Mafi Girma Da Daukakan Aiki A Ranar Juma'a
- Details
- Published Date
- Written by Muhd Awwal Bauchi
- Category: Hadisai
- Hits: 2995
"عن حماد بن عثمان ، أنّهُ سأل أبا عبد الله (عليه السلام) قال : أخبرنا عن أفضل الأعمال يوم الجمعة ؟ فقال : الصلاة على محمد و آل محمد مائة مرة بعد العصر ، و ما زادت فهو أفضل"
Daga Hammad bn Usman, cewa ya tambayi Imam Sadiq (a.s) cewa: Ka ba mu labarin mafi girma da daukakar ayyukan ranar Juma'a. Sai ya ce: "Salati ga Annabi Muhammadu (s) da Alayensa sau dari bayan (sallar) La'asar, abin da ya karu kan hakan kuwa shi ya fi".
A wani hadisin kuma an tambaye shi (a.s) kan yadda za a yi salatin sai ya ce ka ce:
اَللّهمَّ صَلِّ على محمّدٍ وآلِ محمّد، وعجِّلْ فَرَجَهم
Allah Ya sanya mu daga cikin masu yawaita Salati da Annabi da Alayensa (a.s).
Barkanmu da Juma'a, Allah Ya maimaita mana