A+ R A-
22 February 2024

Yakukuwan Manzon Allah (a.s)

YAKIN UHUDU

Abubuwan da suka faru a Badar da arangamar da aka yi na tarihi, ya ci gaba da ruruta wutar kiyayya a zukatan Mushrikan Makka.

Jagoran shirka da kiyayya da Musulunci na lokacin, wato Abu Sufyanu ba shi da wani tunani in ba na yaki ba, da yadda zai sake kai hari a kan Musulmi da samun nasarar soji da zai sauya irin mummunan aIbn da yakin Badar ya yi musu a ruhi da kafafan yada labarai. Don haka sai Mushirikai suka kada tambarin yaki, suka shirya keta iyaka da kai hari a kan Madina.

Bangarorin biyu sun hadu ne a wajen dutsen Uhudu da ke gefen Madina. Sai Manzo (s.a.w.a) ya aje taswirar yaki, ya shata matsayan sojojinsa, ya sanya wasu maharba a daidai farkon runduna, adadinsu ya kai mayaka hamsin, don su bayar da kariya ta bayan rundunar Musulmi.

Da farkon wannan yaki dai dukkan alamu suna nuni ne ga nasarar Musulmi, don kuwa dakarun Musulmi sun mamaye fagen fama da kuma wasan kura da makiya, inda suka sami ganima mai yawan gaske.

To amma maimakon musulmi musamman maharban da Manzon Allah (s.a.w.a) ya ajiye su su kula da wannan umarni nasa, sai hankula suka koma kan ganima, inda wadannan maharban suka bar wuraren da aka aje su suka nufi wajen ganima. Wannan ne ya haifar da mummunar baraka a sahun masu jihadi, yayin da Khalid bin Walid, kwamandan Mushirikai a wancan lokacin, ya yi amfani da wannan dama ya rufarwa mayakan Musulmi ta bayan su. Wannan samame ya haifar da cin karfin rundunar Musulunci da watsewarta, babu wanda ya saura tare da Manzo (s.a.w.a) sai Ali bin Abi Dalib, Hamza bin Abdulmudallibi, Mus'ab bin Umair da wasu 'yan tsiraru daga Sahabbansa, wadanda suka iya kange Manzo Allah (s.a.w.a) da hana kafirai isa gare shi.

Raunin ya tsananta, kuma hasarar da aka yi ta yawaita. Musulmi sun yi hasarar Hamza bin Abdulmudallibi da Mus'ab bin Umair da wani adadi na Shahidai.

YAKIN KHANDAK

Irin wannan karfi da Musulunci ya yi ya sanya Yahudawa suka ji cewa karfin Manzon Allah (s.a.w.a) babban hadari ne gare su, don haka sai suka shiga yin makirce-makirce ga da'awar Musulunci da Annabinsa, inda suka shiga jan hankulan makiya Musulunci don samar da wata babbar rundunar taron dangi don farwa Madina da gamawa da Musulunci.

Sai suka tuntubi kabilun Kuraishawa da Gatfan, suka dace da su a kan kai wa Madina hari da tsige da'awar Musulunci, sai dai labarin haka ya isa kunnen Manzo (s.a.w.a), don haka sai ya shawarci Sahabbansa kan yadda za'a bullo wa lamarin. Sai Salman al-Farisi (RA), wanda ke cikin zababbun Sahabbansa, ya ba shi shawarar da su kewaye Madina da rami, sai Manzo ya karbi wannan shawara, ya shiga haka rami tare da sauran Musulmi.

A bangare guda kuma Kuraishawa sun yi tanaji da kuma tara mazajensu, masu taimaka musu da sauran mabiyansu, ta yadda adadin rundunarsu ya kai mayaka dubu goma, suka kama hanyar Madina.

Shi kuwa Manzo (s.a.w.a) sai ya shirya Sahabbansa don yaki, adadinsu ya kai mayaka dubu uku.

Harin makiya ya fara yayin da Amru bin Abd Wudd al-Amiri ya ketare ramin, ya shiga yin barazana ga Musulmi yana kira da cewa: "Ko akwai mai fito-na-fito da ni?" Sai Ali bin Abi Talib (a.s) ya mike ya ce: "Ni ne gare shi ya Manzon Allah". Sai Manzo (s.a.w.a) ya ce: "zauna Amru ne fa".

Sai Amru bin Abdu Wudd ya maimaita kiransa, ya shiga yi wa Musulmi izgili. Sai Ali (a.s) ya mike ya ce: "Bar ni da shi Manzon Allah". Sai Annabi ya kara cewa: "zauna Amru ne". Sai Ali (a.s) ya ce: "Ko da Amru ne kuwa". Sai Manzo (s.a.w.a) ya yiwa Ali izini ya ba shi takobinsa Zul-fikari, ya sanya masa garkuwarsa ya kuma nada masa rawaninsa, sannan Manzo ya ce:

A nan yana da kyau a fahimci cewa wannan jaddadawa da Manzon Allah (s) ya ke na cewa "Zauna Amru ne fa, ba wai yana yi ne don yana kokwanto Imam Ali (a.s) zai gaza ba ne wajen kashe Amru, face dai yana yi ne don ya nuna wasu abubuwa: Na farko dai ya nuna matsayin Imam Ali (a.s) na jaruntaka, na biyu kuma kana mafi muhimmanci yana so ne ya gwada sahabbansa ya gani ko wani zai taso ya fuskanci Amru ko kuma suna tsoro saboda sanin irin jaruntakar da Amru din yake da ita. To hakan kuwa ya faru don kuwa babu guda daga cikin sahabbai da ya yi ko alamar motsi wajen mikewa da fuskantar Amru, face ma dai sai kowa ya noke, kamar ba su yi imani da cewa idan Amru ya kashe su wajen kare Musulunci da Manzon Allah (s) za su shiga aljanna ba.

"Ya Allah wannan dan'uwana ne kuma dan baffana. To kar Ka bar ni makadaici don Kai ne mafi alherin Mai gadarwa(1)".

Sai Ali ya gabata da kwazon nan na shi da ya saba, sai ya kara da Amru karawa mai tsanani, daga karshe dai ya bar shi kwance matacce.

Sai Musulmi suka yi kabbara yayin da suka ga Amru kwance a kasa kuma Ali na dawowa da nasara, sai Manzo (s.a.w.a) ya tarbe shi da fadarsa cewa:

"Sarar da Ali ya yiwa Amru bin Abd Wudd tafi ayyukan al'ummata har ranar kiyama(2)".

Da dare ya yi sai iska mai tsananin sanyi ta tashi, ta shiga fasa tukwane tana kashe wuta kuma tana karairaye haimomi. Wannan ya sa tsoro ya kama dakarun mushirikai, don haka sai suka sa kai suka bar Madina. Da wannan Allah Ya kaddarawa Musulmi nasara a wannan yaki da aka yi shi a shekara ta biyar bayan hijira.

Bayan an sami nasara a kansu, sai Kuraishawa suka koma Makka suna a tsiraice da kunya da wulakanta, sai Manzon Allah (s.a.w.a) ya shiga ladabtar da Yahudawa maha'intan abokan zama a Madina, wadanda suka saba alkawarinsu tare da Manzon Allah (s.a.w.a), suka yi makirci tare da Kuraishawa da kungiyoyinsu. Sai Allah kuwa ya dora Annabi a kansu, da wannan fitinarsu ta kare.

YAKIN KHAIBAR

Bayan yakin Ahzab (Khandak) ne labari ya zo wa Manzon Allah (s.a.w.a) cewa akwai wani shiri na boye da ke gudana tsakanin Kuraishawa da Yahudawan Khaibara don yakar Musulmi. Sai Manzo (s.a.w.a) ya kuduri lallabar Kuraishawa don ya raba su da Yahudawa a matakin farko, don kuma ya sami daman yada kiransa a tsakanin Larabawa wadanda ba Kuraishawa a mataki na biyu.

Manzon (s.a.w.a) ya fuskanci Makka tare da mazaje dari biyar, inda suka isa Hudaibiyya. Sai Manzo ya aiki wani mutum daga kabilar Khuza'ah zuwa Kuraishawa don ya sanar da su cewa ya zo ziyarar Dakin Allah don yin Umara da soke hadaya a Harami, da cewa a shirye yake ya sa hannun zaman lafiya da su, in kuwa sun ki zai yake su.

Da ma Kuraishawa na fama da zafin galabarsu da aka yi a yakin Khandak; don haka da suka lura da irin karfin Manzo (s.a.w.a) da nacewarsa a kan abin da ya ke so, suka kuma riski irin raunin da suke fama da shi da gazawarsu a yaki, sai suka amsa kiran Manzo (s.a.w.a). Da haka aka rattaba hannu a kan yarjejeniyar sulhu.

Alkawarin ya sami babban tasiri a tarihin ci-gaban Musulunci, yayin da ya bayar da dama ga Musulmi wajen isar da sakonsu ga wadanda ba Kuraishawa ba na daga mazauna tsibirin Larabawa, sannan suka sami sararin sabuwar gwamnatinsu da karfafa ta.

Khaibara wani gari ne daga garuruwan Yahudawa da ke makwabtaka da Madina. Garin na bisan dutse ne, an kewaye shi da ganuwar dutse, wanda 'yan garin ke zaton za ta iya kare su daga takubban masu jihadin da ke samun taimakon Allah.

Yahudawan Khaibara suna da dabi'un sauran Yahudawa, rudin kai ya mamaye su, don haka Khaibara ta kasance wata cibiya ta kullawa musulmi makirci.

A ganuwar Khaibara akwai mayaki kimanin dubu goma, kullum suna fita sahu-sahu don yin atisaye, har suna yin izgili da irin karfin da Musulmi ke da shi suna masu cewa: "Mahammadu ne zai yake mu? Ko kusa!"

Manzon Alah (s.a.w.a) ya hada rundunarsa da azamarsa, ya kuma boye madosarsa. Ya bi hanyoyin da zai sa duk wani yunkurinsa ya zama cikin sirri, ya dogara da wasu masu nuna hanya. Don haka Yahudawa ba su sami wani labari ba sai bayan da Musulmi suka sauka a fagensu da daddare.

Lokacin da suka sami labarin isowar Musulmi sai shugabanninsu da masu fada-a-ji a cikin su suka yi taro don tsara hanyar da za su fitowa al'amarin da hana kai hari ganuwarsu.

Hari ya fara ne yayin da Manzo ya aiki halifa Abubakar "sai ya dawo ba tare da ya sami nasara alhali ya yi iya kokarinsa(3).

Tabari ya ce:

"Manzo Allah (s.a.w.a) ya bayar da tuta ga Umar dan Khaddabi, ya kuma hada shi da wasu mutane, suka je suka hadu da mutanen Khaibara, sai Umar da mutanen shi suka kasa suka dawo wajen Manzon Allah (s.a.w.a) alhali mutanen da suka tafi da shi suna ragontar da shi shi kuma yana ragontar da su (wato kowa na razana dan'uwansa). Sai Manzo (s.a.w.a) ya ce: "Lallai zan bayar da tutar yaki gobe ga wani mutum da ke son Allah da ManzonSa kuma Allah da ManzonSa ke sonsa". A wata ruwaya ta Ibni Hisham, Manzo ya kara da cewa: "Allah zai buda a hannunsa, shi ba mai gudu ba ne". Da aka wayi gari, da ma Abubakar da Umar na ta sa rai ko su ne za a ba su wannan tuta, amma sai Manzo (s.a.w.a) ya kira Ali(4).

Sai ya ce masa: "Karbi wannan tuta ka tafi da ita har sai Allah ya bayar da nasara ta hannunka".

Sai Ali (a.s) ya karbi tutar ya yunkura tare da wasu Musulmi, ya gabaci ganuwar Khaibara, sai wani shugaban Yahudawa ya fito tare da wasu mutane daga jama'arsa, ya yaki Ali (a.s) sai shi kuma (Ali) ya gaggauta sare shi a kai har sai da wadanda ke rundunar suka ji karar saran da aka yi masa(5)".

Da haka Ali (a.s) ya bude kofar, duk wani kuzarin Yahudawan Khaibara ya wargaje daga nan, kuma Allah Ya ba ManzonSa nasara babba, aka watsa waccan runduna mai karfi.


____________

(1)- Siratul-Nabwiyyah na Dahlan, juzu'i na 2, shafi na 6 da 7.

(2)- Siratul-Nabwiyyah na Dahlan, juzu'i na 2, shafi na 6 da na 7; da Mustarak al-Sahihain, juzu'i na 2, shafi na 32, daga Sufyan al-Thauri; haka nan Khatib al-Bagadadi ya ruwaito shi a cikin Tarikh Bagadad, juzu'i na 13, shafi na 19.

(3)- Ibn Hisham, cikin al-Siratul-Nabawiyyah, juzu'i na 3, shafi na 349, bugun Darulu-Ihya'il-Turath al-Arabi, Beruit.

(4)- Tabari cikin Tarikhul-Umamu wal-Muluk, juzu'i na 2, shafi na 300.

(5)- Tarihin Tabari, juzu'i na 2, shafi na 300; don neman karin bayani sai a koma littafan hadisai da na tarihi.