A+ R A-
22 February 2024

Ghadir, Makomar Al'umma Bayan Ma'aiki (s.a.w.a)

Ghadir, Makomar Al'umma Bayan Ma'aiki (s.a.w.a):
Daga:
Muhammad Awwal Bauchi
IRIB-Tehran - I.R.of Iran
This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.

________________________

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

A matsayinmu na musulmi, mun yi imani cewa addinin Musulunci addini ne da aka sauko da shi ga dukkan bil'Adama sannan kuma shari'arsa ta kumshi dukkan abin da dan'Adam yake bukata a rayuwarsa ta yau da kullum. Kamar yadda kuma muka yi imani da cewa gudanar da wannan shari'a da jagorancin al'umma yana hannun wanda yazo da sakon ne wato Manzon Allah (s.a.w.a) matukar dai yana raye, wannan lamari ne da dukkan musulmi suka hadu a kansa. Abin tambaya da kuma kace nacen shi ne yadda lamarin zai kasance a bayansa. Mabiya Ahlulbaiti (a.s) sun yi amanna da cewa ayyana wanda zai gaji Ma'aiki (s.a.w.a) wajen gudanar da wannan aiki nasa ba yana hannun kowa ba ne face Allah da ManzonSa (s.a.w.a), wato a takaice dai al'umma ba su da bakin magana cikin wannan lamari kamar yadda ba su da bakin magana wajen zaban wanda zai zo da sakon Allah Madaukakin Sarki wato Annabi "Allah Shi ne Mafi sanin inda Zai ajiye ManzancinSa(1)". Don haka imamanci ko kuma halifanci (kamar yadda aka fi saninsa) a matsayinsa na ci gaban aikin annabtaka, shi ma Allah da ManzonSa ne suka san inda za su ajiye shi. Ahlulbaiti (a.s) da mabiyansu sun yi amanna da cewa halifanci ko kuma jagorancin al'umman musulmi bayan Ma'aiki wani matsayi ne mai girman gaske don haka babu yadda za a yi Allah da ManzonSa su bar shi a hannun mutane haka kawai musamman idan aka yi la'akari da yanayin siyasa da zamantakewa da Musulunci yake fuskanta a lokacin, don haka suka ce Allah da ManzonSa ne kawai za su zabi wanda zai rike wannan matsayi. Abin tambaya a nan shi ne to wane ne wanda aka zaba din? Yaushe da kuma a ina aka yi zaben? Kuma ya ya aka gudanar da shi?

Wadannan tambayoyi su ne za mu yi kokarin amsa su a dan wannan rubutu muna masu neman taimakon Ubangiji Madaukakin Sarki da kuma kamun kafa da neman izinin Imamin zamaninmu al-Mahdi (a.s).

Dangane da tambayar farko dai mu mun yi imani da cewa, kamar yadda masu iya magana suke cewa wai tun ranar gini ranar zane, tun farko-farkon wannan sako na Musulunci Allah da ManzonSa suka zabi mafi daukakan wannan al'umma bayan Manzo (s.a.w.a) a matsayin wanda zai gaje shi da kuma ci gaba da jagorancin al'umma bayansa, kuma sun ci gaba da bayyana hakan a lokuta daban-daban har lokacin karshe na rayuwar Ma'aiki. Wanda kuwa aka zaban shi ne Amirul Muminina Aliyu bn Abi Talib (a.s). Batun yaushe da kuma ina aka yi zaben kuwa, to kamar yadda muka ce ne an fara wannan zabe ne tun ranar da aka umarci Manzon Allah (s.a.w.a) da ya kirayi makusantansa zuwa ga Musulunci ranar da ake kiranta da Yaum al-Inzar, wato lokacin da Allah Madaukaki ya saukar da ayar: "Kuma ka yi gargadi ga danginka mafiya kusanci(2)", to amma da yake ba akan wannan batu muke son magana ba, mai son karin bayani yana iya komawa ga litattafan da suka yi magana kansa(3).

Wani wajen kuma da Manzo ya fi fitowa fili da ayyana Ali (a.s) a matsayin halifansa shi ne Ghadir Khum wato lokacin da yake dawowa daga hajjin ban kwana a ranar 18 ga watan Zul hajji shekara ta 10 bayan hijira. To wannan batu dai shi ne za mu yi magana a kansa da kuma ganin yadda ya kasance kamar yadda muka yi tambaya a kai a baya.

A hakikanin gaskiya ranar Ghadir tana a matsayin wata rana mai muhimmancin gaske ga tafarki da kuma ci gaban Musulunci saboda matsayin da take da shi na ranar da aka mika ci gaban jagorancin Musulunci a dukkan bangarori da kuma jagorancin al'ummar musulmi ga hannun wani mutum, wanda ba shi ne ya zo da sakon ba, duk kuwa da irin yanayi da barazanar da suke fuskantar al'umma daga ciki da waje, da kuma cewa a wannan rana ce Allah Ya cika ni'imarsa ga al'umma da kuma zaba musu Musulunci a matsayin addinin da ya yarda su bi. Hakan kuwa saboda a daidai wannan lokaci jagorancin Musulunci da musulmi bayan Ma'aiki yana bukatuwa da wani mutum da ke da irin siffofin da Manzo yake da su, saboda wasu dalilai, ciki kuwa har da cewa kusan dukkan lokacin da Manzo ya shafe a Makka da Madina lokaci ne da ke cike da matsaloli irin su tsangwama, yake-yake da sauran matsaloli na cikin gida, wanda hakan ya haifar da wasu tunace-tunace cikin zukatan sahabbai sannan kuma ba a iya cimma wasu daga cikin manufofin da ake son cimmawa ba, duk da cewa hakan yana nuni ne da gazawan su kansu al'umma ba wai addinin ko kuma wanda ya zo da shi ba. Don haka Musulunci yana bukatuwa da wani mutum tsayayye wanda zai ci gaba da shiryar da al'umma kamar yadda Manzo ya yi tun da dai a halin da ake ciki lokaci ya yi da zai koma ga Mahaliccinsa.

Hakikanin hadafinmu ba shi ne bayyana wa mai karatu kissar Ghadir da abubuwan da suka faru dalla-dalla ba ne, don kuwa na riga da na san mai karatu ya san wannan kissar, face dai babban hadafin shi ne fitar da wasu abubuwa muhimmai cikin wannan lamari da kuma bayyanar da wanda ya cancanci jama'a su koma gare shi bayan Ma'aiki (s.a.w.a), to amma don matashiya a gurguje ga yadda lamarin ya kasance:

Malaman tarihi da na tafsiri da ma na hadisi, yayin da suke magana kan wannan lamari da kuma abubuwan da suka faru sun bayyana cewa: A shekarar karshe ta rayuwarsa, Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kuduri aniyar zuwa aikin hajji, abin da daga karshe ake ce masa Hajjin Ban Kwana. Nan da nan labari ya yadu a duk fadin duniyar musulmi, al'amarin da ya sa da yawa daga cikinsu suka yiyo azamar kasancewa tare da Ma'aiki (s.a.w.a) cikin wannan aikin hajjin. An bayyana cewa adadin musulman da suka yi wannan aiki na hajjin ya kai dubu dari da ashirin.

Bayan gudanar da aikin hajjin, sai Ma'aiki (s.a.w.a.) da rundunarsa suka kamo hanyarsu ta dawowa, inda suka iso wani guri da ake ce ma Ghadir Khum a ranar 18 ga watan Zil Hajjin shekara ta goma bayan hijira. Shi wannan guri ya kasance wata mahada ce ta hanyoyin zuwa Madina, Iraki, Masar da kuma Yaman. A nan ne Ma'aiki (s.a.w.a.) ya yi ban kwana da sauran musulmi ya kama hanyarsa ta komowa gida (Madina) kana kuma sauran al'umma ma kowa ya kama hanyarsa. Jim kadan bayan ban kwana da kuma kama hanyar Ma'aiki (s.a.w.a.) zuwa Madina, sai ga Mala'ika Jibril (a.s.) da sako daga Allah zuwa ga ManzonSa, sakon kuwa shi ne ayar nan, wacce daga baya malamai suke kiranta da Ayatul Tabligh wato: " Ya kai Manzo ka isar da abin da aka saukar maka na daga Ubangijinka, idan baka aikata ba to ba ka isar da sakonSa ba, Allah Zai kare daga mutane. Lalle Allah ba Ya shiryar da mutanen da suke kafirai(4)". Nan take sai Ma'aiki (s.a.w.a.) ya yi umurnin da a tsaya sannnan wadanda suka wuce su komo wadanda kuma ba su riga da sun iso ba a jira su su iso.

Lokacin da kowa da kowa ya iso, sai Ma'aiki (s.a.w.a.) ya hau kan abin da aka tanadar masa don kowa da kowa ya gan shi, inda ya gabatar da dogon jawabi. To amma don takaitawa za mu tabo abin da yafi shafan wannan babi da muke magana akai ne. Don haka ga kadan daga cikin abin da ya faru kana kuma da abin da Ma'aiki (s.a.w.a.) din ya ce:

"Ya ku mutane….an kusan a kira ni kuma in amsa, kuma zan kasance abin tambaya haka nan ku ma, to me za ku ce?

Sai dukkansu suka amsa da cewa: "Za mu shaida cewa ka isar (da sako), kuma ka yi nasiha sannan kuma ka yi jihadi, Allah Ya saka maka da alherinSa".

Sai Manzo (s.a.w.a) ya ce: "Ashe ba ku shaida cewa babu wani abin bauta sai Allah ba, kuma Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa, kuma aljanna gaskiya ce sannan wuta gaskiya ce, kuma mutuwa gaskiya ce, kuma ranar kiyama tana zuwa babu kokwanto ga hakan, kuma Allah Zai tayar da wadanda suke kaburbura?.

Sai suka ce: "Lalle mun shaida".

Sai yace: "Ya ku mutane…wanene ya fi soyuwa ga muminai a kan kawunansu?".

Sai suka ce: "Allah da ManzonSa".

Daga nan sai ya daga muryarsa ya ce: "Hakika Allah ne Shugabana, ni kuma shugaban dukkan muminai, kuma ni ne nafi soyuwa gare su a kan kawukansu. To duk wanda na kasance shugabansa, to Aliyu shugabansa ne… duk wanda na kasance shugabansa, to Aliyu shugabansa ne....duk wanda na kasance shugabansa, to Aliyu shugabansa ne… (ya maimaita hakan har sau uku). Ya Allah Ka jibinci wanda ya jibince shi kuma Ka ki wanda ya ki shi, Ka taimaki wanda ya taimake shi ka wulakanta wanda ya nesance shi, Ka sanya gaskiya tare da shi a duk inda ya juya. Lalle wanda ya ke nan ya sanar da wanda ba ya nan".

Jim kadan da gama wannan jawabi na Manzon Allah (s.a.w.a), sai ga Mala'ika Jibril (a.s.) ya sauko da wata ayar daga Allah Ta'ala, wacce daga baya ake kira da Ayar Cikan Addini ita ce kuwa fadin Allah Madaukakin Sarki cewa: ( اليومَ أَكْملْتُ لكُم دينَكُم وأتْممْتُ عليكُم نعْمتي ورضِيتُ لكم الإسلامَ دينًا لَرَادُّكَ إِلَى مَعَادٍ ), (A yau na cika muku addininku, kuma na cika muku ni'imata sannan kuma na zaba muku (addinin) Musulunci a matasayin addini)

Daga nan sai Manzo (s.a.w.a) ya sauko jama'a suka zo suna taya Ali (a.s) murna da wannan matsayi da ya samu cikinsu kuwa har da halifa Abubakar da Ummaru.

A takaice dai wannan ita ce kissar Ghadir wacce ta kasance matsayar karshe da Manzon Allah (s.a.w.a) ya dauka don shiryar da al'ummarsa da kuma kare su daga rarrabuwa kan wanda zai gaje shi kamar yadda malaman hadisi da tafsiri suka tabbatar(5) , duk da cewa, abin bakin ciki, sun samu rarrabuwa da sabanin sakamakon watsin da suka yi da wannan umarni na Ma'aiki kamar yadda suka yi a ranar Uhud. To ko ba komai shi dai ya yi nasa aikin na ayyana musu Ali a matsayin jagoransu.

Idan muka dubi wannan zabi da Manzo (s.a.w.a) ya yi wa Ali za mu ga tamkar yana so ne:

 

  1. Ya jaddada wa musulmi cewa Musulunci (musamman a daidai wannan lokaci) yana bukatuwa da wani mutum ma'abucin ilmi sama da kowa, don kuwa jagoranci na bukatuwa da masaniya ta yadda za a iya bullo wa duk wani makirci da matsala gwagwardon yadda take bukata, wanda babu wanda yake da wannan siffa in ba Ali (a.s) ba.

  2. Ya jaddada cewa Ali na tare da gaskiya ta yadda babu yadda karya ko bata za ta iya kusantarsa, ta yadda idan ya motsa gaskiya za ta bi shi, idan ya tsaya za ta tsaya, duk abin da ya yi riko da shi gaskiya ne duk abin da ya yaka kuwa karya da bata ce, ba zai taba rabuwa da gaskiya ba kamar yadda gaskiya ba za ta rabu da shi ba. Manzo na cewa: "Ali na tare da gaskiya gaskiya kuma na tare da Ali".

  3. Yana so ya fahimtar da mutane cewa babu wani mutumin da yake gani ya cancanci wannan matsayi na jagoranci da ci gaba da isar da sako sai Ali (a.s).

  4. Yana so ne ya nuna wa mutane cewa Ali (a.s) ya mallaki duk wata siffa daga cikin siffofin da yake da su na jagoranci don haka jama'a su bi shi sau da kafa kamar yadda suke binsa. Don kuwa idan ba haka ba babu yadda za a yi Manzo ya mika masa wannan aiki mai muhimmancin gaske, kai sannan ma har Allah Madaukaki ya ce masa idan bai isar da wannan sako ba (bai mika masa ba) tamkar ma bai isar da sakon da aka aiko shi da shi ba ne, duk kuwa da mun yi imani cewar Manzo ya isar da sakon da aka aiko shi da shi, kuma Allah ba Ya shakku (idan har ya dace mu yi amfani da wannan kalma) kan Manzo, amma dai wannan ishara da ya yi wa ManzonSa tamkar wata shiryarwa ce gare shi da kuma bayyana masa cewa Ali ne kawai zai iya rike wannan aiki da ya yi, idan kuwa ba shi ba to duk wanda ya zo zai lalata ayyukan shekaru 23 da ya yi ne.

Halifancin Manzon Allah (s.a.w.a) dai ya bambanta da sauran halifanci ko kuma shugabanci, don kuwa lamarin ba wai shugabanci ba ne, face dai shiryarwa ce da kuma cimma manufofin Musulunci wadanda yanayi bai bar Manzo (s.a.w.a) ya isa gare su ba, don kamar yadda muka sani ne kafirai sun shagaltar da Manzon Allah (s.a.w.a) da yakukuwa ga kuma sauran matsaloli na daban, don haka a daidai wannan lokaci Musulunci na bukatuwa da wani mutum kamar Manzo da zai ci gaba da wannan aiki, babu wani kuma a lokacin da ya cika wadannan sharudda in ba Aliyu bn Abi Talib (a.s) ba. Muna iya fahimtar hakan ne kuwa idan muka yi la'akari da irin siffofin da Ali yake da su da babu wani mahalukin da ya mallake su (in kare cire Manzo) in ba shi ba. Ga kadan daga cikinsu:

 

  1. Ilmi: Ruwayoyi da tarihi sun tabbatar da cewa babu wani daga cikin sahabban Ma'aiki (s.a.w.a) da ya mallaki ilmin da Ali (a.s) ya mallaka. Don kuwa shi ne wanda Ma'aiki (s.a.w.a) ya ke cewa dangane da shi: "Ni ne birnin ilmi Aliyu kuma kofarsa(6)", sannan kuma a wani wajen shi da kansa yana cewa: "Lalle Manzo ya karantar da ni kofofi dubu na ilmi kowace kofa kuma tana bude wasu kofofi dubun(7)", da dai sauran hadisan da suka yi magana kan ilmin Ali (a.s) da aka kawo su cikin litattafa mai son karin bayani yana iya komawa gare su. A takaice kuma tarihi ya tabbatar mana da cewa manyan halifofin Musulunci lokacin shugabancinsu sukan koma ga Ali a duk lokacin da suka gagara magance wata matsala ta ilmi har ma an ruwaito halifa Ummaru yana cewa: Da ba don Ali ba da na halaka(8)" da kuma cewa: "Kada Allah Ya sanya ni cikin wata matsalar da Abul Hasan ba ya nan(9)" da dai sauransu.

  2. Jaruntaka: Jaruntaka dai daya ne daga cikin siffofin da wajibi ne kowani shugaba ya mallaka matukar dai yana son samun nasara cikin jagorancinsa. Don haka babu wani kokwanto ana iya cewa babu wani daga cikin sahabbai da ya mallaki jaruntakar da Ali ya mallaka. Tarihi ya tabbatar mana da irin gudummawar da Ali ya bayar a fagaren yaki wajen kare Manzo da kuma sakon da ya zo da shi, a daidai lokacin da wasu daga cikin sahabbai suke gudu daga fagen faman. Kowa dai ya san irin jaruntar da ya nuna a yakin Badar, Uhud, Hunain, Khandak da dai sauransu. Don karin bayani bari mu kawo kadan daga cikin abin da ya faru a yakin Khandak don ganin matsayin jaruntakarsa da kuma fifikon da ya ke da shi a kan sauran musulmi. Ga kadan daga cikin abin da malamai suka fadi dangane da yakin:

"Sakamakon irin nasarar da Kuraishawa suke samu a kokarin da suke yi na ganin bayan Musulunci ya sanya su neman dauki da hadin gwuiwan sauran al'ummomi masu adawa da Musuluncin ciki kuwa har da yahudawa….bayan da kafiran suka sami adadi mai yawan gaske na sojoji sai suka nufi garin Madina da nufin gamawa da Musulunci kowa ya huta. Lokacin da suka iso sai suka samu musulmai sun kewaye garin Madinan da rami a matsayin wata dabara ta kariya da kuma garkuwa daga makiya sakamakon shawarar da Salman al-Farisi, madaukakin sahabin nan na Manzon Allah (s.a.w.a) ya bayar. Sai dai kuma duk da hakan wasu daga cikin kafiran sun yi kokarin ganin sun haura wannan rami da shiga cikin rundunar musulmi.

Daga cikin wadanda suka sami nasarar tsallake wannan rami har da Amru bn Abdu Wud, wanda aka sanshi da jaruntaka da ba wa maza tsoro saboda irin karfin da yake da shi. Bayan da ya samu nasarar tsallake wannan rami, Amr bn Abdu Wud ya fito yana isgili wa musulmi da cewa waye daga cikinku yake son tafiya aljanna? Wato yana isgili wa musulmi ne da cewa waye ya shirya ya fito ya fuskance shi shi kuwa ya kashe shi ya tura shi aljanna kamar yadda musulmin suka imani da cewa duk wanda aka kashe shi wajen yaki zai shiga aljanna wato zai yi shahada. Jin haka sai Manzo (s.a.w.a) ya kalli sahabbansa ya ce musu "waye zai fuskanci Amru in lamunce masa aljanna" babu wani da motsa in ba Aliyu bn Abi Talib ba wanda yace ni ne zan fuskance shi ya Manzon Allah, amma dai Manzo ya ce masa ya zauna, ya sake gabatar da wannan bukata ga sahabbai amma dai babu wani da ya yarda ya fito sai Ali, a wannan karon ma Manzo ya ce masa ya zauna, haka dai aka yi har sau uku, amma kowa yana jin tsoron fitowa ya fuskanci Amru, babu wanda ya yarda ya fito in ba Imam Ali (a.s) ba wanda daman ya saba fitowa don kare Musulunci da Manzon Allah (s.a.w.a) don haka ne ma aka saukar da ayar: (وَمِنَ النَّاسِ مَن يَشْرِي نَفْسَهُ ابْتِغَاء مَرْضَاتِ اللّهِ ), (Kuma akwai daga mutane wanda yake sayar da ransa, domin neman yardar Allah(10)) lokacin da ya kwanta a kan gadon Manzo lokacin hijira don tseratar da ran Ma'aiki daga barazanar kafirai. Hakan dai ya tabbatar mana da cewa babu abin da Ali yake gani kana kuma babu abin da yake so face sadaukar da kansa da dukkan abin da ya mallaka wajen kare Musulunci da Manzo da a lokacin yake cikin hatsari mai tsananin gaske. Don haka ba ya wani kokwanto ko taraddudi a duk lokacin da Allah da ManzonSa suke bukaci wani abu daga wajensa kamar yadda daman haka ake so musulmin kwarai ya kasance don ( وَمَا كَانَ لِمُؤْمِنٍ وَلَا مُؤْمِنَةٍ إِذَا قَضَى اللَّهُ وَرَسُولُهُ أَمْرًا أَن يَكُونَ لَهُمُ الْخِيَرَةُ مِنْ أَمْرِهِمْ, (Kuma ba ya halalta ga mumini ko kuma mumina, a lokacin da Allah da ManzonSa suka hukumta wani al'amari, su kasance suna da wani zabi cikin al'amarinsu(11)) , don haka ne Ali sabanin sauran mutanen da suke wajen bai tsaya wani bata lokaci ba ya mika kansa lokacin da Allah da ManzonSa suka bukace shi da ya sadaukar da shi dominsu.

Daga nan sai Manzo ya ce masa: Ya Ali Amru ne fa, shi kuwa sai ya mayar masa da amsa cikin ladabi da kauna Ya Rasulallah ai ni kuma Aliyu ne fa, kamar yana so ya ce wa Manzo Ya Ma'aiki ka riga da ka san matsayina da irin kaunar da nake maka da kuma sadaukarwa don kare wannan addini, don haka ka barni kawai in fuskance shi tun da dai sauran mutane sun gaza. Don haka sai Manzo ya yi masa umarni da fita ya sanya masa garkuwarsa da kuma ba shi takobinsa Zul Fikar ya kuma daura masa rawaninsa, ya ce bisimillah, daga nan kuma sai ya daga hannu sama don addu'a yana cewa: "Ya Allah Ka kare shi daga gaba da bayansa, daga dama da hagunsu, daga sama da kasansa", wasu ruwayoyin ma suka ce ya ci gaba da wannan addu'a yana mai cewa: "Ya Allah Ka raba ni da Ubaidah ranar Badar, ka raba ni da Hamza ranar Uhud, don haka yau kan ka kare min Aliyu. Ya Allah! Kada Ka bar ni ni kadai alhali kuwa Kai ne Mafi alherin masu gado(12)". Daga nan sai ya fadi mashahuriyar kalman nan tasa ta cewa: "A yau imani ya fito gaba dayansa don fuskantar shirka dukkansa".

A daidai wannan lokaci kuwa Amru sai tsumuwa yake yi yana ta kirari don ya riga da ya ga sahabban Ma'aiki duk sun tsorata babu wanda yake son ya fito har ma ya ci gaba da ce musu:

( ولقد بُححتُ من النداءِ بجمعكم هل من مبارز؟ تَفِىء إلى أَمْر الله ) <

Wato ina kalubalantarku shin akwai wani mai fitowa? Sai Ali ya fito ya fuskance shi yana rera wannan waka:

لا تَعجَلَنَّ فقَدْ أَتاكَ مُجيبُ صوتِكَ غيرَ عاجِز

"Gaggawan me kake yi hakika ka samu Mai amsa maka maras gazawa"

Daga nan sai aka fara musanyan kalmomi tsakaninsu, yadda Ali (a.s) yake mayar da martani ya fusata Amru don haka ya nufo shi da nufin zai gama da shi amma ina, bayan wani lokaci Imam Ali (a.s) ya sa takobi ya sare shi ya fadi kasa mushe. Ganin haka sai Ali ya yi kabbara sauran musulmi kuwa suka amsa masa wato alamar kenan an samu nasara. Wannan kisan gilla da Ali ya yi wa Amru ya raunana zukatan kafirai da kuma kara karfafa zukatan musulmi wadanda suke cikin razana da fargaba, don haka ne ma aka ruwaito Manzon Allah (s.a.w.a) yana cewa: "Saran da Imam Ali ya yi wa Amru ranar Khandak ya fi dukkan ayyukan mutane da aljannu". A takaice dai wannan shi ne abin da ya faru a yakin Khandak da ke nuna mana kadan daga cikin jaruntakar Ali (a.s).

Akwai abubuwa da yawa da Imam Ali (a.s) yake da su da suka sanya ya cancanci halifanci da jagorantar al'umma sama da kowa daga cikin sahabbai, lokaci ba zai bari mu kawo su a nan ba sai ana iya komawa ga rayuwarsa don ganinsu.

Idan muka koma ga batun Ghadir da ayoyin da suka sauka a lokacin musamman ayar nan da ake kira Ayatul Tabligh (Ma'ida 5:67) za mu ga cewa lalle akwai wani muhimmin abu da ake son fitarwa na gaggawa, don kuwa yadda aka yi magana da Manzo a cikinta ya saba da yadda aka saba masa magana. Misali kalmomi irin su "idan baka aikata ba" da kuma " Allah Zai kare daga mutane", wanda suna nuni a fili da cewa lalle akwai wani abin da zai faru idan Manzo ya isar da wannan sako, amma dai duk da haka Allah din zai kare shi daga sharri wadanda suke son nufinsa da sharri daga cikin al'ummarsa. Ayar tana kokarin nuna cewa ne bayan Manzo (s.a.w.a) babu wani manzo ko addini da zai zo nan gaba saboda an riga da an zabi Musulunci a matsayin addini, sai dai duk da haka akwai wani abin da ya rage a isar da shi wanda idan ba a isar da shi ba tamkar ba a isar da sakon ba ne gaba daya, wannan abu kuma ana bukatuwa da a bayyana shi ne a fili a gaban kusan dukkan musulmi ko kuma alal akalla wakilansu don kada daga baya wasu su yi kokarin haifar da rudani don biyan bukatun kansu da kansu da kuma son zuciyarsu. Wannan abu kuwa shi ne lamarin halifancin Manzo bayansa don ci gaba da shiryar da mutane da jagorantarsu zuwa ga tafarkin da manzo din ya sanya su a kai, saboda hakan yana da muhimmanci ya sake bayyana shi kusan lokacin barinsa duniya (duk da cewa tun farkon sakon ma ya bayyana shi) saboda ya yanke hujja ga wadanda suke da tsatsa cikin zukatansu, wadanda ya riga da ya san wannan zabi da Allah da ManzonSa suka yi ba zai yi musu dadi ba.

Allah Madaukakin Sarki dai ya riga da ya yi kyakkyawar shaida wa ManzonSa cewa ba ya fadin wani abu cikin son rai duk abin da ya fadi wahayi ne daga Ubangiji, kamar yadda ya fadi hakan cikin Surat al-Najm, sai dai duk da wannan shaida sai da wasu suka nuna shakku kan abin da ya bayyana a Ghadir. Tawaye da kin amincewa da hukumcin da Annabawan Allah suka zartar daga bangaren al'ummarsu dai ba abu ne bako ba, musamman ma abin da ya shafi zaban wanda zai gaje su. Misali Alkur'ani mai girma ya gaya mana labarin Annabi Musa (a.s) lokacin da ya roki Ubangiji da Ya sanya Harun (a.s) ya kasance halifansa saboda zaban halifa ba lamari ne da yake hannu al'umma ba, sai dai bayan da Allah Ya amince da wannan addu'a shaidan ya rudi wasu daga cikin al'ummar Musa inda suka yi watsi da wannan halifa suka koma bautan dan maraki. Kamar yadda kuma Alkur'anin ya sanar da mu yadda al'ummar Isa (a.s) suka yi gangamin fuskantarsa duk kuwa da ya zo musu da abin da zai tabbatar musu da sa'adar duniya da ta lahira ne. Dukkan wadannan abubuwa su na nuna mana yadda al'ummomi suke yin watsi da umarnin Annabawansu idan har abin da suka zo da shi ya saba wa abin da suke so, dukkan wadannan suna tabbatar mana da abin da wannan aya take bayani ne na kare Manzo daga sharrin masu sharri.

Don haka bayan samun wannan lamuni sannan kuma da da'a wa umarnin Allah Madaukakin Sarki ya sanya Manzo (s.a.w.a) bayan ya tara dukkan al'umma ya bayyana musu wannan jumla ta "Man Kuntu Mawlahu, Fa Aliyun Mawlahu", wanda hakan ya kasance sanarwa ta fili kan abin da tun da jimawa ya sha fadinsa wato matsayin da Amirul Muminina (a.s) yake da shi da kuma kasancewa wanda zai gaje shi bayan ya koma ga Mahaliccinsa.

Don haka ne muna iya cewa ranar Ghadir rana ce ta hada silsilar hukumcin Ubangiji (wilaya) tun daga lokacin da aka sanar da Adamu (a.s) a matsayin halifan Allah a bayan kasa har zuwa lokacin bayyanar Sahib al-Zaman Imam al-Mahdi (a.s) don tabbatar da hukumar adalci, tabbatar da hukumce-hukumcen Allah da ikonSa cikin al'umma, wanda kuma idan da mutane sun yi riko da shi da ba su fada cikin duhun Sakifa da bala'oin da suka dinga samun al'umma ba. Don gujewa wa fadawa cikin wannan matsala ne ya sanya Allah Ya aiko da Jibrilu (a.s) da wannan sako na tabbatar da wilayan Amirul Muminina (a.s) a kan al'umma da kuma cika addini da hakan.

Abin bakin cikin dai shi ne duk da cewa kusan dukkan al'ummar da suke wajen sun nuna amincewarsu da wannan zabi da Manzo ya yi ko da kuwa a zuciyarsu suna rike da wani abu na daban, amma jim kadan bayan rasuwar Ma'aiki sai suka yi watsi da wannan wasicci nasa suka bi son zuciyarsu inda suka zabi wanda suka zaba a Sakifa bayan zage-zage da kokarin cin kwalan juna. Wasu suna cewa mune muka cancanci halifanci saboda mu ne muka zo tare da Manzo daga Makka, wasu kuma suna cewa mu ne muka cancanta don kuwa mu ne muka ba wa Manzo masauki, wasu kuma suna cewa a'a to shi kenan mu yi sulhu, mu mu zama shuwagabanni ku kuma ku zama wazirai da dai sauran abubuwan da suka faru da tarihi yake jin kunya kawo su, duk da cewa babu wata hujja da suka kawo na kawar da abin da Manzo din ya tabbatar yayin da yace "Man Kuntu Mawlahu, Fa Aliyun Mawlahu", don kuwa su sun riga da sun fahimci mene ne ma'anar kalmar mawla, ba su wani tawili ba face dai kawai su ba a shirye suke su amince da hakan ba ne kawai, tamkar abin nan ne da Ali (a.s) cikin Nahjul Balagah yayin da yake magana kan wadanda suka yi masa tawaye bayan an yi masa bai'a wato Khawarijawa, al'ummar Nana A'isha da kuma ta Mu'awiyya, inda yake cewa:

كَأَنَّهُمْ لَمْ يَسْمَعُوا اللَّهَ سُبْحَانَهُ يَقُولُ تِلْكَ الدَّارُ الْآخِرَةُ نَجْعَلُها لِلَّذِينَ لا يُرِيدُونَ عُلُوًّا فِي الْأَرْضِ وَ لا فَساداً وَ الْعاقِبَةُ لِلْمُتَّقِينَ بَلَى وَ اللَّهِ لَقَدْ سَمِعُوهَا وَ وَعَوْهَا وَ لَكِنَّهُمْ حَلِيَتِ الدُّنْيَا فِي أَعْيُنِهِمْ وَ رَاقَهُمْ زِبْرِجُهَا,

(Kamar ba su ji fadin Allah Madaukaki cewa….."wancan gidan Lahira Muna sanya shi ga wadanda suke ba su nufin daukaka a cikin rayuwar duniya, kuma ba su son barna. Kuma akiba ga masu takawa take(13), lalle wallahi sun ji kuma sun fahimta face dai duniya ce da kawarta kawai suka rufe musu idanuwa(14)).

Sakamakon irin yawan wadanda suka ruwaito wannan lamari na Ghadir ya sanya malaman hadisi suke ganinsa a matsayin hadisi Mutawatiri, to amma duk da haka, masu adawa da wannan lamari saboda sun rasa yadda za su yi su suki hadisin da rashin inganci sai suka koma ga sanya shakku kan abin da hadisin ya ke nunawa na wilaya da shugabancin Ali a kan sauran al'umma inda suke cewa wai wannan kalma ta Mawla ba wai tana nufin shugaba ko majibinci ba ne face dai abin da take nufi shi ne aboki da dai sauransu, wato kamar hadisin yana cewa ne : "Duk wanda na kasance abokinsa, to Aliyu ma abokinsa ne", Allah Ya tsare mu da bin son zuciya da rufe ido kan gaskiya.

Dubi da idon basira zai tabbatar mana da rashin gaskiyar wannan ikirari, da yake ba ma son tsawaitawa, ba za mu tsaya sosai kan wannan batu ma amma dai na yi bayani kan wannan lamari cikin wani rubutu da na yi kan Ghadir da za 'a iya samunsa a shafin internet da na tsara ta wannan adireshi www.alwilayah.net/bukukuwa/ghadir/ghadeer.html ko kuma cikin littafin da aka buga da sunan Ranar Ghadir...Ranar Tabbatar da Halifancin Imam Ali (a.s). Amma duk da haka bari in gabatar da wasu 'yan tambayoyi su ne kuwa: shin anya kuwa duk wani mai hankali zai yarda cewa Manzo zai tara al'ummarsa cikin zafin rana ya ce musu 'Ali abokinku ne'? shin Allah zai ce wa ManzonSa idan bai ce 'Ali abokin musulmi ba ne, kamar bai isar da sako ba har ma ya ce zai kare shi? Shin fadin hakan zai sanya sahabbai su fusata ne ballantana ma har Allah Ya yi alkawarin kare shi daga gare su? Da dai sauran tambayoyi masu yawan gaske da za a iya ganinsu a wannan rubutu da na ambata a sama. Don haka mu dai a iyakacin fahimtarmu wannan kalma ta Mawla tana nufin shugaba kuma majibincin lamari ne.

 

 

____________

(1)- Suratul An'am 6: 124.

(2)- Suratush Shu'ara, 26: 214.

(3)- Tarik al-Tabari 2/63, al-Kamil fi al-Tarikh 2/62, al-Irshad na Mufid yayin da yake magana kan wannan aya, Tafsir al-Majma al-Bayan 2/206, Tarikh al-Damashk na Ibn Asakir 1/86.

(4)- Suratul Ma'ida, 5: 67.

(5)- Mai son karin bayani yana iya duba wadannan litattafa don ganin yadda suka kawo wannan lamari, su ne kuwa: Tafsir al-Kabir na Fakhruz Razi, Durr al-Manthur na Suyuti, Fathul Kadir na Shawkani, yayin da suke magana kan Ayat Tabligh (5:67), Fusul al-Muhimma na Ibn Sabbagh al-Maliki, Asbab al Nuzul na al-Wahidi, Sahih Tirmidhi, Sunan Ibn Maja, Mustadrak al-Sahihain, Fadha'il al-Sahaba na Ahmad bn Hambal, al-Bidayah wa al-Nihayah na Ibn Kathir da dai sauransu masu yawa yayin da suke magana kan wannan batu na Ghadir.

(6)- Al-Mustadrak Ala al-Sahihain: juzu'i na 3 shafi na 126 da 127 da Tarikh al-Bagdadi juzu'i na 11 shafi na 49 da 50 da Usud al-Gabah juzu'i na 4 shafin na 22 da Al-Bidayah wa al-Nihayah juzu'i na 7 shafi na 372 da Tirmizi cikin Sunan juzu'i na 5 shafi na 637.

(7)- Tafsir al-Razi yayin da yake tafsirin aya ta 23 cikin Suratu Aali Imrana sai kuma littafin Kanzul Ummal juzu'i na 13 shafi na 114 hadisi mai lamba 36372.

(8)- Bihar al-Anwar 4/298, Sharh Nahjul Balagah 1/6 da Tazkirat al-Khawas shafi na 87.

(9)- Bihar al-Anwar 4/298.

(10)- Suratul Bakara 2:207.

(11)- Suratul Ahzab 33:36.

(12)- Al-Sirat al-Halabiyya 2/318, al-Manakib na Khawarizmi, shafi na 144 da Sharh Nahjul Balagah.

(13)- Suratul Kasas 28:83.

(14)- Nahjul Balagah, huduba ta uku da aka fi sani da al-Shakshakiyya.