A+ R A-
22 February 2024

Habib bn Mazahir al-Asadi, Aboki Kuma Sahabin Imam Husain (a.s)

Habib bn Mazahir al-Asadi ya kasance daga cikin kabilar Banu Asad, duk da cewa ba a yi bayanin cikakken lokacin da aka haife shi ba, to  amma dai abin da aka tabbatar  shi ne cewa  a lokacin da yayi shahada a Karbala ya kasance yana da shekaru 75 a duniya. Ya kasance daga cikin sahabban Ma'aiki (s.a.w.a) kana kuma daga cikin zababbun shahabban Imam Amirul Muminin Ali (a.s) ya kasance cikin dukkanin yakukuwan da Imam Ali (a.s) ya yi, kamar yadda kuma ya kasance daga cikin sahabbai kana masoya Imam Husain (a.s) wadanda suka ba da jininsu don kare shi da kuma kare yunkurinsa na Karbala.

Tun yana karami, Allah Ya sanya wa Habib tsananin kaunar Imam Husain (a.s) wanda ya kasance kusan tsararsa a bangaren shekaru a wancan lokacin. Irin wannan kaunar da yake nuna wa Imam Husain (a.s) ne ma ya sanya Manzo (s.a.w.a) yake tsananin kaunarsa. An ruwaito cewa wata rana Manzon Allah (s.a.w.a) yana tafiya tare da daya daga cikin sahabbansa mai suna Mazahir (wato baban Habib). Da suka zo wani waje sai Manzo ya zauna a kasa. Sai ya kira dan Mazahir din wato Habib, ko da yaron ya zo sai Manzo (s.a.w.a) ya rungume shi yana sumbantarsa. Wannan yanayi dai ya ba wa Mazahir mamaki, don haka sai ya tambayi Annabi (s.a.w.a) me dan nasa yayi da ya cancanci irin wannan nuna kaunar daga wajensa. Nan take idanuwan Ma'aiki (s.a.w.a) suka ciko da kwalla yana fadin cewa: Ya Mazahir! Lokacin da muke tafiya na lura Habib, yana tafiya a bayan Husain, duk inda ina Husain ya taka shi ma ya kan bi wajen don nuna girmamawa ga Husain. Ya Mazahir, wannan Habib din wata rana zai taimaka wa dana Husain.

Wannan yana nuni da irin matsayin da Habib yake da shi ta yadda har an sanar da Ma'aiki irin rawar da zai taka wajen kare Musulunci a nan gaba.

Habib ya tashi ne a gidan da ya gaji jaruntaka da karimci da cika alkawari da dai sauran siffofi masu kyau kuma na kamala, wanda irin wadannan siffofi su ne suka sanya ya zama abin yarda a wajen Imam Husain (a.s) kafin haka kuma a wajen mahaifinsa Imam Amirul Muminin (a.s).

A hakikanin gaskiya kaunar Ahlulbaiti da kuma sadaukarwa saboda su ba wani bakon abu ba ne a wajen Habib da kuma zuriyarsa don kuwa 'yan'uwansa biyu wato Yazid da Ali su ma sun kasance daga cikin wadanda suka yi shahada tare da Imam Husain (a.s) a Karbala. Wasu riwayoyin sun bayyana cewar: Lokacin da abubuwa suka fara yin tsanani a Karbala, Imam Husain (a.s) ya gaya wa sahabbansa cewa: "A cikinku duk wanda yake tare da mace, to ya koma da ita wajen iyayenta". Sai Ali bn Mazahir (dan'uwan Habib) ya mike ya ce: Ko me ya sa haka, Ya Shugabana! Sai Imam Husain (a.s) ya ce masa: Saboda bayan an kashe ni za a kama matayena a matsayin fursunonin yaki. Ina tsoron kar a kama muku matayenku a matsayin fursunonin yaki. Don haka sai Ali ya tashi ya tafi haimarsa ya gaya wa matarsa abin da Imam Husain (a.s) ya ce, sai ta tambaye shi cewa to  yanzu me kake son yi, sai ya ce mata: Ki tashi in mai da ke wajen iyayenki. Sai ta ce masa: A'a wallahi, mu zauna, ku kuna tausayawa (kuna ba da kariya ga) maza (na daga zuriyar Annabi) mu kuma muna tausayawa wa mata. Don haka sai ya koma wajen Imam Husain (a.s) ya gaya masa cewa: Ba'asadiyya ta ki yarda, face ta ci gaba da zama da ku. Don haka sai Imam Husain (a.s) ya gode musu da musu fatan alheri.

Don haka kaunar Imam Husain (a.s) wani lamari ne da ya sami gindin zama cikin zukatan iyalan Habib musamman ma shi Habib din wanda irin wadannan siffofi da yake da su ne ya sanya ya zamanto abin kauna da kuma yardar Imam Amirul Muminin (a.s), wanda hakan ya sanya ya kan sanar da shi wasu ilmummuka wadanda bai sanar da sauran sahabbansa ba.

Habib bn Mazahir ya kasance abokin Imam Husain (a.s) na kurkusa tun suna kanana. A lokacin da Imam Ali (a.s) ya mayar da helkwatar halifancinsa daga Madina zuwa Kufa, shi ma Habib ya koma garin na Kufa, inda ya zauna a can kuma ya zamanto daga cikin manyan garin. Irin wannan kusaci da yake da shi da Imam Husain (a.s) da kuma kaunar da yake masa ne ma ya sanya shi ne mutumin farko, daga cikin mutanen Kufa, da ya fara rubutawa Imam Husain (a.s) wasika da kiransa da ya zo garin Kufan don jagorantar  al'umma.

Duk da cewa Habib ya taka gagarumar rawa a lokacin halifancin Imam Amirul Muminin (a.s) musamman cikin yakukuwan da yayi, to sai dai suna da kuma tauraruwarsa ta  fi  fitowa fili ne yayin yunkurin Ashura na Imam Husain (a.s).

Don haka bari mu dan yi dubi ko da a  takaice ne dangane da irin rawar da ya taka a wannan fage da kuma irin yadda ya kasance mai cika alkawari da kara tabbatar da wilayarsa ga Ahlulbati (a.s)  duk kuwa da irin tsananin da ake ciki.

Bayan da Imam Husain (a.s) ya kaddamar da yunkurinsa na tsarkake Musulunci daga dauda da kazantar da Umayyawa suka shafa masa daga garin Makka, da kuma wasikun da ya dinga samu daga wajen mutanen Kufa kan ya zo don ya jagorance su. Imam Husain ya aika da dan baffansa Muslim bn Akil zuwa Kufan don gane masa yanayin da ake ciki.

Bayan isar Muslim da kuma irin yadda lamurra suka sauya bayan isar Ubaidullah bn Ziyad garin da nufin murkushe wannan yunkuri na mutanen Kufa, lamarin da ya sanya mutanen Kufan juyawa da baya. Daga karshe dai Ubaidullah ya ba  da umurnin rufe garin ta yadda babu wani da zai shiga ko fita ba tare da sani da kuma izininsa ba.

Wannan yanayi ya sanya Habib bn Mazahir cikin tsananin kumci da damuwa don kuwa a loakcin bai ma san halin da Imam Husain (a.s) din yake ciki don kuwa Ibn Ziyad ya sanya 'yan leken asirinsa suna ta  yada jita-jita da kararraki don dai a razana mutane da kuma kashe musu gwiwan tunanin taimakon Imam Husain (a.s).

A cikin irin wannan yanayin ne sai ga wasikar Imam Husain (a.s) zuwa gare shi yana kiransa da ya zo ya same shi. A cikin wasikar dai Imam Husain (a.s) ya rubuta masa cewa:

"Daga wajen Husain bn Ali zuwa ga masani Habib bn Mazahir. Bayan haka, Ya Habib, ka san irin kusancinmu da Manzon Allah (s.a.w.a), kai din nan ka fi waninka saninmu. Kai din nan ma'abocin dabi'u da kishi ne, don haka kada ka yi mana rowar kanka. Sakayyarka na wajen Kakanmu, Manzon Allah".

Lokacin da Habib bn Mazahir ya samu wannan wasika ta Imam Husain (a.s) ya sanar da matarsa abin da ta kumsa. Na take cikin kauna ta bukace shi da ya gaggauta tafiya don taimakon Imam Husain (a.s).

Daga nan sai Habib ya fara shirin tafiya wajen Imam Husain (a.s), to sai dai kuma cikin sirri ba tare da an sani ba don kada labari ya  yadu Ibn Ziyad ya cutar da shi. To sai dai duk da hakan labarin ya dan fara fita inda kabila da danginsa suka nufo wajensa don neman jin gaskiya labarin. Habib dai ya musanta musu wannan labarin inda ya ce babu gaskiya cikin hakan. Bayan tafiyarsu dai matarsa wacce ta ji yadda tattaunarwar ta su ta kasance ta zo wajensa inda ta tambaye shi wai shin da gaske ne ba zai tafi din ba. To don ya jarraba ta sai ya ce mata lalle ba zai tafi ba. Nan take ta fashe da kuka tana ce masa: Ashe ka mance da maganar kakansu Annabi (s.a.w.a) a kansa ne da dan'uwansa Hasan inda ya ke cewa: Wadannan 'ya'ya nawa su biyu, su ne shugabannin matasan Aljanna, sannan kuma su imamai ne, sun mike ko kuma ba su mike ba. A halin yanzu ga manzon Husain ya zo maka da wasikar neman taimakonka, amma ka ki ka amsa masa?. Sai Habin ya ce mata: Ina tsoron abin da zai sami 'ya'yana na zama marayu, sannan ke kuma ki zama bazawara a bayana. Sai ta  ce masa: Allah Madaukakin Sarki Shi zai kula da mu kuma Ya isar mana, kuma madalla da kasantuwarsa mai kula da mu. Lokacin da Habib ya fahimci irin wannan imani nata da kuma dagewa kan cika alkawari ga iyalan gidan Annabi, don haka sai ya gobe mata da kuma sanar da ita hakikanin abin da ke cikin zuciyarsa na tafiya wajen taimakon Imam Husain (a.s). Sai matar ta ce masa to ina da wata bukata a wajenka. Ya ce mata mece ce bukatar ta ki. Sai ta ce: Ya Habib, don Allah, idan har ka gana da Husain, ka sumbanta min hannunsa a madadina, sannan ka isar min da gaisuwa  ta  zuwa gare shi.

Daga nan sai Habib ya umurci wani bawansa amini da ya kama dokinsa ya tafi da shi can wajen gari ya jira shi a can, idan har an tambaye shi ya ce zai kai shi kiwo ne. Lokacin da yamma ta yi sai Habib ya sulale ya nufin inda dokin nasa yake. Lokacin da ya isa can, ya hau dokin, sai yayi bankwana da bawan nasa ya ce masa: Tafi abinka, na 'yantar da kai. Nan take bawan ya sa kuka yana cewa: Ya kai shugabana ba ka kyauta min ba. Na kasance mai maka hidima shekaru aru-aru. A halin yanzu na sami damar yin hidima wa dan Fatima al-Zahra (a.s), amma kana ce min in tafi. Me ya sa kake hana ni waje a cikin Aljanna? Wadannan kalmomi sun sosa ran Habib, don haka sai ya bukace shi da ya hau bayan doki su tafi tare inda suka isa Karbala tare.

A daidai wannan lokacin da Habib yake ta shirin zuwa Karbala, shi kuma Imam (a.s) yana ta shirin raba tutoci guda goma sha biyu da ya tsara su, sai aka ga ya ajiye guda daya ko da aka tambaye shi ta waye sai ya ce mai ita yana nan tafe.

Ana cikin hakan ne sai aka ga kura tana tasowa daga bangaren garin Kufa, wato Habib da bawansa ne suka doso Karbala. Don haka sai Husain da sahabbansa suka nufi inda suke don yi musu maraba. Lokacin da Habib ya iso ya sauka a kan dokinsa ya nufo inda Imam Husain (a.s) yake yana kuka yayi masa sallama, Imam da sahabbansa suka amsa masa. Lokacin da Zainab (a.s) ta ji zuwan Habib din sai ta tambaya wane ne wannan mutumin da ya zo din? Sai aka ce mata: Habib bn Mazahir ne. Sai ta ce: Ku isar masa da sallamata. Lokacin da aka gaya masa nan take Habib ya fashe da kuka yana fadin cewa: Ni ne wa da har 'yar Amirul Muminin Ali za ta gaishe ni.

Riwayoyi sun bayyana cewar Habib ya iso sansanin Imam Husain (a.s) ne ranar shida ga watan Muharram, don haka bayan isowarsa yayi iyakacin kokarinsa wajen janyo wasu mutane daga cikin 'yan kabilarsa na Banu Asad da suke cikin rundunar Ibn Ziyad inda ya sami nasarar mai do da wasu daga cikinsu zuwa sansanin Imam Husain (a.s) bayan da ya kiraye su zuwa ga taimakon dan 'yar Ma'aiki (s.a.w.a) har zuwa ranar Ashura, ranar  karshe ta Imam Husain (a.s) da mabiyansa.

A wannan rana sahabban Imam Husain (a.s) daya bayan daya suna tafiya filin daga don yakar makiya bayan yaki na wani lokaci, daya bayan daya sunata yin shahada.

Ganin haka sai Habib bn Mazahir ya taho wajen Imam Husain (a.s) ya ce masa: Ya Shugabana! Ka ba ni izinin fita filin daga. Ka bari in sadaukar da raina saboda Musulunci.

Imam Husain (a.s) ya ce masa: Ya Habib, Ya tsohon abokina, ka zauna tare da ni, don kuwa kana kwantar min da rai.

Habib dai ya ci gaba da matsawa. Daga karshe dai Imam Husain (a.s) ya ba shi izinin fita. An ce Imam Husain (a.s) shi ya rike masa dokinsa ya  hau, inda ya shiga fagen daga ya ta bugun makiya da kashe su har lokacin da suka yi masa taron dangi, suka cimmasa ya fadi a kasa.

Ganin haka Imam Husain (a.s) ya ruga da gudu ya tafi wajensa. Koda Habib ya ga Imam Husain sai ya ce masa: Ya dan Manzon Allah, ka gafarta min saboda gazawar da na yi wajen sadaukarwa sama da wannan ran da nake da shi saboda kai da kuma Musulunci". Imam Husain (a.s) ya dauki Habib ya rungume shi yana kuka. Da haka ne dai Habib yayi shahada a kafadar Imam Husain (a.s).