A+ R A-
22 February 2024

Tarihin Kafuwar Shi'a

Tarihin Kafuwar Shi'a:
Daga:
Muhammad Awwal Bauchi
IRIB-Tehran - I.R.of Iran
This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.

________________________

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

 

Kafuwar Shi'anci dai na daga cikin abubuwan da malamai da marubuta daban-daban daga shi'a da sunna suka yi rubuce-rubuce da maganganu daban-daban akai. A daidai lokacin da 'yan shi'a suke cewa shi'anci dai ya kafu ne tun zamanin Manzon Allah (s.a.w.a) ko kuma ma mu ce Manzo din ne ya kafa shi, su kuma 'yan Ahlussunna, musamman ma masu wuce gona da iri daga cikinsu, sun kasu kashi-kashi dangane da wannan batu. Wasu suna cewa ne shi'a ta samo asali ne bayan rasuwar Ma'aikin Allah (s.a.w.a), wasu kuma suna cewa ne shi'an ta kafu ne lokacin Yakin Jamal, (da aka yi tsakanin Imam Ali da Ummul Muminina A'isha da taimakon Talha da Zubairu), wasu kuma cewa suke shi'an ta samo asali ne lokacin Yakin Siffin (yakin da aka yi tsakanin Amirul Muminina Ali (a.s) da Mu'awiyyah), wasu kuma cewa suke an samo shi'an ne bayan Waki'ar Karbala a shekara ta 61 bayan hijira wato lokacin da Umayyawa suka kashe Imam Husaini (a.s) da sahabbansa (r.a), sannan wasu kuma cewa su ke wai Abdullah bn Saba ne ya kafa shi'an. A takaice dai, dukkan bangarorin biyu suna cewa ne, shi'a ta kafu ne:

 

 

 

 1. Lokacin Manzon Allah (s.a.w.a).
 2. Bayan Rasuwar Manzon Allah (s.a.w.a).
 3. Lokacin Yakin Jamal.
 4. Lokacin Yakin Siffin.
 5. Bayan Waki'ar Karbala.
 6. Abdullah bn Saba ne ya kafa shi'a.

 

To yanzu bari mu yi dubi daya bayan daya kan wannan batu da kuma tabbatar da hakikanin gaskiyar lamarin. Za mu fara ne da ra'ayin Ahlusunna.

 

1- Shi'a Ta Kafu Ne Bayan Rasuwar Ma'aiki (s.a.w.a):

 

Masu wannan ra'ayi dai suna cewa ne Shi'a ta kafu ne bayan rasuwar Manzon Allah (s.a.w.a) lokacin da al'umma suka kasu kashi uku. Kashin farko su ne sahabban da suke tare da Imam Ali (a.s), wadanda suka ki yin mubaya'a wa halifa Abubakar, suna masu cewa Ali (a.s) shi ne wanda Manzon Allah (s.a.w.a) ya zaba a matsayin halifansa ba wani na daban ba, wadannan sahabbai su ne 'yan shi'a. Kashi na biyu kuma su ne Ansarawa (mutanen Madina) wadanda suka taru a Sakifa suka ce daya daga cikinsu ne wato Sa'ad bn Ubadah ne zai zamanto halifa. Sai kuma kashi na uku wadanda suka zabi Abubakar bn Abi Kahafa a matsayin halifa.

 

Daga cikin wannan bayani dai muna iya fahimtar cewa a ra'ayin wadannan mutane shi'a ta samo asali ne bayan rasuwar Ma'aiki (s.a.w.a) kuma 'yan shi'a su ne wasu mutane daga cikin sahabbai da suka jingina kansu da Imam Ali (a.s), bayan rasuwar Ma'aiki (s.a.w.a).

 

Babu shakka cikin cewa wadannan sahabbai da suka ki yin bai'a wa Abubakar da sunan cewa ba shi ne ya cancanci halifanci bayan Ma'aiki (s.a.w.a) 'yan shi'a ne, wato mabiya Ali (a.s) ne wadanda suka riga da suka ji abubuwan da Manzon Allah (s.a.w.a) ya fada kan Ali, sannan kuma sun san cewa a wurare daban-daban ya nada Ali a matsayin halifansa, to me ya sa yanzu kuma za a ce su yi mubaya'a wa wani na daban?

 

To amma gaskiyar lamarin dai shi ne cewa ba wai bayan Manzon Allah (s.a.w.a) ne aka samu shi'a ba, don kuwa idan mun sallama cewar wadannan sahabbai (da suka ki yin bai'a) 'yan shi'a ne, to babu yadda za a ce a rana guda ne kawai (wato ranar rasuwar Ma'aiki) suka samar da kansu, face dai tun kafin rasuwar Ma'aikin dama suna nan kuma suna da wannan ra'ayi. Tarihi dai ya tabbatar mana da cewa tun kafin rasuwar Ma'aiki daman wadannan sahabbai suna nan kuma ma a na kiransu da sunan 'yan shi'an Ali, kamar yadda za mu gani nan gaba.

 

3- Shi'a Ta Kafu Ne Lokacin Yakin Jamal:

 

Masu wannan ra'ayi suna cewa ne shi'a ta kafu ne lokacin Yakin Jamal, wato yakin da aka yi tsakanin Amirul Muminina Ali (a.s) da kuma 'yan tawaye karkashin jagorancin Ummul Muminina A'isha da kuma taimakon Talha da Zubair. Suna cewa ne bayan tawayen da Talha da Zubairu suka yi wa Imam Ali (a.s) bayan sun yi masa bai'a tun farko da kuma haduwa da A'isha da suka yi, shi ne da ya haifar da yaki tsakanin bangaren Ali (a.s) da na A'isha ko kuma yaqin da ake kira da Harbul Jamal (Yakin Jamal- Rakumi -), to a nan ne aka samu kafuwar shi'a, wato wadanda suka kasance tare da Ali sune ake kiransu 'yan shi'a, don haka kafuwar shi'anci ta samo ne daga wannan lokaci.

 

Wannan dai zance ne da ba shi da tushe, don haka ba za mu vata lokaci a kansa ba, musamman ma ganin cewa dalilin da zai biyo baya zai kawar mana da wannan ikirari.

 

3- Shi'a Ta Kafu Ne Lokacin Yakin Siffin:

 

To sai kuma masu cewa shi'a ta kafu ne lokacin yakin Siffin tsakanin Amirul Muminina Ali (a.s) da 'yan tawaye karkashin jagorancin Mu'awiyya. Masu wannan ra'ayi dai cewa su ke shi'a ko kuma 'yan shi'a sun samo asali ne lokacin wannan yaki don haka ne ma a ke cewa Shi'atu Ali ('Yan Shi'an Ali) da kuma Shi'atu Mu'awiyyah ('Yan shi'an Mu'awiyya), wato wadanda suke tare da Ali saboda wasu "dalilai na siyasa" (kamar yadda suke cewa) su ne ake ce ma shi'a, don haka a nan ne aka samo shi'a.

 

Ko ba a fadi ba dai babu gaskiya cikin wannan ikirari musamman ma dai idan muka yi la'akari da abubuwan da muka fadi a baya, kuma kamar yadda za mu gani nan gaba. Abin da masu wannan ra'ayi suka mance shi ne cewa wannan siffa (shi'atu Ali da kuma shi'atu Mu'awiyya) da ake amfani da ita ga wadannan kungiyoyi biyu a yarance ne kawai wato ana nufin kungiyar Ali ko kuma kungiyar Mu'awiyya, amma ba wai a bangaren Istilahi ba, don da haka ne to da a yanzu ma ana ci gaba da samun wasu jama'a da suke kiran kansu 'yan shi'an Mu'awiyya kamar yadda ake samun 'yan shi'an Ali. Wannan ba komai ba ne kawai face dai kokarin wofantar da hankulan wawayen mutane masu karancin tunani.

 

Wani abin da yake da kyau a fahimta shi ne cewa wannan rikici da ya faru tsakanin bangarorin biyu ya wuce rikici na siyasa kamar yadda wadannan mutane suke gani, face dai lamari ne dake da alaka da akida da kuma koyarwa ta Musulunci, wato a takaice dai yaki ne tsakanin gaskiya da karya. Abin da ya zama wajibi akan wadannan mutane su yi bayani wa al'umma shi ne, wani bangare ko kuma wata kungiya ce take kan gaskiya, wacce ce kuma take kan bata, don kuwa "babu wani abu bayan gaskiya face bata". Wannan shi ne abin da ya hau kansu su yi bayani kansa ba wai kokarin nokewa da fitar da wasu uzururruka marasa tushe ba. Shin Ali da Sahabbansa (r.a) da suka yaki Mu'awiyya ne suke kan gaskiya ko kuwa Mu'awiyya da sahabbansa ne suke kan gaskiya? Daya ne dai cikin biyu, babu kuma na uku, wato babu yadda za a ce dukkansu suna kan gaskiya. Wasu dai sun yi kokarin cewa Ali ne yake kan gaskiya, wato Mu'awiyya ya yi kuskure, to amma sai kuma suka kirkiro wata ka'ida cewa duk wanda ya yi kokari ya yi ijtihadi, idan ya samu dacewa to yana da lada biyu idan kuwa bai samu dacewa ba to yana da lada guda. Don haka Ali da ya dace yana da lada biyu shi kuwa Mu'awiyyan duk da cewa ya yi ijtihadi amma bai dace ba, to yana da lada guda. Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi al-Raji'un....wannan wani irin kin gaskiya ne? Ko da man mun sallama ga wannan ka'ida, to amma abin tambaya a nan shi ne cewa wai shin da gaske ijtihadin ne kuwa Mu'awiyya ya yi ko kuma ...? Wannan dai tambaya ce da take bukatuwa da amsa!

 

To da yake da dama sun yi shiru, sun ki bayyana gaskiyar wannan lamari, bari mu yi kokarin bayyana abin da muka fahimta daga wannan lamari.

 

Daya daga cikin dalilan da suka sanya wadannan mutane suke ganin dukkanin bangarorin biyu suna da gaskiya, baya ga dalili na son rai, shi ne batun cewa ai rikicin rikici ne kawai na siyasa ba shi da wata alaka da addini, wato a takaice dai rikici ne kawai na neman mulki da iko akan juna. To sai dai mu a iyakacin fahimtarmu wannan rikici ya hada dukkan wadannan bangarori (addini da siyasa) musamman ma idan muka dauki siyasa a ma'anarta na neman mulki. Abin nufi kuwa shi ne cewa daya daga cikin bangarorin biyu yana kare addini ne daya kuwa yana kokarin tabbatar da mulkinsa ne, abin da kawai ya rage mana shi ne mu gano mai kare Musuluncin da kuma mai kare siyasar neman mulki. Wannan shi ne abin da ya kamata mu yi ba wai mu tsaya muna boye gaskiya da cewa rikici ne kawai na siyasa ba.

 

Wani abin da yake da kyau a kara fahimta shi ne cewa masu cewa wannan rikici na siyasa ne, ba su tunani sosai ba, da dai sun yi tunanin lalle da ba su ce haka ba.

 

Na farko dai fadin hakan yana iya sanya sakamakon jagororin wadannan bangarori biyu cikin hatsari, don hakan na iya tabbatar da cewa sun ta da fitina ne kawai tsakanin al'umma don biyan wasu bukatunsu na siyasa da neman mulki da ta yi sanadiyyar mutuwa ko shahadar dubun-dubatan musulmi. Idan kuwa har haka ne, to fa babu makawa makomarsu wuta ne (wal iyazu billahi). Allah Madaukakin Sarki na cewa: "Kuma duk wanda ya kashe wani mumini da ganganci, to sakamakonsa Jahannama, yana madawwami a cikinta, kuma Allah Ya yi fushi da shi kuma Ya la'ane shi, kuma Ya yi masa tattalin azaba mai girma". (Suratun Nisa': 5:93)

 

Kamar yadda kuma aka jiyo Ibn Umar yana cewa ya ji Manzon Allah (s.a.w.a) yana cewa: "Kada ku kafirta a bayana ta hanyar sare wuyayen junanku". A cikin Bukhari ma an ruwaito Abdullahi bn Mas'ud na cewa: Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: "Zagin musulmi fasikanci ne, kashe shi kuwa kafirci ne".

 

Daga cikin wadannan nassosi dai muna iya fahimtar cewa:

 

 

 

 • Kashe musulmi aiki ne na kafirci.
 • Kashe mumini da gangan na iya kai mutum wutan Jahannama.

 

Abin tambaya a nan shi ne shin musulmi/mumini nawa ne aka kashe a wannan yaki na Siffin? Amsa dai, suna da yawa. To mene ne hukumcin wadanda suka tayar da wannan fitina?

 

A ganinmu dai hanya guda da za a iya kubutar da bangare guda daga fadawa karkashin wannan hukumci ita ce idan har akwai wata ka'ida ko doka da ta halalta wa musulmi yakin dan'uwansa musulmi, idan kuwa ba haka ba, to babu mafita.

 

Idan muka yi dubi za mu ga cewa Musulunci ya ba wa halaltaccen shugaba (halifa) ikon yakan 'yan tawaye wadanda suke kokarin ruguza Musulunci da haifar da fitina tsakanin musulmi. A nan yana da kyau a fahimci cewa wannan aiki fa ba aikin kowani jebun shugaba ba ne face dai aiki ne na shugaban da ya dace, shi ya sa muka yi amfani da kalmar halaltaccen shugaba, wanda Allah da ManzonSa suka amince da shugabancinsa.

 

Mu dai bayan bincike da tunani mai zurfi ba mu ga wanda ya dace da wannan siffa ta halaltaccen shugaba tsakani Imam Ali (a.s) da Mu'awiyya ba sai Amirul Muminina Ali (a.s), hakan kuwa saboda wadannan dalilai ne:

 

 

 

 1. 1- Fadin Manzon Allah (s.a.w.a) cewa: "Ali na tare da gaskiya kuma gaskiya na tare da shi, ba za su taba rabuwa ba har sai sun same ni a bakin tafki(1)".
 2. Fadinsa (s.a.w.a) cewa: "Ali na tare da Alkur'ani, Alkur'ani kuma na tare da Ali, kuma dukkan wadannan biyun ba za su rabu da juna ba har sai sun riske ni a bakin tafki"(2).
 3. Fadinsa (s.a.w.a) cewa: "Duk wanda ya yi min biyayya ya yi wa Allah Madaukakin Sarki, wanda kuma ya saba min ya saba wa Allah, wanda kuma ya yi wa Ali biyayya to ya yi min biyayya, wanda kuma ya saba wa Ali ya saba min(3)".
 4. Fadinsa (s.a.w.a) ga Ammar bn Yasir cewa: "Ya Ammar! Idan ka ga Aliyu ya kama wani tafarki sannan sauran jama'a kuma suka kama wani tafarkin na daban, to ka bi Aliyu ka bar mutane, don kuwa shi ba zai tura ka zuwa ga bata ba kamar yadda kuma ba zai fitar da kai daga tafarkin shiriya ba(4)".

 

Wadannan hadisai dai suna nuni ne da kasantuwar Ali na tare da gaskiya a duk inda yake, don haka duk tafarkin da ya dauka, to tafarki ne na gaskiya, wanda kuma ya saba masa ya saba wa Allah da ManzonSa.

 

A bangare guda kuma mun rasa irin wadannan shaidu akan Mu'awiyya face ma dai wasu hadisai da suke tabbatar da rashin gaskiya da kuma zaluncinsa. Ga wasu daga ciki:

 

1- Bangaren Mu'awiyya shi ne bangaren masu wuce gona da iri (Kaucacciyar Hanya):

 

(A). Fadin Manzon Allah (s.a.w.a) cewa: "Ya Ali! Da sannu wata kungiya ta masu wuce gona da iri (fi'atul Bagiyya) za ta yake ka, lalle za ka kasance a kan gaskiya. Duk wani wanda bai goya maka baya ba a wannan ba zai kasance daga cikinmu ba(5)".

 

Wannan hadisi na nuna mana cewa Ali da kungiyarsa su ne suke kan gaskiya kuma bangaren Mu'awiyya su ne masu wuce gona da iri, don haka hakkin Ali (a.s) ne ya yake su idan suka ki dawowa kan gaskiya bayan kiransu zuwa ga hakan, kamar yadda kuma tarihi ya tabbatar mana da cewa ya kiraye su zuwa ga hakan, bayan sun ki ne ya yake su: Allah Madaukakin Sarki na cewa:

 

( وَ إِنْ طَائِفَتَانِ مِنَ الْمُؤمِنِينَ اقْتَتَلواْ فَأَصْلِحُوا بيْنَهُمَا فَإِنْ بَغَتْ إِحْدَاهُمَا على الأُخْرى فَقَتِلُوا الَّتِي تَبْغى حَتَّى تَفِىء إلى أَمْر الله )

 

"Kuma idan jama'a biyu ta muminai suka yi yaki, to ku yi sulhu a tsakaninsu. Idan dayansu ta yi zalunci a kan gudar, to sai ku yaki wadda ke yin zalunci har ta koma zuwa ga umarnin Allah......". (Suratul Hujurat: 49:9).

 

A fili wannan aya tana nuna hakkin da halaltaccen shugaba yake da shi ne na yakan masu wuce gona da iri karkashin jagorancin Mu'awiyya.

 

(B). Fadinsa (s.a.w.a) ga Ammar bn Yasir cewa: "Ya Ammar! Hakika a bayana za ka yi yaki da kungiyoyi biyu tare da Ali, Al-Nakithin (masu karya alkawari ko bai'arsu) da kuma Al-Kasitin (azzalumai), sannan kuma masu wuce gona da iri za su kashe ka".

 

2- Fada da Ali Fada Ne Da Manzon Allah (s.a.w.a):

 

(A). Zaid bn Arkam ya ruwaito cewa: Manzon Allah (s.a.w.a) ya fada wa Ali, Fatima, Hasan da Husaini (a.s) cewa: "Ina zaman lafiya da mai zaman lafiya da ku, sannan kuma ina yaki da mai yaki da ku".

 

Baya ga wannan hadisi akwai kuma wasu hadisai da suke nuna gaskiyar Ali (a.s) da kuma kaucewar Mu'awiyya:

 

(B). Fadin Manzon Allah (s.a.w.a) ga Imam Ali (a.s) cewa: "Ba mai sonka sai mumini babu kuma mai kinka sai munafuki(6)".

 

(C). Fadarsa (s.a.w.a) ga Ali (a.s) cewa: "Mumini ba ya kinka kamar yadda kuma munafuki ba ya sonka". Don haka ne ma aka jiyo Abuzar al-Giffari yana cewa: Mu kan gane munafuki ne da karyata Allah da ManzonSa... da kuma kiyayyarsa ga Aliyu bn Abi Talib(7).

 

(D). Fadarsa (s.a.w.a) cewa: "Duk wanda ya cutar da Ali ya cutar da ni(8)".

 

Fadarsa (s.a.w.a) cewa: "Duk wanda ya zagi Ali ya zage ni(9)".

 

Tarihi dai ya ruwaito mana cewa Mu'awiyya da mutanensa sun kasance suna zagin Ali da la'antarsa a kan mimbari saboda kiyayyar da suke yi da shi.

 

Ibn Kathir cikin al-Bidayah ya bayyana cewa daya daga cikin haramtattun ayyukan da Mu'awiyya da mabiyansa suka dinga yi shi ne la'antar Ali akan mimbarin sallar juma'a, ta yadda har ma daga baya akan zo masallacin Annabi a Madina a aikata hakan....".

 

To ga bayanai dai ya rage wa mai karatu ya yi hukumci.

 

4- Shi'a Ta Kafu Ne Bayan Waki'ar Karbala:

 

Yanzu kuma bari mu yi dubi kan batu na uku, wato cewa shi'a ta kafu ne bayan Waki'ar Karbala. Wannan ma dai kamar sauran ikirarin da suka gabata babu gaskiya cikinsa, don kuwa tun kafin waki'ar Karbala akwai 'yan shi'a mabiya Ahlulbaiti (a.s). Idan muka duba za mu ga cewa wadannan mutane da suka kasance tare da Imam Husaini (a.s) har suka yi shahada, 'yan shi'a ne wadanda suka kasance tare da Amirul Muminina Ali (a.s) da kuma dansa Imam Hasan (a.s) kafin daga baya kuma suka kasance da Imam Husaini (a.s). Don haka babu yadda za a ce a lokacin ne suka samar da kansu kana kuma suka bi Husaini (a.s), kamar yadda kuma ba bayan wannan waki'ar ne aka samu shi'an ba. Idan har aka ce haka, to fa dole ne a amsa tambayar cewa su wane ne wadanda suka kasance tare da Husain (a.s) a wannan rana?

 

Abin da dai ya kamata masu wadannan ra'ayuyyuka su ce ko kuma su fahimta shi ne cewa dukkan wadannan abubuwa guda uku ko kuma lokuta uku, wato bayan rasuwar Ma'aiki, lokacin yakin Siffin da kuma bayan waki'ar Karbala ba su ne asalin kafuwar shi'a ba face dai ana iya cewa lokuta ne da suka taimaka wajen yaduwar shi'a da fitar da matsayinsu a fili, amma ba su ne kafuwar shi'a ba. Misali bayan rasuwar Manzon Allah (s.a.w.a) matsayar da mabiya Ali ('yan shi'a) suka dauka ta kin yin bai'a wa halifa Abubakar na nuni ne da cewa akwai wasu mutane da suke da ra'ayin cewa lalle halifanci na Imam Ali (Ahlulbaiti) (a.s) ne kuma ba a shirye suke su yi watsi da wasiyyar Annabinsu ba. Haka ma lokacin Siffin, 'yan shi'a sun dada fitowa fili inda suka tsaya kyam tare Imaminsu (Ali) da kuma ba da rayukansu wajen taimakawa wa Imaminsu kare Musulunci da ladabtar da 'yan tawaye, kamar yadda kuma suka yi hakan a lokacin waki'ar Ashura, inda suka kasance tare da Imaminsu (Imam Husaini) wajen kare Musulunci daga fadawa hannun shu'uman mutane da kuma bayyanar da Musulunci na hakika daga jabun musuluncin da Umayyawa suke kokarin gabatarwa.

 

5- Abdullah bn Sabah Ne Ya Kafa Shi'a:

 

Masu wannan ra'ayi dai suna cewa ne wai wani mutum mai suna Abdullah bn Saba shi ne wanda ya kirkiri shi'anci. A cikin rubuce-rubucensukan wannan majahulin mutum sun bayyana cewa shi wani bayahude wanda ya shigo cikin addinin Musulunci lokacin halifanci Usman bn Affan da nufin cutar da Musuluncin, inda ya samu tasirantuwa cikin zukatan wasu sahabbai da cusa musu akidunsa lamarin da ya haifar da shi'anci.

 

To sai dai kuma malumanmu sun bayyana cewa daya daga cikin Asatirul awwalina shi ne wannan batu na Abdullah bn Saba da kuma cewa shi ne wanda ya kirkiro shi'anci, don kuwa duniya ma dai ba ta taba sanin wani mutum mai suna Abdullah bn Saba ba. Malumman tarihi da masu bincike daban-daban sun tabbatar da cewa babu wani mutum mai suna Abdullah bn Saba, face dai makiya shi'a ne suka kirkiro wannan suna don wasa da hankulan mutane da katange su daga fahimtar gaskiya.

 

Daga cikin malumman tarihin da suka kawo wannan labari maras tushe, wanda kuma daga baya ma wasu malamai suka tasirantu da rubutun nasa shi ne Ibn Jarir al-Tabari. Ga abin da yake cewa cikin littafin tarihinsa:

 

Abdullah bn Saba dai ya kasance bayahude ne daga San'a, mahaifiyarsa kuwa bakar fata ce, ya musulunta ne lokacin Usman, daga nan sai ya fara yawo kasashen musulmi da nufin batar da su. Ya fara ne daga Hijaz sai kuma Basra sai Kufa daga nan kuma ya nufi Sham, sai dai kuma bai samu nasarar janyo ko da mutum guda ba daga cikin mutanen Sham zuwa ga abin da yake so, inda suka fatattake shi ya nufi Masar. Daga cikin irin abubuwan da ya dinga yadawa a Masar din har da cewa: Abin mamaki shi ne cewa (Annabi) Isa zai dawo amma ana karyata cewa (Annabi) Muhammadu (s.a.w.a.) zai dawo, alhali kuwa Allah Madaukakin Sarki na cewa: ( إِنَّ الَّذي فَرَضَ عَلَيْكَ الْقُرْانَ لَرَادُّكَ إِلَى مَعَادٍ ), (Lalle ne Wanda Ya faralta Alkur'ani a kanka, hakika, Mai mayar da kai ne zuwa ga makoma) (10). don haka Muhammadu shi ne ya fi cancanta da dawowa akan Isa. Don haka sai mutanen suka yarda masa,sai aka shigo da akidar raja'a (komowa zuwa ga rayuwa bayan mutuwa). Daga nan sai ya ce musu: Akwai annabawa guda dubu kuma kowani Annabi yana da wasiyyi, wasiyyin Manzon Allah (s.a.w.a) kuwa shi ne Ali. Har ila yau kuma sai ya ci gaba da ce musu: Muhammadu dai shi ne cikamakin Annabawa Aliyu kuma cikamakin wasiyyai, Usman ya kwace hakkin wannan wasiyyi (Ali) ne da kuma zaluntarsa, don haka wajibi ne a fuskance shi don kwato wannan hakki da maishe shi zuwa ga masu shi. Daga nan kuma sai Abdullah bn Saba ya watsa mutanensa zuwa garuruwan musulmi da umartansu da su watsa batun 'umarni da kyawawa da kuma hani da munana', batanci ga shuwagabanni da kiran mutane su yi musu tawaye, inda ya samu janyo hankulan wani adadi na musulmi cikinsu kuwa har da manyan sahabbai da tabi'ai irin su Abu Zar, Ammar bn Yasir, Muhammad bn Hudhaifa, Abdurrahman bn Udais, Muhammad bn Abi Bakr, Sa'asa'a bn Sauhan al-Abdi, Malik al-Ashtar da dai sauransu na daga cikin fitattun musulmin farko.

 

Tabari ya ci gaba da cewa: Ta haka ne wadannan mutane da ya kira Sabi'awa suka dinga tunzura mutane da kiransu zuwa ga tawaye ga shuwagabanninsu, inda suka sami nasarar tunzura mutane zuwa garin Madina da mamaye gidan halifa Usman, daga karshe suka kashe shi. Tabari ya ci gaba da cewa bayan kashe Usman da kuma mubaya'ar da mutane suka yi wa Ali (a.s) da kuma tawayen da Talha da Zubairu suka yi masa abin da ya yi sanadiyyar haifar da yakin Jamal, wadannan sabi'awa sun sake tada wata fitinar lokacin da suka lura cewa shuwagabannin bangarorin da suke yaki da junan suna kokarin fahimtar juna da kawo karshen yakin. Sabi'awan dai sun ji tsoron cewa ne idan har aka fahimci juna to fa za a gano su da kuma neman zartar musu da haddi kan jinin Usman da suka zubar. Don haka sai suka shiga rundunonin biyu da fara kai hare-hare abin da ya haifar da wannan yaki ba tare da ma shugabannin bangarorin biyu sun san da hakan ba(11).

 

To wannan dai shi ne abin da Tabari ya ce dangane da Abdullah bn Saba da mabiyansa (Sabi'awa) wanda aka ce suna suka kafa shi'anci.

 

To yanzu kuma bari mu yi dubi a gurguje kan wannan labari da Tabari ya bayar don ganin rashin ingancin abin da ya ce da kuma karyar samuwar Abdullah bn Saba.

 

(1)- Dangane da batun Abdullah bn Saba malamai da dama da kuma wasu dalilai sun tabbatar da cewa mutum ne wanda Allah bai halicce shi ba, wato dai malaman tarihi ne kawai suka kirkiro don wata manufa ta siyasa da kuma cutar da shi'anci musamman lokacin mulkin Umayyawa da Abbasiyawa. Don kuwa idan muka duba za mu ga cewa shi Tabari ya ruwaito wannan 'tatsuniya' tasa kan Abdullah bn Saba ne daga Saif bn Umar al-Tamimi, wanda aka sanshi da karya da kirkiro labari.

 

(2)- Abu na biyu kuma shi ne duk wani mutum mai hankali zai yi wahala ya yarda da wannan labari na Tabari, don kuwa abu ne da ba zai taba yiyuwa ba a ce wai wani bayahude ya musulunta (bayan Manzon Allah), ya samu irin wannan dama ta shiga cikin musulmi, da wofantar da manyan sahabbai irinsu Abu Zar da Ammar da dai sauransu (wadanda suka musulunta tun lokacin Manzo) har ya yaudare su, su yarda da akidarsa, su taru su kashe halifan musulmi. Kai wannan labari dai ya yi kama da labari gizo da koki da ake gaya mana lokacin muna yara. Abin tambaya a nan ina sauran musulmi suke da har suka bar wannan Bayahude ya ratsa cikin musulmi ba tare da sun dakatar da shi ba? Ina mahukuntan lokacin su ke da har suka gagara kama shi da hukumta shi ba? Da dai sauran tambayoyi masu yawan gaske, wadanda suke tabbatar mana da rashin ingancin wannan lamari. A bangare guda kuma ma wannan labari cin mutumci ne ga manyan sahabban Manzon Allah (s.a.w.a) da kuma tarihin Musulunci shi kansa, ganin yadda wani bayahude zai shigo cikin musulmi ya yi wasan kura da su da kuma tarihinsu, a hakikanin gaskiya ma dai yarda da wannan tarihi zai iya sanya alamun tambaya da dama a kan tarihin Musulunci.

 

(3)- Abu na uku kuma tarihi ya tabbatar mana da cewa halifa Usman ba ya wasa da masu adawa da mulkinsa, wato a takaice dai ya kan yi amfani da karfi akan masu nuna rashin amincewa da siyasarsa, kamar yadda ya yi da sahabin Manzo Abu Zar wanda ya ke nuna rashin amincewa da irin wariya da wasa da baitul malin musulmi da aka yi lokacin halifancin Usman, inda Usman ya azabtar da shi da tura shi zuwa wani kauye, kamar yadda kuma yaransa suka bugi Ammar bn Yasir har suka karya masa awaza da dai sauransu. Irin wannan yanayi zai iya tabbatar mana da rashin gaskiyar samun wani bayahude ya zo cikin musulmi ya tayar da fitinar da har za ta kawo karshen rayuwar halifa.

 

Da dai sauran dalilai, mai son karin bayani yana iya komawa ga rubutun da muka yi kan "Shi'a Da Abdullah bn Saba" don ganin karin bayani.

 

A takaice dai wadannan bayanai suna nuna mana cewa Abdullah bn Saba, idan ma har akwai wani mutum mai suna hakan, ba shi da wata alaka da shi'anci. Kai idan ma har mun sallama cewa akwai wannan majahulin mutum, to amma abu ne mai wuya a ce kawai rana guda ne ya sanya wa wadannan sahabbai tunanin cewa halifanci fa hakki ne na Ali da Ahlulbaiti (a.s), face sai dai a ce ya zo ne ya samu wadannan mutane suna da wannan ra'ayi, shi kuwa sai ya gina a kan hakan don cimma burinsa. To idan kuwa hakan ne, to babu makawa ba shi ne ya assasa shi'anci ba, face dai wadannan sahabbai daman 'yan shi'a ne, sun ji abubuwan da Manzon Allah (s.a.w.a) ya fadi tun ranar farko yada sakon Musulunci kuma suka ci gaba da riko da shi. Hakan fa idan wai mun sallama ne cewa akwai Abdullah bn Saba kuma ya yi abin da aka ce ya yi din.

 

To amma ai duk wanda ya san wadannan mutane (Abu Zar, Ammar da dai sauransu) ya san sun fi karfi wani bayahude ya yi wasa da hankulansu. A nan gaba za mu yi rubutu kan tarihin rayuwar wadannan mutane don gani matsayinsu.

 

 

 

6- Shi'a Ta Kafu Ne Lokacin Manzon Allah (s.a.w.a):

 

To yanzu bari mu yi dubi cikin asalin kafuwar shi'a.

 

Dubi cikin tarihi da kuma hadisan Ma'aiki (a.s) za su iya tabbatar mana da cewa tun lokacin Manzon Allah (s.a.w.a), kai tun ma farko-farkon sakonsa (s.a.w.a) ya bayyanar da shi'anci kuma ya ambaci wasu mutane da sunan shi'a, don haka muna iya cewa shi'a ta samo asali ne tun zamanin Manzo (s.a.w.a). Ga kadan daga cikin abubuwan da suke tabbatar da hakan:

 

1- Tabari cikin tafsirinsa Jami'ul Bayan ya ce: Ibn Humaid ya gaya mana…daga Abu al-Jarud daga Muhammad bn Ali cewa: Yayin da aka karanta wannan aya ta: ( إِنَّ الّذين أَمَنُوا وعَمِلُوا الصَّالِحاتِ أُولئكَ هُمْ خَيْرُ الْبَريَّة ) sai Annabi (s.a.w.a) ya ce wa Ali: Kai ne Ya Ali da 'yan shi'anka.

 

2- Al-Shawkani cikin tafisirinsa Fathul Kadir juzu'i na 5: Ibn Mardawihi ya ruwaito daga A'isha tana cewa na ce wa Manzon Allah (s.a.w.a) Ya Manzon Allah wace halitta ce tafi soyuwa a wajen Allah, sai ya ce: A'a A'isha ashe ba ki karanta fadin Allah cewa:
( إِنَّ الّذين أَمَنُوا وعَمِلُوا الصَّالِحاتِ أُولئكَ هُمْ خَيْرُ الْبَر) ba.

 

3- Ibn Asakir ya ruwaito daga Jabir bn Abdullah al-Ansari cewa: Mun kasance wajen Manzon Allah (s.a.w.a) sai Aliyu ya zo sai ya ce: "Na rantse da wanda raina ke hannunsa, wannan (Ali) da mabiyansa ('yan shi'ansa) su ne masu samun rabo ranar kiyama", sai ya karanto wannan aya ta Alkur'ani mai girma da ke cewa (إِنَّ الّذين أَمَنُوا وعَمِلُوا الصَّالِحاتِ أُولئكَ هُمْ خَيْرُ الْبَريَّة), ta yadda hatta sahabbai Manzon Allah (s.a.w.a) a duk lokacin da Aliyu ya zo sukan ce : Hakika "Khairul Bariyya". ya iso.

 

4- Al-Shabalanji cikin littafinsa Nurul Absar, yayin da yake magana kan falalar Aliyu (a.s) ya kawo wani hadisi daga Ibn Abbas da ke cewa: Lokacin da aka saukar da ayar: ( إِنَّ الّذين أَمَنُوا وعَمِلُوا الصَّالِحاتِ أُولئكَ هُمْ خَيْرُ الْبَريَّة )", Manzon Allah (s.a.w.a) ya gaya wa Ali cewa: "Kai da shi'arka za ku zo ranar kiyama yardaddu….".

 

5- Ibn Hajar al-Haithami cikin littafinsa al-Sawa'ik al-Muhrika ya ce Ibn Abbas na cewa: Lokacin da aka saukar da wannan aya Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce wa Ali "Kai da shi'arka za ku zo ranar kiyawam yardaddu....", har daga karshe ma yake cewa wannan hadisi ingantacce ne.

 

(Yana da kyau a fahimci cewa shi fa Ibn Hajar yana daga cikin mutanen da suke gaba da shi'a sosai, kai ya ma rubuta wannan littafi ne don sukan shi'an, to amma dai ga abin da yake cewa)

 

Akwai dai malaman Ahlussunna da dama da suka ruwaito wannan bayani, daga cikinsu kuwa akwai Al-Khadib al-Khawarizmi cikin al-Manakib, Abu Na'im al-Isfahani cikin Al-Khisal, Ibn Sabbag al-Maliki cikin Fusul al-Muhimma, Shaikh Sulaiman al-Kanduzi cikin Yanabi'ul Mawadda, Alusi cikin Ma'ani da dai sauransu.

 

Wannan ne ma ya sa ake kiran wasu daga cikin sahabbai da sunan 'Yan Shi'an Ali, daga cikinsu kuwa har da:

 

1)- Ammar Yasir. (2)- Mikdad bn al-Aswad al-Kindi. (3)- Salman al-Farisi. (4)- Abu Dharr al-Ghiffari. Wadannan hudun dai su ne ake kira da Arkanul Arba' (Ginshikan ('yan shi'a) hudu) 5)- Hudhayfah bn Yaman, (6)- Khuzayma bn Thabit, wanda Manzon Allah (s.a.w.a) ya kira shi da 'Dhush Shahadatayn (Wanda shahadarsa take daidai da na mutane biyu). (7)- Abu Ayyub al-Ansari, wanda ya sauki Manzo (s.a.w.a) a gidansa bayan hijira. (8)- Abdullah bn Abbas. (9)- Sahl bn Hunayf. (10)-Usman bn Hunayf. (11)- Al-Bara'a bn Azib al-Ansari. (12)- Ubayy bn Ka'ab. (13)- Abu al-Haitham Malik bn al-Taihan. (14)- Khalid bn Sa'id. (15)- Adi bn Hatam (16)- Ubadah bn al-Samit. (17)- Bilal al-Habashi. (18)- Abu Rafi', bawan Manzon Allah (s.a.w.a). (19)- Hashim bn Utbah. (20)- Jabir bn Abdullah al-Ansari. Da dai sauransu.

 

Dukkan wadannan abubuwa suna nuna mana da cewa shi'anci ya kasance a zukatan al'umma tun zamanin Manzon Allah (s.a.w.a) har zuwa lokacin wafatinsa (s.a.w.a), hakan ne kuma ya sanya lokacin da suka ga an bar wasiccin Manzon Allah (s.a.w.a) kan wanda zai gaje shi suka taru a gidan Ali (a.s), gidan da Manzon Allah (s.a.w.a) ya yi ta musu wasiyya kansa duk tsawon rayuwarsa, don kuwa ba don haka ba abu ne mai wahalan gaske a ce a rana guda ne kawai zukatansu suka kulla musu haka, ko da wasa.

 

Baya ga wadannan abubuwa, wani abin da ke dada tabbatar mana da kafuwar shi'anci tun lokacin Ma'aiki (s.a.w.a) shi ne, idan muka duba za mu ga cewa daya daga cikin ginshikan akidun shi'a shi ne Imamanci ko kuma Halifanci kamar yadda aka fi sani, wanda ya fara tun daga Amirul Muminina Ali (a.s) har zuwa na biyu Imam al-Mahdi (a.s), to wannan akida kuwa tun farko-farkon Musulunci Manzon Allah (s.a.w.a) ya kafa ta kuma ta samu gindin zama a zukatan musulmi. A takaice ma dai tun ranar da Manzon Allah (s.a.w.a) ya fara kiran mutane zuwa ga Musulunci ya kafa tushen shi'anci. Abin tambaya shi ne ya ya aka yi hakan ya faru. Ga kadan daga cikin bayanin hakan:

 

1- Umarnin farko da Allah Madaukakin Sarki ya yi wa ManzonSa wajen isar da sakon Musulunci ga al'umma shi ne umarnin Kiran Makusanta, inda Allah Yake cewa: ( وَأَنذِرْ عَشِيرَتَكَ الْلأَقْرَبِينِ ), ma'ana: "Kuma ka yi gargadi ga danginka mafiya kusanci".

 

Malaman tarihi sun ruwaito cewa bayan saukar wannan aya, Manzo (s.a.w.a) ya gayyaci danginsa cin abinci don isar da wannan sako gare su. Fara kiransa ke da wuya sai baffansa Abu Lahabi ya dakatar da shi, ya tsawatar da shi a kan ci gaba da kiran. Sai taro ya watse ba tare da Manzo ya sami daman ci-gaba da kiransa ga mutanensa ba. Bayan wasu 'yan kwanaki sai Manzo (s.a.w.a) ya sake gayyatar dangin nasa. Bayan sun gama cin abinci sai ya riga fara magana, inda ya ce:

 

"Ya ku 'ya'yan Abdul-Mudallibi, lallai Allah Ya aiko ni ne gare ku da aika na musamman, inda Ya ce: "Kuma ka gargadi danginka na kusa." To ina kiran ku ne zuwa ga kalmomi biyu masu sauki ga harshe (amma) kuma masu nauyi a mizani: Shaidawa babu abin bauta sai Allah, kuma ni ManzonSa ne. Wane ne zai amsa min wannan al'amari ya kuma taimake ni a kan aiwatar da shi, sai ya zama dan'uwana, abin wasicina, mataimakina, mai jiran gadona kuma halifana a baya na?(12).

 

Sai Ali bin Abi Dalib (a.s) ya mike, alhali shi ya fi karancin shekaru a tsakanin wadanda ke nan, ya sanar da cewa: "Ni ne Ya Manzon Allah, zan taimake ka a kan wannan al'amarin" Sai Manzo ya umurce shi da zama. Ya kuma maimaita kiransa amma babu wanda ya amsa masa sai Ali (a.s), don haka daga karshe dai Manzon Allah (s.a.w.a) ya amince masa da hakan(13).

 

Don haka daga nan za mu ga cewa tun a wannan rana ne Manzon Allah (s.a.w.a) ya tabbatar da wannan akida ta imamanci da kuma gina tushen shi'anci. A takaice dai tun a wannan rana ce Manzo ya gina wadannan abubuwa guda uku, su ne kuwa:

 

 

 

 • Babu wani abin bautawa da gaskiya sai Allah.
 • Annabi Muhammadu kuwa ManzonSa ne.
 • Sannan Aliyu kuma dan'uwansa ne, wasiyyi kana kuma halifansa a bayansa.

 

Baya ga wannan akwai kuma wasu lokuta daban-daban da Manzon Allah (s.a.w.a) ya tabbatar da akidar halifancin Ali a bayansa, kamar su hadisin Manzila, wato fadin Manzo (s.a.w.a) ga Ali cewa: "Matsayinka a wajena kamar matsayin Haruna ne a wajen Musa, sai dai kawai babu annabi a bayana", da kuma a Ghadir Khum lokacin da ya ce: "Duk wanda na kasance shugabansa, to Aliyu ma shugabansa ne....", da dai sauran hadisai da dama da suke tabbatar da hakan.

 

Bayan wannan takaitaccen bayani dai muna iya fahimtar cewa shi'anci dai ba wai wani kagaggen abu ba ne da har za a iya magana kan lokacin da ya samu. Matukar dai ana son magana kan kafuwar shi'a ko kuma lokacin samuwarta, to dole ne a koma ga lokacin kafuwar Musulunci da samuwarsa don kuwa babu wani banbanci da lokacin samuwar Musulunci da samuwar shi'anci. A takaice dai tun ranar kafa tubalin Musulunci aka kafa tubalin shi'aci, face dai kawai wasu masu kokarin ganin sun dushe hasken Musulunci ne suke yaudaran kansu da kuma wadanda suka rufe idanuwa da zukatansu, to sai dai kuma sun mance cewa Allah Ya yi alkawarin cika haskenSa ko da kuwa ba sa so.

 

Wassalamu Alaikum Wa Rahmatullah

 

 

 

____________

(1)- Al-Khadib al-Bagadadi, cikin Tarikh Bagadad,juzu'i na 14, shafi na 321; da al-Haithami cikin Majma al-Zawa'id, juzu'i na 7, shafi na 235; da tafsirin Razi, juzu'i na 1, shafi na 111 da kuma Kanzul Ummal, juzu'i na 11, shafi na 621, hadisi na 33018.

(2)- Don karin bayani dubi Kanzul Ummal na Muttaki al-Hindi, juzu'i na 11, hadisi na 32912.

(3)- Dubi Kanzul Ummal, juzu'i na 11, shafi na 614, hadisi na 32973.

(4)- Dubi Kanzul Ummal, juzu'i na 11, shafi na 613, hadisi na 32972, Dailami ne ya ruwaito daga Ammar bn Yasir da kuma Abu Ayyub al-Ansari.

(5)- Kanzul Ummal na Muttaki al-Hindi juzu'i na 11, shafi na 613, hadisi na 32970 - Ibn Asakir daga Ammar bn Yasir.

(6)- Sahih Muslim, juzu'i, shafi na 61, Sunan Ibn Majah, juzu'i na 1, shafi na 42, Musnad Ahmad bn Hanbal, juzu'i na 1, shafi na 84, 95, 128, Sunan Tirmizi, juzu'i na 5, shafi na 299, 306 da kuma 371 da kuma Fadha'il al-Sahaba na Ibn Hambal, shafi na 17 dai sauransu.

(7)- Mai son karin bayani kan wadannan hadisai yana iya duba, Tirmizi, Jami'ul-Sahih, juzu'i na 5, shafi na 299; da Ahmad bin Hambali, cikin Musnad, juzu'i na 6, shafi na 292; da Mustadrak al-Sahihain, juzu'i na 3, shafi na 129.

(8)- Majma'al Zawa'id na al-Haithami, juzu'i na 9, shafi na 131.

(9)- Musnad Ahmad Ibn Hambal, juzu'i na 6, shafi na 323, Majma'al-Zawa'id, na Haitami, juzu'i na 9, shafi na 130.

(10)- Suratul Kasas; 28:85.

(11)- Don karin bayani ana iya duba Tarikh al-Tabari, juzu'i na 3, shafi na 378.

(12)- Mai son karin bayani yana iya duba Ibn Athir, cikin al-Kamil, juzu'i na 2, shafi na 24; da Biharul-Anwar, juzu'i na 18, shafi na 164; da Fikihul-Sirah, na Sheikh Muhammad Gazzali, shafi na 102.

(13)- Wadanda suka fitar da wannan sun hada da: Baihaki cikin Sunan da Dala'il da Tha'alabi da Dabari cikin tafsiransu, wajen fassarar Surar Shu'ara'i; da Dabari cikin tarihinsa, juzu'i na 2, shafi na 217; da Ibn Athir cikin al-Kamil, juzu'i na 2, shafi na 22, da Siratul-Halabiyya, juzu'i na 1, shafi na 381; da Ahmad bin Hambali, cikin Musnad, juzu'i na 1, shafi na 11; da Nasa'i cikin Khasa'isu Amirul Mu'uminin, shafi na 6; da Kanzul Ummal, juzu'i na 6, hadisi na 6008, da wasun wadannan da lafuzza masu kusantar juna.