A+ R A-
22 February 2024

Kofar Rahamar Ubangiji Mai Fadin Gaske

Allah Madaukakin Sarki Yana da kofofi da hanyoyi da dama na rahama ga bayinSa, addu’a tana daga cikin wadannan kofofi ko kuma ma a ce tana daga cikin mafiya fadinsu wajen samun rahamar Ubangiji cikin rayuwar ‘yan’adam.

Allah Madaukakin Sarki Ya sanya mabudin wannan kofa ta rahama a hannun dukkanin bil’adama da kuma sake musu marar amfani da wannan mabudin wajen bude wannan kofa a duk lokacin da suka ga dama.

Hakan kuwa yana daga cikin rahama da kuma tausayin Allah ga bayinSa na cewa suna da dama a duk lokacin da suke so, su roke shi, su yi magana da Shi, su bukaci duk abin da suke a wajensa ba tare da wani shamaki ba. Ya umurce su da yin addu’a sannan kuma Ya lamunce musu amsa wannan bukata da suka nema daga wajensa.

Allah Madaukakin Sarki Yana cewa: “Kuma Ubangijinku ya ce: Ku kira Ni, in karba (amsa) muku”. Lalle mutum ba zai taba tunanin samun irin wannan falala mai fadin gaske irin wannan ba. Wato ba da umurnin addu’a (gabatar da bukata) da kuma ba da lamunin amsawa, shin akwai gatar da ta wuce wannan? Wata garabasar ma ita ce cewa Allah Ya sanya addu’a a matsayin ma’aunin matsayin bawa a wajenSa yayin da yake cewa: “Ka ce, Ubangijina ba Ya kula da ku in ba domin addu’arku ba”.

A hakikanin gaskiya ba karamin rashin rabo ba ne a ce Allah Madaukakin Sarki Ya bude wa mutum wannan kofa mai fadin gaske ta samun rahama kamar addu’a amma mutum ya juya bayansa daga shiga wannan kofar. Lalle hakan babbar hasara ce.

Alhamdu lillahi mun sami babbar rabo ta hanyar rumbunan addu’oi da muka samu daga wajen Ahlulbaiti (a.s) wanda babu wata al’umma da ta gaji irin wadannan rumbunan. Alhamdu lillahi wadannan rumbunan suna a tattare da mu kuma a hannayenmu duk kuwa da tsawon zamunna da suka shude kana kuma cikin mawuyacin yanayi na siyasa da rayuwa da Ahlulbaiti (a.s) suka fuskanta.

Don haka komai dai yana hannunmu musamman cikin wadannan ranaku da suka rage na Ramalana.

Kada ku manta da ni cikin addu’oinku na alheri.