ جَنَّاتٍ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ وَالَّذِينَ كَفَرُوا يَتَمَتَّعُونَ وَيَأْكُلُونَ كَمَا تَأْكُلُ الْأَنْعَامُ وَالنَّارُ مَثْوًى لَّهُمْ)

"Lalle ne, Allah na shigar da wadanda suka yi imani kuma suka aikata ayyukan kwarai a gidajen Aljanna, kogunan ruwa na gudana daga karkashinsu, kuma wadanda suka kafirta, suna jin dan dadi (a duniya) kuma suna ci, kamar yadda dabbobi ke ci, kuma wuta ita ce mazauni a gare su" (Suratu Muhammad 47:12)

 


([i]). Muntakhabul Athar, shafi na 101.