A+ R A-
22 February 2024

Nahjul Balagha...Kanin Alkur'ani

Ya kamata mu fahimci Amirul Muminin Ali (a.s), ba wai kawai daga maganganun da ake fadi da wadanda muke ji da wakoki da kissoshi da sauransu da ake yi dangane da shi ba, face yana da kyau mu san shi ta hanyar karantar maganganunsa, wadanda suke cikin littafin nan da watakila za a iya cewa mafi dacewar fassara da kuma sunan da aka ba shi, shi ne cewa: Nahjul Balagha, kanin Alkur’ani.

Mu yi dubi cikin hudubobi, wasiku da jumlolin da suke cikinsa wadanda kai ka ce kamar an yi su ne don wannan zamani na mu….

A wadannan ranaku da muke cikin juyayin rabuwa da Shugabanmu, yana da kyau mu dan koma cikin wannan littafi na Nahjul Balagha, don mu fahimci wannan mutumin wanda ya ketare kan iyaka na addini da mazhaba….

Mutumin da sanannen marubucin nan Kirista dan kasar Labanon, George Jordac, cikin kauna da sonsa ya rubuta masa littafi (The Voice of Human Justice) inda ya rubuta cewa: Ali ya kasance abin komawa da kuma rikon dukkanin mutanen masu neman gaskiya…”

Mutumin da bawan Allah ne sannan babu wani da yake gani a gabansa in ba Allah ba, kamar yadda mu ma babu wani abin da muka gani a tattare da shi in ba Allah ba….

Mutumin da Alkur’ani ya siffanta shi a matsayin ‘wani bangare na Annabi’ sannan shi kuma Annabin ya bayyana shi a matsayin wani mutum mai kolin matsayin da ‘babu wanda ya san shi sai Allah da Manzonsa’…

Ina isar da sakon ta’aziyya da juyayin shahadar Imam Ali (a.s) ga dukkanin bil’adama musamman mabiya wannan babban bawan Allah, ina mai fatan cewa cikin wadannan ranakun za mu dan leka Nahjul Balagha don kara fahimtar wannan babban bawan Allah.